NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 77 of 97

nta da ta ƙara tambayar adireshin gidana don Safiyya na daga cikin mutanen da ke tabbatar da maganarsu idan sun faɗa, ko bata zo da ƴan daba ba to tabbas zuwanta sai ya haifar da rashin daɗi. Sai bayan kiran ma ya katse na ga ashe tun kusan da na fita ne ta ke kira miscalls goma haka ta bar mini, na shiga message ina duba saƙon da ta turo. _"Beb na kasa yin breakfast, zuciyata taƙi yarda da cewa Nazifi ne zai yi miki kishiya, don Allah ki ɗaga kirana ko ki turo min da address na gidanki, yanzu haka ina shirin baro legos nan da awa ɗaya da mintuna zan shigo kano jirgi zan biyo, kuma don girman Allah ki daina kuka na sanki sarai, am on my way to na zo nayi haukar da zata sa a fasa auren nan yau"._ Girgiza kaina kawai nayi ina sauke numfashi a fili na furta Allah ya sanyaya miki. Ina kwance nayi nisa cikin tunani Ummani ta kira ni, Allah sarki uwa muryarta kawai ya shaida min cikin damuwa take, bayan mun gama gaisawa ta tambayeni babu dai wata matsala ko na ce mata ehh babu komai har ma na shaida mata masu tada hatsaniyar basa gidan jiya Yaya Babba ya zo duk ya kora su sai dai ban sani ba ko sai anjima za su zo amma dai yanzu daga ni sai Iyam ne sai baƙin ƙauye mutum uku da suka zo. Sai sannan naji natsuwa ta samu a muryarta tana aduan Allah yasa ma su tsaya a can gidan su yi bikinsu, haka tayi ta min hira duk dan ta ɗebe min kewa, katin wayarta ma ya ƙare kuma babu jimawa ta ƙara kira wai har ta bayar an siyo mata katin ɗari biyu, haka muka ci gaba da wayarmu na shagaltu a labarin rayuwarta da take bani, har sai da taji an fara yi mata warning kana ta ce to ko ta turo min Hindatu da Sa'adatu su tayani zama zuwa yamma sai su dawo na ce mata a'a kar su zo a sami matsala tunda duk suma zuciyarsu a wuya take. Nan ta shiga nanata min da cewa in ƙara haƙuri da kauda kai cikin maganganunta na kwantar da hankali da sa natsuwa da haka mu ka yi sallama. Wajen sha biyu na rana gida ya fara cika da mutane, ashe biki sosai Iyam ta shirya matsayinta na uwar ango dan har sai da ta kai an wangale gate, waɗanda su ka fara zuwan duk ƴan  uwa ne irin na nesa sai jama'arta na tsohuwar unguwarsu, kan kace kobo gida ya ɗinke da hayaniyar jama'a kace auren fari ne ko kuma zata aurar da ƴar autarta ne. Da kanta ta zo har ɗakina karon farko tun zamanta a gidan tace na sauko na tayata karɓar baƙi kafin ƴaƴanta su zo, bayan fitarta na daɗa gyara jikina tukunna na fita, tunda na sakko ido yayo kaina ni kuwa na mayar da komai ba komai ba kamar yanda mahaifiyata ta ce da ni, don haka cikin fara'a da mutuntawa muka gaggaisa da mutanen da na samu a falo sannan na wuce ɗakin Iyam, can na sameta sunata hidima ita da muƙarrabanta, na ce mata gani me za'ai, tayi min nuni da kulolin abinci tace in ke zuzzubawa ga plate ina kaiwa baƙi. Kamar na juyawata na koma ɗaki ganin an raina min hankali amma haka na daure kawai na shiga buɗe kulolin ina zuzzuba abincin, alala ne da dambu aka yi sai lemon zoɓo da na jinja, idan na zuba kamar faranti biyar sai in ɗauka in je in raba kana na dawo, hidimar baƙin nata dai ta dawo hannuna gaba ɗaya kuma ko kaɗan ban bar wani shaida da za'a karanci ƙunci da kishin da ke danƙare a zuciyata ba balle aji daɗin yaɓa min magana amma a haka ma ban taira ba, don ina jin ƙusƙus ɗin wasu na cewa ko dai ba na son mijin dama ko kuma akwai abunda na ƙulla don haka banza dai ba zan ke wannan sabgogin ba. Sai da lokacin sallar ƙarfe ɗaya kana na yakice na koma ɗaki, sallah nayi na kishingiɗa ina hutawa don na gaji kam. Lubabatu su ka shigo ɗakin ita da baƙi wanda ta rako, matan abokansa ne da suka yi tasowar yarinta kuma ban yi mamakin ganinsu ba dan dama da su ne mu ke ma'amala ta mutunci tun a tsohuwar unguwarmu, na tarbe su cikin mutunci nasa Lubabatu ta kawo musu abinci duk da ina fargabar kar Iyam ta hana, to da yake taga baƙin sun shafi ɗanta sai ga uban abinci kuwa an hayo da shi, mun yi hira da su sun nuna min kulawa kusan zan ce don su taushe ni ma shi ne maƙudin zuwan nasu ba kamar yanda nayi tunanin ƴan taya murna ba ne kamar yanda na san mazajensu za su taya shi. Bayan tafiyarsu Iyam tace na zo mu ci gaba da aikin raba abinci ni da Lubabatu, lokacin ƙarfe biyu da rabi a sannan ne Lubabatu ke labarta min ba'a jima da ɗaura auren ba yanzu haka wasu har sun kamo hanyar dawowa, furucin nata yasa gabana faɗuwa da ƙara jin matsananincin kishin Nazifi. ina tsaka da rabon lemo sai ji nayi anwa hannuna muguwar damƙa, na kaikato kaina wajen ganin waye don har ga Allah zatona ma ko su Anty Aisha ne ƴan neman bala'i da hana kwanciyar hankali suka dawo, sai dai me! ware idon da zanyi sai ganin Safiyya na yi, ban san lokacin da na watsar da kayan hannuna ba na ɗago gaba ɗayana na rungumeta cikin murna da jin daɗi sai kuma kuka kamar dama jiransa na ke yi. Bata ɗago kaina daga kafaɗarta ba ta kama hannuna zamu bar wajen
🏠