a wata lambar ta kirasa don sai bayan ya Éaga ne ya ke cewa,"wannan numbern fa ina na ki wayan?". da haka kuma ya tashi ya fice yayin da na ke jin zuciyata kamar zata yi bindiga.
Ya jima kafin ya dawo ciki, kuma sai lokacin ne ma yake kashe wayar don ina ji yana ce mata,"Kishiyar Iyam ce sai Yayyuna biyu da Æanwar Malam. Sai dai mun Æaraso Éin nan da sha Éaya jirgin namu zai ta so".
Idona ya cika da ruwan hawaye inda na ke kallon fuskarsa da ke bayyana annurinta. da Æyar na mayar da hawayen idona da ke son zubowa, na rufe Æur'anin da na ke karantawa na tashi tare da ninke sallayar duk na mayar da su ma'adanarsu. na zauna gefen gadon ina cewa da shi,"ina kwana".
"Lafiya lau". ya amsa a gajarce.
Tun daga haka ban Æara magana ba, kuma kamar jira ake gari ya waye sai ga kira na ta shigowa wayarsa, ba ya numfasawar minti guda wani kiran zai Æara shigowa, har sai da shima ya fara gajiya da hakan don dama tun daren jiyan na lura a gajiye ya ke sosai.
Fita nayi na bar masa Éakin na kama hidimar gyaran gidana, sun yi kaca kaca da falon har Æarni yake yi kuma an rasa me gyarawa duk uban Æ´an matan cikinsu, gidan dai tsit ina ga sunji kashedin Yaya Babba sun kama gabansu, cikin ÆanÆanan lokaci na kimtsa falon na tashe shi da Æamshi, kana na koma sama nayi wanka na shirya tsab abina na ci kwalliyata ina ta yin iya ÆoÆarina wajen basar da lamarin bikin nan, kuma Allah sai ya saka min natsuwa a zuciyata, duk da babu Æunshi babu gyaran kai amma fess na fito nayi kyau da ni, ban baro Éakina ba sai da na gyara shi na sanya karatun Æur'ani.
Lokacin da na sakko Æarfe takwas da rabi, na leÆa Éakin ina ce masa,"Zan Éora abinci ne da kai?".
Wani kallo yay min kafin yace,"Da sai kin tambayeni?".
"Yau Éin kamawa tayi na tambaya".
"Kiyi duk yanda yay miki".
KafaÉa na Éaga na fita, kunun tsamiya na Éora da soyayyar doya babu Æwai, ina ga Æwan sun cinye shi daga shekaranjiya zuwa jiya, dama kiret uku ne yay saura yana cewa za'a kawo ba'a kawo ba. Ban Éora da yawa ba, daidai cikina da na Iyam da na yaran ne, yanda na ke ta abuna kamar ba wadda za'ai wa kishiya ba. na zuba doya a flask Éin zan kai mata sai ga shi ya shigo kicin Éin sanye cikin dakakkiyar shadda fara sai uban Æyalli da Éaukar ido take yi, an yiwa babbar rigar azababben Éinki irin na sarakai, fuskarsa sai fidda annuri yake irin na sabbin angwaye masu Éoki, Æamshi kuwa la'ila ha'ilallah ban taÉa dai jin Æamshi me irin wannan daÉin ba.
Kibiyar kishi ta soke ni naji hannayena sun shiga karkarwa, da Æyar na iya saita kaina. Muryarsa a tausashe yace da ni,"Zamu wuce can wajen Éaurin auren, a Abuja ne na san kin gani a katin, ban san lokacin da zamu dawo ba amma ba zama zamu yi ba ana Éaurawa zamu taho. Amarya sai gobe za'a kawota, babu wani abu da kika buÆata zan iya tafiya?".
"Babu komai". Na faÉa a sanyaye.
"Don Allah Sa'ida kar inji wata fitina. ko Iyam ba wani taro zata yi ba duk Æ´an uwa ne".
Na ce,"fitina ai sai fitinanne, ni da banda matsala da kowa".
Ya ce,"Na tafi to".
Na ce,"Allah ya kiyaye ya tsare hanya, a dawo lafiya".
Ya amsa da amin kana ya juya ya fita ni kuma na rakashi da ido, babu yacca ban ba hawaye karsu zubo min amma ina marayan kuka na saki ina durÆushewa a kicin Éin.
Ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawa shi kaÉai yasan irin zafi da raÉaÉin da zuciyata ke yi a wannan lokacin. Haka na ci kukana na gode Allah kafin in miÆe da Æyar in wanke fuskata a cikin sink Éin kicin, kaina kuwa kamar zai tsage saboda azababben ciwo, ga jikina da ke karkarwa kamar me shirin kwancewa zazzaÉi. Abincin da na gama haÉawa na kwasa, sai da na haÉe har da nawa na juye a ciki don sam bana tunanin a yau dai wani abu shi abinci zai shiga cikina, ai ko yawun bakina jinsa na ke tamkar maÉaci.
Ina shiga Éakin Iyam na aje mata abincinta, kallo ta bini da shi da mamakinta na ganina fess kamar ba wadda miji ke Æara aure ba, kuma saboda an fi son ganinka a Æuntatace har ce take to Allah sa ba mugun abu na Æulla ba don ita bata taÉa ganin wacca za'a kishiya na harkokin gabanta ba rai fess a ranar biki.
Na fito ina Æwala kiran su Rumana Iyam ta leÆo tana shaida min ai da su aka tafi jiya, ta faÉa tana ta Æare min kallo gami da Æara cika da mamakina, kicin na koma na aje abincin na su kana na koma Éaki, ina shiga kuwa na tarar da wayata na Æara da sauri naje na Éauka sai dai ganin sunan da ke kan screen Éin yasa ban Éaga ba.
_"zan yo hayar Æ´an daba mu zo gobe"._
Maganar ta Safiyya a jiya ta haska min cikin kai, don haka kawai na mayar da wayar na ajiye, na sani Safiyya me matuÆar damuwa da damuwa ta ce, tana kira ne don taji a wanne hali na ke, to sai dai raunin da ke tare da ni ba zai iya Éoye halin da zuciyata ke ciki ba wanda ko da na faÉi akasin hakan don Éoyewa za'a Æaryata ni, kuma ina tsoro