ba ne ni wanda bai san ciwon kansa ba, ba zan mutu a haka ba bayan nayi aure tun da Æuruciyata, ina son ganin jinina Éa na cikina".
Ya Æarasa maganar yana jifana da wani irin kallo na wulaÆanci da nuna tsana. Sosai maganganunsa suka sosa zuciyata, ashe har akwai ranar da Nazifi zai wanke ni da irin munanan kalamai haka?, ashe har Nazifi zai iya ci min mutunci haka?, duk irin tarin sadaukarwar da na yi akansa a baya?, kuma har yana da bakin cewa banyi karatun arziÆi ba?, har yana da bakin ce mini ban da aiki sai in miÆa hannu a bani a bani?.
Tunanina ya katse dalilin jin maganarsa a tsakar kaina yana sake cewa,"shekaru da yawa ba ki tsinana min komai ba, sannan ki sawa ranki cewar da ke kaÉai zan zauna tsabagen son kai irin na ki, wacece ke da har za ki ce ba za'ai miki kishiya ba, marar haihuwa ko wacca mijinta ke kunyar shiga da ita manyan wurare?, to ki sani dole zan auro mace Æ´ar boko, wacce ta waye, wacce zata haifa min yara, wacce zata taimaka min ba wai ni in Æare a Éaukar nauyinta da na Æ´an uwanta ba...".
"Kai Nazifi!". Na katse shi ta hanyar kiran sunansa kai tsaye, abin da ban taÉa ba. idauwana suka firfito waje cikin Éaga murya na ce,"na gaji da cin fuska da rashin mutunci da gorin da ku ke min kai da Æ´an uwanka a cikin gidan nan, ba kuma zan ci gaba da Éauka ba, an kawo gejin da haÆurina ya Æare, nima zan fito in Éaga murya tamkar kowacce mace mai Æ´anci, dama na sani ba don komai aka Æulla munaÆisar wannan auren ba sai don a Æara samun hanyar cin zarafina, to kuwa kun yi kaÉan gaba Éayanku, kawai! akan ban haihu ba?, akan bani da aikin yi?, akan ka taimaki Æ´an uwana?...ehen haihuwa ni ce zan bawa kaina?, karatun kuma ta silar wa nayi asararsa?, to idan ka manta bari na tuna maka, ban da Æaddarar da ta haÉa aurena da kai sanin kanka ne da yanzu na zama abar kwatance fiye da kai Éin nan. kuma har kana faÉin ban da wayewa, kai Éin yaushe ka waye Nazifi?, sanin kanka ne ko a shiga aji na fika, kai ina naka satifiket Éin da ka ke da zarafin raina na wani?, har yaushe ka fara jin turancin?, Ohhh laifina shi ne kawo maka Æ´an uwana da nayi akan ka taimaka musu da jari?, Ko kuma fifita aurenka da nayi akan ilimin bokona?, karatun da iyayena suka ci burinsa akaina, amma nasa Æafa na shure duk don saboda kai da farin cikinka, har yanzu akwai ciwon rashin karatuna a zuciyar mahaifina, ka sani ba wai baka sani ba, taimakon mene ban maka ba a sanda Æ´an uwanka suka kasa taimaka maka, amma daga Æarshe in rasa sakamakon da zan samu daga wurinka sai na tozarci da gori? In kasa sanin za ka Æara aure tsabar bana da mutunci a idonka...to Nazifi ka Æara aura, ka kawo duk wacce za ka kawo, kuma ba zaka taÉa burgeni ba sai ka auro Éiyar mangofak, sai ka auro Éiyar masu kuÉin duk duniya, sai ka auro wacce zata cika maka gidan nan da Æ´aÆ´a, sai ka auro wacce ita take rabawa dukka ma'aikatan duniyar nan office tukunna in san da gaske kayi aure".
na Æyasta yatsuna na ce,"amma ka rubuta ka ce na faÉa maka wataran, wallahi da sannu za ka girbi abunda ka shuka, domin sai na kai Æararka wurin Allah".
Hankalinsa kwance, a nutse ya ke kallona yace,"kin gama haukar taki?". yay dakiyar faÉa don shi kansa ya san baida gaskiya ya kuma matuÆar mamakina ayau kamar yanda ni kaina nayi mamakin kaina. kuma saboda ya Æara ci min fuska ya ce,"Idan kin gama sai ki shirya gobe dangin matata za su zo suyi jeren kayan arziÆi, iyayenta su ne suka siya mata kayan Éaki ba da na mijinta zata yi amfani ba, kuma kar inji kar in gani, idan ba haka ba kuwa za ki sha mamakina...za ki iya fice min daga Éaki".
Na tsaya kallonsa babu ko Æifce, lallai masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce mutum mugun ice, mutum butulu, Namiji Æayar Ruwa, Namiji Æanin ajali, Namiji rigar Æaya. wato Nazifi ya manta duk wani faÉi tashi da nayi da wuya ba daÉi duk akansa kafin zuwan matsayin da yake kai yanzu, ina tare da shi tun baida ko sisi, na zauna da shi cikin tsananin talaucinsa ban guje shi ba, kullum cikin ÆoÆarin in faranta masa na ke in kwantar masa da hankalin damuwa da yake yi, amma shi ne yanzu saboda dukiya ta samu zai juya min baya, har da Æaro aure yana min gorin kayan Éaki da iyayen aba su siya min ba a sanda zamu dawo sabon gida, kai jama'a anya duniya da amana?, kai babu!, domin in akwai da ruwa bai dafa kifi ba.
Na danne zuciyata ina Éoye bala'in raunina da ke neman karkaryewa a gabansa, naja dogon tsaki na juya zan bar masa Éakin saboda zuciyata ingiza ni take yi akan in aikata ba daidai ba. Ina shirin fita mahaifiyarsa ta danno kai, na yi saurin komowa da baya domin bata hanya, haka ta tsira yanzu duk sanda ta so shigowa take kai tsaye babu neman izini balle shayin a yacca zata shigo ta tarar da mu.
Na sa kai zan fita tayi saurin dakatar da ni da cewa,"korar ki na yi?".
Nace,"a'a Iyam da ma zan fita Éin ne".
"To dawo".
Na dawo na