fiyya".
"Shi wa?".
"Mijin nawa mana".
Wani zabura tayi daga kan gadon da take kwance tare da faÉin,"A'uzubillahi". Sai kuma ta danno ashar ta ce,"kina nufin kishiya aka yi maki?". Na ce,"za dai ayi gobe in Allah ya kaimu". Yadda ta daki Æirjinta da Æarfi ina iya jiyo sautin dukan ta ce,"kuma sai kike mene ke yanzu?". Yanda tayi maganar kaÉai ya sakani sakin murmushin da ban shirya ba ina Æara haskota da yanayin al'amuranta a cikin idona. "Beb na ce sai kike mene yanzu da za'ai miki kishiya?". Na ce,"sai na ke zaune mana gani muna waya da ke ina jin daÉi". Ashar ta Æara lailayowa ta yarfa min. "Sa'ida Salman Madobi bura'ubanki na ce, za'ai maki kishiyan kike gaya min kina zaune miji da amayarsa na can hotuna na yawo a media ba ki tafi kin bankawa Æ´an iska wuta sun babbake ba, kai Allah ya tsinewa sanyin halin da na sanki da shi. Kar dai ki ce min babu wani mataki da kika Éauka kan lamarin, na wawoo i cant imagine wai Nazifi ne zai miki kishiya, hey duniya ba tabbas wai yau Nazifin Sa'i zai haÉata da wata, hewoo ni ko ina zan taÉa yarda da namiji".
Na ce,"Wai ba zamu gaisa ba ne Safiyya kina ta faman magana".
"Ba za'a gaisa ba Éin, za ki hanani magana saboda na taÉa zuciyarki. Kin san yanda na kaÉu da lamarin kuwa? tukunna ma! kuÉi ku ka yi ne don naga ba shigar tsumma yay ba, kuma yay Æiba ya murmure abunsa har da tumbi, if i guess right Nazifi Mai Kalwa yay kuÉi ya juya miki baya shine har zai Æara aure. Ke kuma shashasha Sauna kina kallonsa you didnt take any worst action. Wait let me drink cold water becoz ina jin numfashina na seezing kar in faÉi in mutu lokacina bai yi ba".
Ina jiyo yanda take kwankwaÉar ruwa, bayan ta gama sha tace,"Na fi kowa saninki, ba ki komai ba akan lamarin auren nan, ba kuma za ki ba, kina nan kina kuka idan kika gama ki kama kiran sunan Hubbi. To Hubbi ya ci bantan bura'ubansa Éan shegiya annamimi butulu mara halacci. Kinga kina jina ba, just give me your address ina lagos yanzu haka na zo wata seminar, zan yi hayar Æ´an daba mu zo gobe, sai na sa an karairaya Nazifi Sa'ida kinji na faÉa miki, ita kuma shegiyar da ke ÆoÆarin shairing miji da mijin Æawata zan yanke mata nonuwa duka don uban babanta, lamarin Nazifi wasa ne. Kinga gida guda za ku zauna?".
Shiru ban ce da ita komai ba, gwara na barta ta gama zazzaga masifar sai muyi wayar arziÆi. jin shirun na wa kuma yasa ta cewa,"kai Allah ya kwashewa Nazifi albarka kasa ya ÉaiÉaice, ya rasa wadda zaiwa kishiya sai ke Sa'ida, Allah ya isana ban yafe masa ba wallahi, ina ma mota tabi ta kansa ya mutu dama ai ba son aurenku na ke ba".
Nasa hannu na goge hawayena, sai kuma kukan yaci Æarfina na kasa riÆe shi. Nan hankalina Safiyya ya tashi ta sassauto ta shiga lallashina har sai da nayi shiru. Na bata labarin komai da ke faruwa, tayi shiru kiran yana ta tafiya sai da na kira sunanta kana ta ce,"na suma ne bari na farfaÉo tukunna, ai ban san abun yay tsamari haka ba, ke kuma duk kika manta kina da ni, ko da ya ke ba wani sona kike ba dama kin fi son wannan gantalallan mijin naki".
Nuna mata nayi bana son tana zagar min miji, hakan yasata cewa,"Am sorry Beb amma zan shigo kano just becoz of you indai ina da rai da lafiya. kin san ina jin magananki so nayi shiru da zage zagen, Nazifi ne yaje da halinsa amma wallahi ba zan fasa tsine masa ba kuma Allah yasa matan ta kwashe kuÉinsa duka ta gudu ta barsa da paralyzed, kuma ba zai taÉa haihuwa ba ko zai auro mata Éari, ina ma abun nasa ya ruÉe in ga ta inda shi zai haihun".
Kai na girgiza kawai na ce,"kinga mayi wayar wani lokacin".
Na faÉa ina kashe kiran don ba zata daina wannan mugggan adu'an da maganganun nata ba, bata san zata iya faÉa a bakin mala'iku Æ´an amin ba.
Da Yamma ina kwance Éaki abun duniya ya ishe ni Hajjo ta zo ita da yaranta biyu Amina da na ke kira Mamana da kuma Muslimata. bayan mun gaisa na kawo musu abun sha tana kallona tace min,"Nazifi ya kira ni ya karanta min duk halin da ake ciki, faÉan da kika ji ina yi miki Éazu nayi ne saboda fuskantar yana wajen. Mahaifiyarki ta faÉa min gaskiyar komai dan ko da muka yi waya da shi ba yarda da zancensa nayi ba, namiji me kai Æara ba abin yarda ba ne. Daga can gidan naku na ke yanzu, itama mun yi magana ni duk sai yau na ke jin komai, tana ta faman nanata min kalmar haÆuri kin san hali, na ce mata ai shiyasa mata da yawa ake wayan gari zuciyarsu ta buga sun mutu saboda baÆin cikin Éa namiji, to Æilan kema so take ki mutu ina jin dai sun gaji da ke ne. anji haÆuri ba ya yawa kuma me haÆuri shi ke da riba amma irin haÆurin da ke kike yi ba komai ba ne sai cutarwa Sa'ida, kawai saboda kina da haÆuri sai aka ce kike Éaukar kowanne cin kashi, bama na miji ba kawai har da Æanne da Yayye, anji mahaifiyarsa idan ta miki anan ki kauda kai, amma banda Æ´an uwansa saboda haka ki takawa kowa burki Sa'ida kina jina, ko matarsa ce ta shigo karki wa