NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 67 of 97

tsaya daga gefe, ta kalle ni da fuskar nan tata ta marasa mutuncin uwar miji ta ce,"hayaniya na jiyo tun daga ɗakina lafiya?". Ban yi magana ba nayi shiru saboda gaba ɗaya sun mayar da ni banza wadda bata san abin da take ba. cikin raina na ce,_"hmm ko ba komai ana barin halak don kunya dai, kuma insha Allahu da sannu za ku gane kurenku"._ Ɗan nata ya ce da ita,"ki zauna". Ta gama fahimtar abin da ke faruwa hakan yasa ta juyo gareni tana faɗin,"yauwa ki kwashe tarkacenki na ɗakin kusa da matakalar bene, saboda baƙi za su fara zuwa gobe za su sauka anan, taron biki za'a fara a gidan ban sani ba ko kin sani, na san dai duk kinga ai na kusa da abun". Ina jan yatsuna na ce,"na sani, amma Iyam ɗakunan gidan da yawa ai da sai a duba wani, wancan ɗin har yaushe na gama kwashe kayan cikinsa". Ta jijjiga kai ta ce,"zan sa a fito miki da su tsakar falo in ya so kya kwashe su anan. Ai dama na san ke dai sai kin yi baƙin ciki da auren nan, to ba'a aure ke aka auro ki?, ko ba'a zama da kishiya uwar ubanki ta zauna da ita?, Ni fa dalilin mugun halinki yasa na ce kar a bari ki sani don ban san irin malaman da za ki bi ba, to koma dai menene Sa'ida aure Nazifi zai ƙara ko za ki mutu sai dai ki mutu, akan me zai ta zama da juya irinki wacce ba'a san ranar haihuwarta ba?, kina zaune jaɓar sai cinye masa kuɗaɗe ki ke ba aikin fari balle na baƙi, kina ɗauko dangi da ɗai ɗai kina a taimaka musu da abinyi, to dukiyar ɗana ba zata lalace a taimakon ƴan uwanki ba kawai, na san wannan dalilin ne ma yasa kika sha abin da zai hanaki haihuwa, kai muguntar ɗan talaka ma bata yi ba wallahi". Tayi shiru tana jan tsaki, ta mayar da kallonta ga ɗanta ta ce,"kai kuma lusari ka bari mace zata ɗaga maka hankali akan zaka ƙara aure, ba ka gaya mata da izinin mahaifiyarka zaka ƙara, mata nawa Allah ya halasta ma ka zama da su?, in ba zata iya ba ta kama gabanta mana wani ya riƙe mata ƙafa ne ko akwai wanda ya rufe mata ƙofa. ina dalili a hanaka auren mace mai ilimin zamani da wayewa wacce take haihuwa ba juya ba...". Ba zan iya ci gaba da tsayuwa ina jin waɗannan bakaƙen kalaman ba, da sauri na fice a ɗakin cikin fashewar kuka, ina zuwa parlo na tarar da Yayan Shago tsaye, da alama ya shiga ɗakin Iyam ne ya tarar bata nan ya fito. Dauriyar tsayar da hawayena nayi ina gyara natsuwata na duƙa na gaida shi cikin girmamawa, ya amsa cikin tausayawa yanayin da ya ganni. Murya a sanyaye nace da shi,"ka zauna mana yanzu zata fito". Zama yay ni kuma na shiga kitchen na kawo masa ruwa da lemu. ko da na duƙa wajen ajiye tray ɗin hannuna kasa ɗagowa nayi kawai naji sabon kuka ya ƙwace min, bakina na rawa na furta,"Yayan Shago yanzu abin da aka min anyi min adalci kenan?". Shima cikin rashin jin daɗin faruwar lamarin ya ce,"ko kaɗan ba'ai miki adalci ba Sa'ida, ba ɓoye miki auren kaɗai ba hatta kishiyar kanta da za'a miki wallahi ba'a kyauta miki ba indai kan dalilin da suke faɗa ne, babu irin shawarar da ban bawa Nazifi ba akan auren nan yaƙi jina sam, ƙarshe ma kada baki yay ya faɗa min shawara kowacce iri ce in dai daga gareni ne ba ya so in riƙe girmana kawai. to kin san sha'anin mu maza in muna son abu idonmu rufewa yake musamman aka ce aure...amma kiyi haƙuri kinji dama ke ɗin me haƙuri ce, ki barshi yayo aurensa ke kuma ki riƙe adu'a ki kuma tsarkake zuciyarki a zamantakewarku, kar ki taɓa bari zugar shaiɗan ko ta ƙawaye su canja tunaninki, ki kama aurenki ki riƙe kar kishiya tayi silar rasa igiyoyin aurenki, idan da son samu ma Sa'ida ki ɗan nemi sana'a za ta ɗebi miki kewa". Ya ƙarasa maganar cikin alamar rarrashi, cikin ƴaƴan Iyam Yayan Shago da Lubabatu na daban ne, su na da kyawun zuciya, duk abubuwan da ke ta faruwa su kaɗai ne abun duniya bai sauya kyakykyawan ɗabi'arsu ba. Na sa hannu ina goge majinar hancina sannan na ce,"babu komai in sha Allahu zanyi haƙuri, zan jajirce kuma zan daure, na gode Yayan Shago". Na miƙe daidai da fitowar Iyam, ta taho tana faɗin,"wani abun ta kitsa maka kenan, to Rabilu me za ka iya yi?, kai kam ai sai dai kallo, batun aji maganarka ma ai bata taso ba". Maganganun da Iyam ke faɗa masa su ka taɓa zuciyata, tausayinsa ya kama ni, cikin yaranta maza shi ne babba amma saboda ba shi da kuɗi ya zama abin banza, babu ruwanta tai ta yaɓa masa magana, ta mayar da shi ƙarami a cikin ƙannensa, an mayarshi tamkar wani bare. Allah ya kyauta na faɗa a raina ina barin wajen. "Keeee!". muryar Yaya ta faɗi hakan wanda tsakiyar kaina ma sai da ya amsa, na rumtse ido ina juyowa in kalleta cikin tsananin jin haushinta, yanzu sam sunana ma ta daina kira sai dai kee. Shiru nayi ta wurga min harara tana cewa,"me za ki je sama kiyi a wannan lokacin?". kafin na bata amsa ta kalli Iyam ta ce,"wannan yarinyar bata san da zuwan baƙi ba ne?, Na duba kitchen na ga babu abincin da za'a ba su
🏠