ni sakar mata fuska balle ta sami fakar rainaki har ta kai ga cin mutunci, ke mu'amala da ita ma ba dole ki barsu idan haÉe miki kai za su yi can su Æarata, banda hauka ma duk sun zo sun tare miki a gida ita tana gani saboda uwar kawai ce bata san abunda ya kamata ba taÆi tsawatar musu. To ni dai na faÉa miki ki taka musu burki hatta shi kansa karma ya kawo matarsa ya dinÆa wulaÆantaki a gabanta, hanyar ma da kika Éauka kici gaba da yin hakan ba zan ce miki ki daina ba, ta hakanne za ki mutunta kanki. Kuma daga yanzu duk wata matsala idan kina da ki tafi kanki tsaye wurin Yayan mahaifinki ki faÉa masa, ai ban taho ba sai da na jira ya dawo na sameshi na faÉa masa yace shi waccan shari'ar ma bai san da ita ba har kawo yanzu da na ke faÉa masa. Kuma Allah yasa Malam Mudassir(Æanin Kaka) yanan da ike ya san daidai sai yay ta faÉa yana akan me yasa ita mace ba'a bata ikon da zata yi magana ko ta kare kanta kawai shikenan duk abinda miji ya faÉa kai za'a hau a zauna ga uban masu daidai da gaskiya yay magana, mace ta kawo kukanta gidansu da take tunanin samun sassauci sai a Æi sauraronta balle tayi magana kawai a yanke hukunci, ba dole baÆin ciki yaywa mutum yawa ba, shiyasa ai ga matan nan duk ba'a rasa su da ciwon zuciya da hawan jini, sai Æ´arka ta mutu bincike ya nuna ciwon da yay ajalinta a zo ana inama inama, me yasa da take raye baku bata izini da ikon da zata faÉi damuwarta ba, shikenan da yarinya tazo ku iyaye maza ku Æi sauraronta ke kuma uwa bakki da aiki sai na tayi haÆuri kowacce mace haÆuri take yi, to don kowa na haÆuri shikenan sai aka ce matsalar wata bata fi ta wata ba, duk rashin bawa Æ´aÆ´a ikon faÉar halin damuwar da suke ciki ke sawa zuciyoyinsu su buga".
Hajjo bata jima ba ta tafi bayan ban baki da ta babbani, ta kuma bani adu'oi da Éora ni akan dabaru masu tsari. Tun bayan tafiyar Hajjo ban Æunshe kaina a Éaki ba, idan fita ta kama fita na ke nayi sabgogina na dawo, sai dai kaf cikin yara da manyan babu wanda ya ishe ni kallo banda Rumana da suka dawo a lalle take nuna min itama na Éauke kai kawai nayi gaba tare da mata gargaÉin kar in ga Æafarta a Éakina.
Tashin hayaniya na jiyo kaman na faÉa hakan yasa na fita da sauri na leÆa tunda masu jeran kayan amarya sun zo suma, tunanina ko da su ta haÉosu sai dai ina leÆa kaina Æasa na hango Yaya Babba wato Babban Éan Iyam wanda Yaya take bi, Da yake shi ba nan garin yake ba can kaduna ya ke zaune yana kasuwancin gwanjo, kowacce ta natsu a falon hatta ita Yayan yana musu faÉa.
"Haka ake yi dama sai ka ce garin mahaukata, ku zo ku wani tare a gidan mutum, kuma don rashin hankali kun zo kuna Éaga hankalin matar gidan, ai duk an faÉa min abubuwan da kuke aikatawa, hisabi ne dai yanzu tun a duniya Allah ke yi ba sai anje lahira ba da gaggawa Allah ke sakayya kar wacce ta fasa mugun halinta".
Ashe har da Nazifin shima yana wajen naji yana ce masa,"Kai kuma susun banza ai da iliminka, ina addini ya ce saboda ka aurota ka bar mahaifiyarka da Æ´an uwanka su wulaÆantata? Ina ce addini ce yay ka tsareta ka tsare mata mutuncinta da kimarta, ko ita Éin jaka ce ko daga sama ta faÉo ka tsinceta ka aura da zaka bar Æ´an uwanka na cin zarafinta?...".
Iyam ta iso wajen tana cewa,"Sam sam sam ban yarda da hakan ba, babu ruwanka da shishshigi, idan matarka ka zo Éauka to Éaukarta ku tafi ba zaka saka yarana a gaba kana faman yi musu faÉa ba".
Tana yin shiru ya kaÉa kai yace,"tom shikenan". Ya juya ya Æare musu kallo ya ce,"ku ci gaba da zama, wallahi duk wadda ta kwana a gidan nan sai dai gobe taje kwaso kayanta a gidan aurenta".
Ya kalli matarsa ya ce,"ke kuma tashi mu wuce". Yana faÉar haka ya fice fuuuu, ni dai nayi ta mamakin inda yaji labarin, amma nafi tunanin Lubabatu ce ta zayyana masa komai.
Da daddare har na fara bacci kiransa ya shigo wayata wai na zo na sameshi, har zan banza da shi kuma dai na fita. Ina sakkowa naji suna maganar a Abuja za'a Éaura auren, wasu za su bi jirgi wasu a mota kuma duk shi ya Éauki nauyi, raina na ce an gaida me kuÉin duniya, na kyaÉe ba ki na shige Éakin nasa. Na sameshi yana faman shan Æamshi ban wani bi ta kansa ba na haye gado na kwanta, sai can bacci ya fara Éaukata naji yana lalubena, yanda ya nuna min yunwarsa dan dole na sallama masa yayi yanda ya so da ni. Bayan lafawar komai ni na fara wanka kafin shi, ni dai wannan daren shi yay bacci ni ina daga gefensa ina kallonsa, azababben kishinsa mai tsanani naji ya mamaye zuciyata, tunani da lissafi kawai na ke yi akan ta yanda abunda na mallaka tsawon shekaru takwas zai koma mallakinmu mu biyu, shikenan yanzu duk irin salon abubuwan da yake yi min a shimfiÉa itama sai yayi mata? Kuma yanzu yafi sonta akaina?
Na rumtse ido ina jin zuciyata na faÉa min dole in miÆe tsaye don ba zai yiwu na bar mata shi ba.
Da asuba bayan ya dawo daga masallaci ina ji ta kirasa a waya, ina ga d