".
Iyam ta kyaÉe baki ta ce,"yau tana jin kanta da hayaÆi ina zata yi wani aiki, ai kawai ki kwaÉe ki shiga kiyi da kanki ko kuma ki tattara yara suyi, in ba haka ba kuma a san in da za'a kai a biya kuÉi su girka".
Yaya ta kama masifa tana faÉin mene amfanina a gidan da sai an fidda kuÉi an kai wani waje girki, tayi min tatas ta ce in shiga kitchen in Éora abinci mai sauÆi saboda masu zuwa Éaukar kayan lefe na kan hanya. kamar mara galihu haka na wuce ina jiyota tana faÉawa Iyam wai Malam ya ce shi ba da yawunsa ba cikin Æannensa mata wata taje kai lefe, shi ne Iyam Éin ke faÉin to kar ya barsu suje Éin itama ai tana da Æannen kuma ta isa da su kuma sun isa zamewa Nazifi wakilai.
Cous cous na Éora jallof saboda nayi saurin gamawa gudun tashin hankalin Yaya, ba Æaramin dauriya na ke ba wajen Éoye halin da na ke neman shiga na azababben kishi. kafin la'asar gida ya cika da mutane, baÆin fuskar ba wasu da yawa ba ne, yawanci Æ´an uwan Iyam ne sai Æannen Malam su biyu Mama Laraba da Anty Huduriyya, sai Æawayen Iyam da kafatanin Æ´aÆ´anta mata, sai Ummaa itama da nata mutanen, tawagar dai duk ta marasa kirki ce, shiyasa dama tunda na dawo naga wannan gayyar kaina ya Éaure na ke ta rayawa a raina ina cewa sai kace za'a yi biki, ashe ashe ile sace da ni shashasha ina ta harkokin gabana ban san miji zai danÆaro min kishiya ba. Abincin da na tafe kula da shi sai da suka cinye shi tass masu santi nayi masu kushewa nayi, ni dai ina kammala abubuwan da zan yi a Æasa na haye sama saboda na daina jin ma habaice habaicen da su ke ta aikin yi tun zamansu falo.
Tun da na shiga Éaki gaba Éaya na kasa sukuni, yayin da mamaki ya cika ni fal, na kuma kasa gasgata abin da ke faruwa a yau, kuka na ke rabza kamar an aiko min da mutuwar uwata, kukan da nake ba na komai ba ne face kukan abu mafi zafi a duniyata, kukan butulcewar Nazifi da gorinsa gami da Æarin aurensa ba tare da na sani ba. ban taÉa zaton akwai ranar da Nazifi zai iya Æaro aure ba, na dinÆa tuna irin yanda Nazifi ya ke matuÆar Æaunata ada tunanin da kullum sai nayi, da irin gwagwarmayar da muka sha tare wanda zan ce ma na fisa. Na girgiza kai cikin tsananin danasani da nadamar damar da nayi sakaci da, haÉi da gangancin Éora dukkan yardata akan Éa namiji, ni sai a yau ma da batun kishiya ya tashi komai na farkon haÉuwata da shi ke zuwar min daki daki, kuma sai a yau naji ashe duk wasu wulaÆancinsa na baya ba komai ba ne ga ainihin wulaÆanci nan, domin akan wannan ne ya iya buÉe baki ya gaggaya min maganganu ma su Æona zuciya har yana faÉin yana kunyar shigar da ni cikin jama'ar kunyarsa, banda wayewa! Ina zaune daÉas! satifiket Éin sakandire!, ba zai zauna da mara haihuwa ba! hmmm lallai Nazifi.
bayan kukana ya lafa na kwanta jiki a sanyaye, kaina jinsa na ke tamkar zai tsage, cikin tsananin damuwar da nake ciki naji ana ÆwanÆwasa Æofar Éakin, na miÆe cike da fargaba naje na buÉe, sai da na sauke wawiyar ajiyar zuciya ganin ba azababbiyar da nake tsammanin gani ba ce. murmushin yaÆe na saki ina cewa da Lubabatu,"to shigo ciki mana kin tsaya".
ta girgiza kai tana faÉin,"a'a Anty Sa'ida ba zan ja miki magana ba, Yaya ce ta aiko ni wai ki sakko yanzu ki ga lefen amarya za'a tafi kaiwa".
Nace,"ai ba sai na gani ba su kai kawai".
Ta kamo hannuna tana cewa,"kiyi haÆuri kawai ki je kar akan wasu banzan kayan lefe a ci miki mutunci a gaban mutane".
Kai na kaÉa na juya ciki na Éauko mayafina na yafa muka sauka tare, lokacin ana ta firfito da akwatunan daga Éakin Iyam, abin ya Éaure min kai, ban taÉa sanin da ana haÉa wani lefe a Éakinta ba, ko da yake sha'anin kuÉi Æila a rana Éaya aka haÉa su aka ajiye sai yau da za'a kai aka bani damar gani. Kujera Éaya mu ka zauna ni da Lubabatu har lokacin tana riÆe da hannuna tana tausata a hankali gudun kar su jita su babbakata da masifa. tana ta min Æ´an hira duk dan Æarfafa min gwiwar in daure in nuna musu abun da su ke ta rawar kai akai ba komai ba ne a wajena. haka aka jere shegun akwatuna guda goma sha shidda kowacce akwatu aka buÉe maÆil take da kaya na alfarma, bakin kowa ya buÉe sai maganganu ake da irin ÆoÆarin da yay wajen haÉa kayan, ita kuma Yaya na faÉa musu ai wadda za'a auro Éin ba Æ´ar Æananan mutane ba ce, mahaifinta me kuÉi ne kuma itama yarinyar tana aikinta a wata babbar ma'aikata, har tana faÉar sanadin haÉuwar tasu a jirgi ne lokacin da ya dawo daga Dubai.
Iyam ta ce,"wallahi ai sai yanzu ne Shalele zai yi aure, yarinyar Æ´ar boko ba cima zaune ba, gata lafiyayya don da suka je wannan gwaje gwajen da ake a asibiti an tabbatar da lafiya Æalau take, ga kyau kamar ka saceta ka gudu fara tasss da ita, Æ´ar manyan gida ce fa don Babanta ma ba Æasar nan yake zaune ba".
Furucin na ta yay matuÆar ba ni mamaki, wato duk wanda ya san a yand