a kuma cikin huci take faÉin,"barni Suwaiba in daki yarinyar nan ta gane Annabi ya faku, Æ´ar cikina tayi min rashin kunya in Æyaleta, idan ban sa Yahya ya ÉaÉÉalata ba shegiya na ke sai dai muyi shari'a. Kamarta fa na shayar da wannan Nonon". Ta faÉa tana nuna nononta da kuma juyawa ta kalli Fati ta ce da ita,"ke sauka kira min su Mardiyya ni ba zan yi da ita ba sai dai ƳaÆ´ana".
Ko Éar ban nuna mata tsoro ba, ina tsaye yanda na ke Æam su ko sai faman haÆuri suke bata, ni dai abu Éaya kawai na sani ba zan daku ba kuma ba zan yi duk abunda za'a saka ni ba sai idan naga dama. Nazifi ne ya shigo duk kuma sai suka ja da baya suna ba shi wuri, ya kalli Yayan yana ce mata,"me yake faruwa?".
Daga tambayar kuma sai ta kama balbale shi da masifa, ai ya barni duk na raina su bana ganinsu da Æima, Æarshema rashin mutuncin nawa har ya kai ga kan mahaifiyarsu, shi kuma da bai san darajar uwarsa ba ya bar matarsa na barinta da yunwa, to ko ya Éau mataki ko kuma ita ta Éauka da kanta. Shi kuwa cikin girmamawa ya shiga bata haÆuri kana ya juyo gareni nima yace na bata haÆurin, ba don raina ya so ba na ce tayi haÆuri kana suka fita a Éakin su ka barmu.
Tun bayan fitarsu ban kalle shi ba na nemi wuri na zauna. Ina jin kallonsa a jikina wanda na ke hango fuskarsa ta cikin madubi na shaida tsananin Éacin ransa. Can yay nisa ya ce da ni,"me ya hanaki yin girki?".
Kai tsaye na ce,"saboda bana jin yunwa".
"Idan ke ba kya ji sauran mutanen da ke cikin gidan fa?".
"Wanda nauyin dafa masa ke kaina ma ban dafa na ba shi ba".
"Kina nufin me kenan Sa'ida?".
"Ina nufin mijina ma ban dafa na ba shi ba balle wasu da hakkin ci da su ba a kaina ko na me gidan yake ba, wanda ya damu da yaci ai ya san hanyar kitchen".
"Har da mahaifiyata?".
Nayi shiru ban ce masa komai ba, ya Éaga murya da ke shaida Éacin ransa ya ce,"tambayarki na ke yi har da mahaifiyata ma sai dai ta shiga ta dafa da kanta?".
Shiru na yi na Æi cewa komai. Yay Æwafa yana jijjiga kai kafin ya Éauko waya a aljihu, bayan wucewar sakannin da ba su wuce goma ba na ji yana faÉin,"Kiyi haÆuri Hajjo zan takura ki, kamar yanda na faÉa miki ne dai a Éazu na kasa yin shiru kan abubuwan da Sa'ida ke min a gidana saboda bana so azo ga matakin da kowa ba zai ji daÉinsa ba, ta san me ya faru a baya to ina tausaya mata shiyasa ba zan mayar da ita gaban su Kaka ba don har yanzu ta kan hukuncin Abbaa da ya yanke mata na rashin zuwa gida, amma hakan bai sa ta gyara Éin ba".
Ai yana cewa Hajjo na zuba masa ido, idan nasa mamaki a matsayin kallon da nake masa tabbas na yiwa kalmar rashin adalci.
"Tom shikenan gata". ya miÆo min wayar na karÉa ina kallon screen Éin da ke Éauke da sunan Yayar mahaifiyata Hajjo, Æirjina ya buga na runtse ido nasa wayar a kunne, ina ga dai hankalinsa ba zai kwanta sai ya shiga tsakanina da kowa nawa tukunna, ita kuma ko me haÉa ya faÉa mata oho, kai Namiji Æayar ruwa baka san da ita ba sai ka taka, kamar yanda ban san da wannan Éoyayyan halin na Nazifi ba sai a yanzu da duniya ke gara masa.
Hajjo ta katse Sallamata da ce min,"ke kuma mijinki yay ta kai Æararki hakan kika zaÉarwa kanki ko Sa'ida?".
Na rumtse ido ina jin zuciyata na bala'in matsewa, muryana a hankali kuma a raunane na ce,"ba haka ba ne Hajjo kiyi min alfarmar tsayawa kiji ta bakina kar ki yanke irin hukuncin su Kaka...".
Murya ta Éaga wajen dakatar da ni,"dalla can rufe min baki, wanne irin iskanci ne da rashin sanin darajar iyaye yasa za ki Æi dafa abinci ki bawa uwar mijinki, dan ubanki da bata haiifa ba har kya ganshi ki so ki aure, wawiya kawai idan ba ki bi uwar miji ba ta ina za ki kama mijin naki a tafin hannu, ko haka kika ga matan yayyunki na wa mahaifiyarki, ba gida guda su ke ba amma kullum da kwanon abincinta a gidan matar Sa'id. Kishiya kuma akanki a ka soma? kaf cikin mu biyar da mahaifiyarmu ta haifa wa kike gani tana zaune ita Éaya banda mahaifiyarki? Kuma Æ´an uwanki Samira da Husna duk ba kishiyoyin ne da su ba, kin taÉa zuwa kinga wacca kishiyarta ta zauna akanta? Ko kin taÉa jin wata cikinsu mijinta ya kai Æararta akan kishiya, sai ke saboda sakarci da shashanci za ki Éata rawarki da tsalle, to ki shiga taitayinki wallahi, kar na Æara jin makamanciyar magana irin haka ta kin hana uwar mijinki abinci, ita kam ko ce tayi ki kwanta tabi ta kanki ki kwanta biyayya dole, Saboda haka yanzu muna gama wayar da ke ki wuce ki girka abinci ki kai mata tare da bata haÆuri kina jina".
Na Éaga kai kamar ina gabanta na ce,"zan bi umarninki in yi yacca kika ce in sha Allah".
Sai kuma ta kama yi min faÉa sosai akan rashin bashi hakkinsa da na ke, shi ko kunyar kai mata wannan Æarar ma bai yi ba. Tana faÉan tana haÉawa da aya da hadisi har ta gama kana mu kai sallama da ita bayan ce min da tayi tana tafe nan da anjima zata zo in gwada mata kalar iskancin da nake yi tunda har an iya aka