hil azim idan ba ki bar min magana ba zan zabga miki maruka a wannan damammiyar fuskar taki da ta zame mana musiba cikin ahali, kuma ki kwashe kayanki tun da ban ce miki a yunwace nake ba".
Ni dai ban ko motsa ba kaina na Æasa ina ta biya kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Yayin da ita kuma na ke jinta tana ci gaba da faÉin,"haba wannan wacce kalar annoba ce, yarinya sa'annin aurenku duk sun haihu daga masu Æ´aÆ´a biyu sai uku, amma ke kina zaune sai dai a ciyar da ke ki cikawa mutane masai da kashi, aure shekara takwas babu wani labari, ai wallahi da sake a wannan lamarin, dole a duba".
Furucin nata yasa na Éago da sauri na kalleta, ta Æara jefa min wani matsiyacin kallon tace,"Æarya na miki?, ko sharri na miki?. to ki kira min mijinki duk inda yake ya dawo ina son magana da shi, yazo ayiwa tufkar hanci, ba zai yiwu yayta Éawainiya da ke yana faman hidimta miki amma kin kasa biyansa da ÆyanÆyasar Æwai ko guda, gida har gida kamar wannan ace babu Æ´aÆ´a, wa zai gaji uban dukiyar da aka tara?, to idan shi baida hankalin tunani da lura mu Æ´an uwansa da muka san ciwonsa zamu nemi mafita. Yazo ya Éauke ki a daren nan kuje asibiti ayi miki gwajin haihuwa, idan haihuwar ce ba kya yi muji, idan kuma irinku ne masu dogon jinkiri shima muji, ke idan ma da gayya kika hana haihuwar zamu ji ai, don ni nafi tunanin mugunta ce irin ta Éiyar talakawa, bai wuci zuwa kika yi aka sa miki tsarin iyali ba. Yo me ma ake da Æarin aure da ba zai yi ba ya ke ta zama da baÆar aniya, ai wallahi muddin Éaya cikin abin da na lissafa ba za'a shafe wata guda curr ba sai ya Æara aure tunda ke ba abar mora ba ce, gwara auren wadda ahali za suyi alfahari da ita, waye ba ya so yaga zuri'arsa?, yo wannan ma ai cutarwa ce ace yana zaune da macen da bata haihuwa, me amfanin auren?, Ai ko ma'aiki cewa yay kuyi aure ku hayayyafa domin in alfahari da ku ranar gobe Æiyama...don haka Maza maza tashi kira min shi a waya, kuskurena ne ma da ban zo da tawa ba, ki kirasa yazo kuje asibiti yanzu yanzu, wallahi ko haihuwa ko Æarin aure, ba za'a ci gaba da zama a yanda ake ba".
Maganganunta duk sun saka jikina Éari, cikin kaina babu abin da ke nanatuwa sai kalmar rashin haihuwa da Æarin aure, wato duk a baya basu san da matsalar rashin haihuwar ba sai a yanzu. Kuma har tana da bakin kirana Æ´ar talaka, ehh lallai ciki mai manta kyautar jiya, saurin share hawayena nayi ina ÆoÆarin daidaita yanayina, domin kuwa tun da har na gano manufarsu ta tsangwamata to ba zan taÉa bari suga raunina ba, ballatana su Æara samun damar cin zarafina yanda suke so.
"Ba kiji me nace miki ba ne, ki tashi ki kira min shi a waya, ni ba wajenki na zo ba balle ki sani a gaba da kirsa".
Hmmm Éan Adam kenan mai wuyar gane hali, dama ai shi gwano ba ya jin warin jikinsa, ban da haka mancewa tayi Æ´arta ta fari har yanzu bata haihu ba, shekararta goma sha shida da aure shiru babu labari, kuma babu wanda ya tsangwameta Æarshe ma Éa aka samu a dangi aka bata, sai ni da ban ko rufe shekara goma ba zata Æwazzafe ni, ta Éaga min hankali, ita ba Éanta nake aure ba, yo ko Éanta na ke aure irin rayuwar da na yi da shi ai ta shafa min lafiya.
Ji nayi ba zan iya yin shiru ba da zage zagen da take ta yarfo min, hakan yasa murya a hankali nace,"Yaya dama wannan shi ne kuskuren nawa wanda yasa duk ku ka juya min baya?, soyayya ta koma Æiyayya?, akan abin da bani na Éorawa kaina ba, akan lamarin da yake na ubangiji shi ne ake tsangwamata haka. Yaya haihuwa fa ta Allah ce na san kin sani, haka duk wanda ya haihu ba shi ya bawa kansa ba, kuma duk wanda aka haifa ba shi ya haifi kansa ba. in har ace ina da iko da haihuwa ai da tuni wani labarin ake, domin nima ina so na ganni da zuri'ata, na ga yau na kafa nawa ahalin".
Muryata ce ta raunana a daidai wannan gaÉar, sai dai ban bari ko kusa ta fahimci cewa kuka nake so nayi ba, tabbas ba zan juri wulaÆanci ba matsawar akan wannan matsalar ce, ai bani kaÉai zan haihun ba, dole sai da Éan uwan nasu, don haka muddin za'a duba lafiyata akan rashin haihuwata to shima sai an duba tasa. Maganarta naji a tsakiyar kaina tana faÉin,"kin gama min wankin babban bargon?, Nace kin gama zagin nawa?".
Na kasa danne abin da nake ji a Æirjina na Éago kaina ina kallonta, lokacin ta miÆe tsaye tana gyara yafen mayafinta, na rumtse ido nace.
"Ki haÆuri ban faÉa miki komai da rashin kunya ba, iya gaskiyata na faÉa, haihuwa ba ni zan bawa kaina ita ba Allah ne mai bayarwa, kuma mafi aksarin jinkiri alkhairi ne, bamu san mai Allah ya shirya mana ba, da haihuwar yuyuyu gwara haihuwar babu, rayuwar nan ba'a Æareta ba duk da bamu san gawar fari ba, amma ni ina da yaÆinin ba zamu kai ga kushewa ba sai Allah ya azurtamu da haihuwa, sai Allah ya bamu mai jin Æanmu da alfaharinmu. Kar ki tafi zan kirasa a waya muje asibitin yanzu a duba ni, amma don darajar Allah kar ku yanke hukuncin Æarin aure,