NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 71 of 97

ce ya gaida su Yasmin da Ajmal sannan na ajiye wayar daga gefena. Har na aje wayar sai kuma na ɗauka na kira Ummani, itama hankalinta ba ƙaramin tashi yay ba da ganin kiran nawa, musamman da ta jini ina kuka sosai. "Sa'ida me yake faruwa ne? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". "Ummani aure zai ƙara kuma bai faɗa min ba tsabar bai ɗaukeni da daraja da ƙima ba a cikin gidan nan, Ummani na gaji ni kam na gaji ba zan iya ci gaba da zama ba don ban san da manufar da ya ƙullo auren ba, ki cece ni Ummani kar su kashe miki ni da baƙin ciki". Daga ɓangaren Ummani ta jinjina kai tayi shiru domin ita kanta lamarin ya taɓata, ƙarin aurensa ba abun mamaki ba ne, kawai ta yanda ya ɓullo da lamarin wajen ƙin shine abin takaicin da ɓacin rai. To ya za'ayi ita uwa ce, bata da wani kalami da zata faɗawa ƴarta wanda ya wuci nasihar dai da ake yi kullum, sai kuma ta kwantar mata da hankali, in ace ma Abbaa ya sauko ne sai tace to da safe ta taho gida ta zaune ta rage zafi in suka gama bidirin bikinsu ta koma in ƴan uwan nasa sun bar gidan, amma tabbas Nazifi bai kyauta ba ko kaɗan, ita tsoronta ma kar su illata zuciyar ƴarta amma babu komai adu'a bata bar komai ba, tana yi mata za kuma ta ƙara dagewa akan hakan. Da kalamai masu daɗi da tausasawa mahaifiyata taita lallashina tana bani baki tana nusar da ni fa'idar haƙuri da ɗauke kai da miƙa dukkan lamura ga ubangiji, da sannu komai zai shuɗe ya zama tarihi. Tun bayan gama wayarmu da Ummani na kwanta babu abunda na ke sai hawaye, hawayen da sai da ya jiƙa filon da na ke kwance, ban san dalilina ma na damuwa akan lamarin auren nan ba, ai tun ranar farko da Yaya ta zo taci zarafina na sakawa raina muddin ba haihuwa nayi a gidan nan ba ba fa zan huta da gori da cin mutunci ba, aure kuma kamar Nazifi ya riga yayi ne na san da wannan don da hankalina ai da tunanina take takensa kaɗai sun isa su sanar da ni hakan, to da yake dai kishi halitta ce a jikin tsokar zuciya babu yanda zanyi sai dai nayi ta adu'a Allah ya sauƙaƙa min, sabon tozarci ne dai na san zan fusance shi idan matarsa ta zo, haka nayi ta faman lissafin yanda zan fara gudanar da sabuwar rayuwata a cikin gidan daga gobe. Kaman yanda na saba cikin dare nayi sallolina na kaiwa Allah kukana, karatun ƙur'ani tunda na fara sai da na sauke izu goma ina karatun ina kuka, kuma kaman ɗaukewar ruwan sama haka hawayen idona ya ƙafe babu ko saura da ke son fitowa daga zuciyata, wani ƙwarin gwiwa na shigana wanda ban taɓa jina a cikinsa ba dangane da abunda na ƙudurta a raina. Washegari da safe ban farka ba sai wajen ƙarfe goma na safe duk da ba baccin daɗi nayi ba, Lubabatu dai ta leƙo wajen takwas tace Rumana ta fito za'a kaisu ƙunshi da kitso to tunda na mayar da ƙofar na rufe ban ƙara buɗewa ba duk da naji an zo an buga nayi biris. Shi kuwa dama yau ban shirya zan leƙa wurinsa ba sam balle tunanin abunda zan shirya masa ya ci. Na yi wanka nayi shirina nai zamana a ɗaki na kunna data na hau online don ɗebe kewa amma duk da haka can cikin zuciyata na ƙarayin babu daɗi, ina cikin tunanin abunda zai faru tsakanina da su idan na fita sai kawai ganin Yaya nayi ta shigo cikin ɗakin babu sallama tana banka min uwar harara, ban san garin ya aka yi na mance ban saka maƙulli ba don ni ƙudirin da nayi yau cikinsu babu me ganina. Ƙirjina ya buga na sauke dogon numfashi, kafin tayi magana cikin sanyin jiki kuma a tsorace na ce,"ina kwana". Ta zuba min ido wajen kallona ta ce,"da ban kwana ba za ki ganni ne tsaye gabanki, wato ke ba ki da mutunci ko, wuyanki har yay riƙar da gari zai waye ki ƙi sakkowa ki dafawa mahaifiyarmu abinci saboda ba ki da tarbiya ba ki san darajar iyaye ba, idan uwarki ce za ki hanata abinci ko da ita ta saka aka yi miki kishiyar?". Kaina a ƙasa na ce,"don Allah kar ki ƙara sako mahaifiyata kiyi komai akaina ni ɗaya". Ai kuwa ta fusata tayo kaina zata mareni na riƙe hannun da ƙarfin da ban san ina da shi ba, a hankali na sakko na tsaya gabanta ina kallon cikin idonta na ce,"Kin bani shekaru sama da sha biyar, a haife kuma kin haife ni, ba iya aurar da kamata kika yi ba har jikoki kina da. Bai kamata ace da girmanki kina dabi da ƴar cikinki ba kuma matar ƙanin ƙaninki, kamar hakan abun kunya ne, don haka na roƙe ki kija sauran guntun mutuncin da nake ganinki da shi kar kiyi saken da zan bi ta kai in taka na wuce, bana saurin rama abu ina da haƙurin shanyewa amma duk ranar da tura ta kai bango babu wanda zai ji daɗina, ba zan so in gwada miki a yanzu ba saboda darajar ƴarki da ke hannuna". Kallona take yi cikin tsananin mamaki, sai kuma ta harzuƙa ta ƙwace hannunta da na ke riƙe da shi tana faɗin sai tayi min duka taga wanda ya tsaya min. Hargaginta ya janyo hankalin ƴan ƙasa sai ga su yuya guda kamar za'ai yaƙi. Suwaiba matar Yaya Babba ce ta riƙeta tana bata haƙuri, it
🏠