NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 70 of 97

ta. na miƙe na ƙarasa na buɗe, ta na jin na cire key kuwa tayi saurin danno kai ta shigo ta mayar ta tura ƙofar tana cewa,"Anty sauri saka key". kallonta na tsaya yi duk a tsorace ta ke. "lafiya?". Ta marairaice fuska kamar zata yi kuka sai kuma ta rungume ni tana saka kuka tana faɗin,"Anty ki daina fushi da ni Allah na daina yi miki duk irin abunda mu ka yi miki a baya, wallahi ba zan ƙara ba anyi mana wa'azi a islamiyarmu ma, ina sonki Anty". Na janyeta ina cewa,"na ji, yanzu ya aka yi?". Shiru tayi bata ce komai ba, don haka na mata nuni da ƙofar ina cewa,"to je ki sai da safe". Na faɗa a hasale don haushin kowa da ya shafi Nazifi na ke. Ta kama hannuna tana ta min rantse rantse da ba ni haƙuri har dai na ƙyaleta, sai da na koma na zauna ina lazimi kana take ce min wai haka aka ce su je su faɗawa Abbansu suna jin yunwa kuma tun rana ban ba su abinci ba, shine ita ta gudo Atika kuma ta tafi. Gajeriyar dariya kawai na yi, na rasa wannan bala'i na su na rashin son in zauna lafiya a gidana, haka kuma na rasa masifa da jarabar da ke cikin so da duk abunda ke faruwa har abunda ya faru a yau na ke jin Nazifi a raina. Rumana ta miƙo min homework ɗinta in yi mata, na karɓa na duba sai naga english ne kuma turancin kam yafi ƙarfin kaina tunda dai ni ba wani jinsa na ke sosai ba balle ma har na wani iya bayani akan abun da aka tambaya. nace ta tashi ta kaiwa Fati tayi mata amma ƙememe yarinyar nan taƙi wai sai da safe yanzu idan ta fita za'a iya dukanta. bayan na gama jin karatun da aka yi musu a islamiya sai ta kwanta bacci. Ina zaune har ƙarfe tara kan darduma na kasa kwanciya, haka ban san ma tunanin me na ke yi ba. hannu na miƙa na ɗauko wayata ina sauke ajiyar zuciya, so na ke nayi waya da wani ko na ɗanji salama cikin zuciyata, bashin kamfani na ciwo na nera ɗari na danna kiran Maman Yasmin, ko da ta ɗaga muryarta da nuna tsananin damuwa take tambayata lafiyata da wannan daren haka. ban san lokacin da na fashe mata da kuka ba ina cewa,"Maman Yasmin aure zai ƙara". "Aure? Nazifin ne zai ƙara aure?". "Ehh Maman Yasmin, ɗazu ma su ka kai lefe jibi ɗaurin aure, ban san ya zan yi ba Maman Yasmin ina ga Nazifi so ya ke ya kashe ni, wallahi yanzu haka zuciyata ciwo take yi min, kuma Maman Yasmin ina sonsa ba na son wata tayi silar rabani da shi". Maman Yasmin tayi wani murmushi da sautinsa ya fidda jin daɗi ta ce,"To kuma sai mene na kuka Sa'ida? Sai me don Nazifi gayyar tsiya zai ƙara aure? Ke yanzu har wani kishinsa kike bayan bai ganinki da mutunci daidai da ƙwayar zarra, to ni wallah ce na ke ma kin daima sonsa kina dai zaune ne jiran ƙaddarar da ta haɗa ta zo ta raba". Sai kuma ta numfasa ta ƙara cewa,"in faɗa miki gaskiya wallahi mugun daɗi naji ba kaɗan ba da batun nan, ai gwara ya ƙaro auren ya kawo wacca zata ci kutumar ubansa ta gasa masa aya a hannu da shi da duk ƴan uwan nasa tunda ke kin kasa ƙwatarwa kanki ƴanci. Allah ne ya dubeki ya kawo maki mafita, saboda haka ki bar damun kanki ki zuba ido kiyi kallo kina daga kwance za'a rama maki duk abunda aka yi miki. da yardar Allah auren nan sai ya saka su cikin baƙin cikin duniya ƴan bantan uba marasa mutunci, za su auro daidai da rashin mutuncinsu ne don ba za su samu wacca za su juya irinki ba lusarar banza da haƙurinta ke halakar da ita". Haka Maman Yasmin ta dinƙa zazzaga bala'i, ita da na kira ta kwantar min da hankali, ƙarshe sai ga shi zage zagen da take ya haɗe har ni, wai saura in bari kuma idan Amaryar ta zo na bata wuri itama ta takani son ranta. Awannan gaɓar ba shawara ko haƙuri zata bani ba har gida zata zo tayi min mugun dukan da zan kasa motsi. Yashaik ne ya amshe wayar daga hannunta don yanda take bambamin bala'i tamkar ita za'ai wa kishiyar, to da yake shima yanzu ya san komai dangane da halin da nake ciki, don lokacin da ya takura kansa da zuwa gidan C.I.D ɗin da Kaka ya saka shi, Ummani ta zaunar da shi ta fahimtar da shi komai, da ike indai ta faɗi abu to ko ba haka ba ne ya yarda kawai, cikin ikon Allah kuma sai gashi ranar ya zo ya taradda Yaya na yi min tijara shima Nazifin nayi min, dama yana daga ƙofar falo zai shigo yaji duk abunda ke faruwa, shigowar da bai yi ba kenan ya juya, a daren ranar ya kirani yay ta bani haƙuri ya kuma lallasheni shima yay min nasa nasihohin, har yake cewa zai bani jari sai na faɗa masa ai tuntuni Nazifi ya hanani sana'a kowacce iri, wai in ba a aikin gwamnati ba matarsa ba zata yi kasuwanci ba tasa a ke masa kallon ƙaramin mutum. Tunda Yashaik ya fara lallashina da kalaman kwantar da hankali gami da nasiha mai ratsa jiki, wallahi sai naji tamkar Abbaana, dama shi komai nasa na Abbaa ne hatta muryarsa wani lokacin. cikin ƙanƙanin lokaci sai naji raina ya fara washewa a ƙalla baƙin cikin Nazifi ya ragu, bai barni ba har sai da yay silar da na saki murmushi mai sauti, da haka muka yi sallama bayan na
🏠