NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 73 of 97

i min akwatuna na watso su waje. Na miƙa masa wayarsa suka ci gaba da magana da ita, ina ji tana ce masa,"kayi haƙuri Nazifi, na dai yi mata faɗa idan taji ta gyara shikenan, idan kuwa bata gyara ba kanta ta yiwa kuma ba kowa ta wulaƙanta ba sai iyayenta". Yay mata godiya suka yi sallama, ya fita a ɗakin na raka shi da kallo, kafin na miƙe cikin karaya wasu zafafan hawaye na sauka akan kuncina yayinda a zuciyata na ke faɗin tsakanina da Nazifi sai Allah ya saka min. Shayi na dafa na zuba a flask daidai cikin mutum guda, kana na ɗora taliya fara dama akwai sauran miya. Don haka abincin da na haɗa na daidai cikin Iyam ne ita kaɗai, na ɗeba na kai mata ɗaki, basu ma san da shigowata ba saboda shewa da hayaniyar da suke yi, can na hango Iyam daga wajen wadrobe ɗinta ƴaƴan jikoki sun sakata gaba tana yi musu wasa, na wuce mutanen kan hanyar da babu wanda ya amsa sallamata a cikinsu, na durƙusa har ƙasa na bata haƙuri bata dai ce da ni komai ba na ta shi na fita bayan na aje mata abincin, ina jin Ummaa na faɗin Allah ya shiryeni yasa kishiya ta koya min hankali, a raina na ce ta dai koya muku. Da rana ina zaune da waya a hannu, na kunna data na hau whatsapp, da ma ni shi kaɗai na ke dan shi kawai Nazifi ya yarje min in ke yi, babbar wayar ma da ƙaƙa ya bari na riƙe, Ina cikin kallon status na buɗe na Adamu ƙaninsa, nan take na yi karo da hoton da ya zamar min yajin albasa a ido. Hotuna da bidiyo na Nazifi da Amayarsa, irin hotunan nan da ake yi na kafin aure, kasa ɗauke ƙwayar idona nayi akai, kyan da suka yi ko hasidin iza hasadun, shi ya saka yadi me tsada ita kuma cikin wata doguwar riga ta net, kana ganinta ka ga jinin shuwa, hanci kaman tsinin biro ga ido da gashin ido masha'Allah, ba ƙarya tana da kyau iyakar kyau irin kyan da namiji ba zai gani ya ƙyale ba, wataƙila kuma wannan kyan shi ya ruɗe shi domin a rayuwarsa yana matuƙar son kyakykyawar mace. da gani ta girmeni kam zata iya ba ni shekaru uku, idonta kaɗai zai shaida maka a waye take kuma tasha boko kamar yanda ya faɗa, ban san lokacin da na jefar da wayata ba ganin yacca a bidiyon yake faman ruƙota zuwa jikinsa ita kuma har tana kwantar da kai a ƙirjinsa. Kaina na jinginar jikin gado ina hawaye sosai. Tsawon wani lokaci wayata tayi ƙara na ɗauko, sabuwar lamba na gani a jiki, muryata na saita kana na ɗaga tare da yin sallama. Daga can ɓangaren aka ce,"Ke Sauna ba hoton mijinki da wata na ke gani ba yana yawo a IG?". Muryar kawai ta shaida min wacece, kuma sosai nayi farin ciki da kiran nata, Safiyya ce ƙawata ta ƙud da ƙud tun aji ɗaya a makarantar boko, ita kaɗai ce wadda yau zan nuna in kirata da sunan ƙawa, ina sonta fiye da yanda take sona kamar yanda itama ke cewa tana sona fiye da yanda na ke sonta, rabona da ita kusan shekara uku da rabi kenan da Babansu Allah ya ɗaga shi gwamnati ta ba shi matsayi suka koma Abuja da zama. "Hello Beb". Na murmusa kuncina kaɗan murya a sanyaye na ce,"Na'am Beb". Ta sauke numfashi da cewar,"ohh i thought i was mistaken in ce wa kuma zan ƙara nema ya ban numbernki...hey tukunna ma are you well naji muryanki somehow cool". Na ce,"Safiyya natsu muyi waya da kyau mana har yanzu kina nan yanda kike, kuma ni ki min hausa zalla ki daina haɗa min da turancinki tunda kin zama baturiya". Tayi dariya sosai kana tace,"To matar Ustaz ai ni ban iya larabci ba balle nayi miki. Beb ba fa ki da mutunci wallahi, kinga wahalan da na sha before i gat your number, i so much missed you almost four years. Bamu da zumunci gaba ɗayanmu mun zama wasu ƴan banza". Na ce,"ai ni ina gwada lambarki bana samu". "Eyyah that number ai ba yayi, tun da naje saudiya na jefar da layin shikenan nima sai na rasa na ki, ba yanda ban yi ba wajen in sameki na rasa, in ta shiga kafafen sadarwa ina searching sunanki bana gani, ke har yanzu kina nan da duhun kai". Da murmushi nace,"Yanzu ai na kika samo lamban nawa?". "Akwai wata something Tijjani oho that fat girl dai da ta nace miki na tsaneta, sai da na ɗauke numfashi aka rirriƙeni kana na iya kiranta fa na ce ta bani lambanki, itama numban nata wurin Uncle Maths na samu kin san Yayanta ne, Beb ina kishinki sosai". "Hmm Allah ya shirya min ke. yanzu dai mu gaisa ina Baba da Mama?". Cikin saurin maganar nan tata ta ce,"Ke Babanmu ma ya ƙaro walaƙanci ya danƙarowa Mama kishiya ai kuwa na kora kishiyar in faɗa miki, bari wannan labarin sai mun haɗu. Yanzu kina jina na shiga IG ne ina kallon page na arewaweddings i then came across a picture of someone who looks like your husband, har na wuce kamannin suka tsaya min a rai na ce sai na nemeki na ji. Mijinki ne ko Ya?". Na ce,"a me kika gansa?". "Umm like ango haka, wallah sak mijinki kin san Allah mai halitta sai ki ga me kama da ke ma. Amma dai wannan na san ba shi ba ne kama ne kawai may be kuma brother nasa ne ba?". Na ce,"Shine Sa
🏠