bayan ta buga wani uban tsaki da ni kaina sai da ya shige ni. Sannan na Éago ina cewa da ita,"bara na Æarasa rabon nan sai mu je". Wata muguwar harara ta watsa min tana cewa,"ke dai wallahi anyi asararriya, to idan kin Æarasa Allah ya tsine min, lusarar mace kawai".
Ina kallonta da murmushin Æarfin hali na ce,"ba wani abu ba ne lokaci guda ne anyi an wuce wurin fa, bara saur...".
Tsawa ta sakar min,"ke dalla rufe min baki idan bassu da hannun Éauka su mutu ko kuma wanda ya tarasu ya zo ya raba musu, dama ga su nan duk kalar yunwa, muje ni kina Éata min lokaci".
Ni dai daÉi duk ya cikani nama rasa ya zan kwatanta murnar ganinta nace,"Safiyya ta ya kika zo gidan nan?".
Maimakon amsa tambayata sai ce tayi,"Ina ne Éakinki?". tayi maganar a zafafe.
"Æakina na sama".
Tana riÆe da hannuna muka hau sama, muna shiga Éaki ta isa ga wadrobe ta buÉe ta Éauko mayafi ta cillo min,"saka mu je".
"Muje ina?"
"Gidan yankan kai". Ta faÉa tana wurga min harara da ke bayyana tsantsar jin haushina da take yi. Sai kuma ta kama faÉin,"Shashasha kawai mara aji, mijinki na Æara aure amma saboda rashin sanin ciwon kai ke ce da rabon abinci wa Æ´an bikin da ba gayyarki ba, ai wallahi ke dai banza ce ta ajin Æarshe wacce ta rako mata duniya, to idan tunaninki wannan biyayyar aure ce kike magana ta gaskiya zubarwa da kai daraja ne da neman suna irin na jahilan mata. Su kansu waÉanda ki ka zage kina bawa abinci kallon typical mahaukaciya su ke miki".
Hannuna na Éora bisa kafaÉarta na ce,"numfasa don Allah, ni wannan abun ba ya damuna don haka kar ki bari kema ya dame ki".
Ta tunkuÉe hannuna,"to ita Jummai cangal Éin nan ta dawo ta tare naganta a compound tana faman ba da istruction".
Kallonta na ke yi sosai da yanda Æwayar idonta ta kaÉa tayi jajir, na sauke numfashi na ce,"na faÉa miki ki daina kiranta da wannan sunan ko dan darajar auren Éanta da na ke".
Ta fusata ta ce,"Ki sa a yanka ni Jummai cangal ba zan fasa faÉa ba".
Tayi maganar tana Éaga kiran da ya shigo wayarta, tayi sallama tare da cewa,"na je Ummani". Tayi shiru na Éan wani lokaci kafin ta sake cewa,"insha Allahu Ummani ba za'a sami wata matsala ba, naji faÉanki kuma ba zan saÉa daga nasihar da kika min ba, amin ya Allah".
Ta sauke wayar na ce,"Gidanmu kika je?".
Ta ce,"Ehh da nake ta kiranki kika Æi Éauka saboda ga annoba na kiranki sai na nemi waccan fat friend taki ta tura min lambar Ummani, ke ni tsautsayi ne ma ya kai ni gidan don ba a haka na zo garin nan ba. kinga kayan jikin nan nawa sai da naje can na sauya su, da na bacci na zo da hijab Éin me aiki don ina tashi na kira Baba na ce a yankar min tiket, jiya fa ban iya barci ba Sa'ida ina ji ma jinina ya hau sai na koma zan yi bp. Ummani ce tayi min faÉa da nasiha banda haka da shigowata gidan nan tuni anyi asibiti da kaf zuri'ar Nazifi da wanda ya zo taya su murna, ke kaÉai za ki rage kema Éin kuma ba haka zan barki ba sai na raunanaki".
Ina murmushi na ce,"Uhmm ke dai ki koyi haÆuri kam, wannan zafin zuciyar taki yay yawa, duk akan wata kishiya ki Éaga hankali. Ko da yake ni naji daÉi ma sanadinta ga shi Allah ya kawo min ke bayan rabuwar shekaru da yawa".
"Mtssswww Kinga ba doguwar magana na zo muyi ba saka mayafinki mu je".
"Wai sai ce kike in saka mayafi muje, ina zamu? Kuma ai kin san ban tambaya ba".
"To me miji ai na faÉa masa tifa tayi awon gaba da kishiyar uwata zamu wuce asibiti da ke tare dubiya, in kuma yarda ne ba kiyi ba duba kiga". Ta faÉa tana nuna min message, da gaske kam take yi dama ba wani shiri su ke da shi ba don haka duk amsoshin da ya dawo mata da su a gajarce ne kamar yanda itama ta tura masa saÆon kamar tana basa umarni.
Na ce,"To ai bana fita da mayafi kin fi kowa sani, miÆo min hijab".
"Æunshe ki da ake da hijab ya zama past Beb, so yafa mayafi mu tafi, a tarihin Amaryar Nazifi da na duba babu saka hijabi idan zata fita a al'amuranta kuma auren Nazifi ba zai sauya ra'ayinta ba, infact ba macen da Namiji zai juya ba ce yanda ya so and tana da mutunci sai dai akwai ji da kai. Duk nayi wannan binciken akanta ne bayan gama wayarmu da ke jiya, mun ma yi waya da ita na karanta mata bani da hankali ko na misÆala zarra har feÉe mutum ina iya yi, kuma gasa fatar na ke nasa ayi masa romon kayarsa ya ci, don haka ta kiyaye taÉa wacca zata shiga gidanta don gatan ta cikin gidan ya fita da kaf abunda ta ke taÆama da shi, sannan ta shirya kurÉan baÆin cikin gidan aurenta domin wanda zata aura annamimi ne".
Mayafin ta dankama min aka muka fita ina kallonta baki sake, ita ta rufe Æofar tana riÆe da hannuna muka sauka, gabanin zamu fita a falo Iyam ta shiga dakatar da mu da saurin murya. ni na juyo amma Safiyya tsayawa kawai tayi shima kuma dan na tsaya Éin ne na ruÆota. Iyam ta iso garemu tana faÉin,"ki kaita ina? Ke kuma algunguma gidan uwar wa za ki je".
BuÉar