NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 69 of 97

a na auri Nazifi da yanda ahalinsa su ke a baya, la shakka sai anyi rubutun babban littafi na butulci akansu. Ni dai duk ɗage ɗagen kayan da su ke yi kaina na ƙasa, na ƙagu su tattara su kwashi kayansu nima in tashi in bar wajen. Ƙawar Iyam ta kira sunana tana cewa,"Uwar gida ba ki ce kaya sun yi ba". Iyam tayi caraf ta ce,"tana baƙin ciki ai bata faɗa ba, wa ya san me ke zuciyarta yanzu. Kuyi kuyi a rufe su kafin ta cinna musu wuta". Ni dai ban ɗago ba kuma ban yi magana ba, banda kuma niyyar cewa ƙala, duk da irin shewar da suke yi na daɗa ƙona zuciyata, kuma dama na san an kira ni na zo ɗin ba don komai ba sai don a ƙuntata min. Ummaa har faɗi take yi wai to duk irin hidimar da Nazifi yay min har na yi baƙin ciki da aurensa ko hidimar da yaywa matar da zai aura in dai ba rashin halacci irin nawa ba, kuma banda abuna ɗan miji ai ɗanka ne, idan ta zo ta haifa duk tsiya nima nace ɗana. A wannan lokacin ne Anty Aisha ta shigo, sallamarta ce tasa na ɗaga kai, taci kwalliya ta caɓa ado tana taunar cingom kamar wata ƴan mata, ni ban lura ba ma babu ita a wajen ba sam, yaran da suka shigo da kuloli ta kalla ta ce,"ku kai can ku ajiye". Sai ta ƙara cewa,"Iyam yamma tayi fa kar dare yay mana a hanya, kin san sun ce a yau za su wuce da lefen can Abuja wurin Kakarta. ga kulolin kayan garan can a mota, kajin kuma da aka soya gaba ɗaya kula uku ne na ɗebarwa wannan ƴar a ciki gashi nan a leda, dublan da alkakin ne dai ga kula guda nan an bar mata". Haka suka ɗunguma gaba ɗayansu su ka tafi, tsabar yawansu motocin gidan biyar aka ɗiba, bayan fitarsu na tashi na bar wajen ban ko bi ta kan kulolin da aka ce na ɗauka ba, ina jin Iyam na ƙananun maganganu akan na raina abun da aka bani, itama ban kulata ba nayi gaba abuna, kaza dai ba zan ɗauka ba don ba yunwarta na ke ba, dublan da alkaki duk ba na ci sune mayunwatansu. Da daddare ina kwance sai ga Nazifi ya shigo ɗakina da munafukan akwatinansa guda biyu wai na faɗar kishiya, baƙin ciki ya tokare ni, to ai ko lokacin da zai auren sanda baida uwar komai akwati biyu ya shaƙo min da kaya da ƙaramar jakar bakko ɗaya. don haka ko kallo bai isheni ba shi da kayansa na juya masa baya, ina jin yana faɗin wai ko na raina ne, ban ce masa kanzil ba nayi ma kamar bacci na ke yi, ya gaji da tsayuwarsa ganin banda niyyar kula shi ya ce,"Allah ya gani na fita hakkinki, ga su nan ki ɗauka ko kar ki ɗauka ruwanki. Kuma idan akwai abunda kike buƙata sai ki faɗa min". Ya faɗa yana juyawa ya fita ya bar min akwatunan, ai kamar an finciko ni haka na miƙe na duro a gadon, ƙafa nasa na dinƙa tura akwatunan har na kaisu bakin ƙofa kana na cilla su waje, kallona ya tsaya yi da mamaki da takaicin jefa masa kayansa a gaban ƙafafunsa, na kalle shi na banka masa harara tare da jan tsaki na danna ƙofata na rufe tare da sanya maƙulli, babu yanda bai da ni ba akan na buɗe ƙofar na ƙi, har da min barazanar zai kira Abbaa a waya yanzu ya faɗa masa rashin mutuncina gaba gaba ya ke yi, ni inda zai kira ɗin ma ai daɗi zan ji, don ko banza ƙila sanadin rabuwarmu kenan, don na lura ba zan tsani Nazifi ba in ba rabuwa muka yi ba. Wai duk yanda na kai da ƙoƙarin danne abinda ke tasowa daga can ƙuryar zuciyata amma hakan ya faskara, ban taɓa tsammanin cin fuska irin wadda Nazifi yay min yau ba, kawai na fashe da azababben kuka mai ƙaramin sauti saboda Rumana da ke ɗakin, babu abunda na ke buƙata a wannan lokacin irin na samu kafaɗan da zan kwanatar da kaina in zubar da hawaye har a lallasheni, sai dai bani da kowa cikin wannan gidan, Allah ne kawai gata na, yau in ace ka haifa ma ko a wannan kafaɗar ɗanka kayi kukanka duk da hawayen uwa rauni ne ga ƴaƴanta. na jima ina kuka sosai kafin na iya rarrashin kaina. Nayi kuka, kukan da ban taɓa irinsa ba tun bayan da abubuwan su ka canja a gidan nan, ban san a dalilin auren nan kuma ya rayuwata zata ci gaba da tafiya ba. bayan na idar da sallar isha'i na yi jugum ina ta faman tunani iri iri na game da rayuwar aurena, ya kuma zamu ƙare zama da wacca zata shigo? Itama irinsu ce? Me aka faɗa mata game da ni? Na san dai ba zata taɓa zama irina ba. Rumtse ido nayi ina ji anata knocking ƙofa na ƙi tashi na buɗe kuma da alama aiken zuwan gayyar tsiyar ne ban san ko uwar da zan yi musu ba, ba zai wuce zancen abinci ba tunda naji ba su jima da dawowa ba, ni kuma a yanzu dai in ba uwata da ubana ba wallahi babu wanda ya isa ya sakani shiga kitchen na dafa masa abinci, don ko me gidan yau sai dai yaci a inda yake zuwa zance, ko in ya rage na rana ya ci. Knocking ɗin ƙarshe ne ma Rumana tace,"Anty ni ce please ki buɗe min". Ba zan iya ƙin buɗe mata ba don Allah ya sani yarinyar ta shiga raina musamman da Allah yasa ta gane hanyar daidai, duk da ba wani yarda na gama yi da ita ba tunda jinin Yaya ne ke yawo a jikin
🏠