NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 65 of 97

ganin gabana sosai, cikin matsanancin tashin hankali da kaɗuwa na faɗa ɗakinsa. Zaune na same shi akan cushion ya miƙe ƙafafu kamar ba wanda na fita na bari ya fito a wanka ba, rediyo na kusa da shi yana sauraren tafsir a freedom radio, hannunsa kuma riƙe yake da littafin Muwaɗɗa yana karantawa. A hankali na ƙarasa gabansa na tsaya, kallonsa nake yi tun daga tsakiyan kai har tafin ƙafarsa, nafi ƙarfin minti biyu tsaye a gabansa amma tamkar bai san da shigowar tawa ba, ƙafafuna suka gaza ci gaba da ɗaukar tsayuwata, na duƙe a gabansa ina dire gwiwoyina a bisa carpet. Sai a sannan ya ɗago ido yay min kallo ɗaya ya ɗauke, can kuma sai ya ƙara dubana da kyau sannan ya buɗi baki yace,"lafiya?". kai na shiga girgiza masa na gaza furta komai. tsaki yaja na takaici yana sakko da ƙafafunsa ƙasa fuska a ɗaure ya ce,"sarai kin san bana son wannan halin ko, mene ya faru?". Hannuna da ke aikin karkarwa na ɗago na miƙa masa katin ɗaurin auren ina cewa,"tabbacin wannan na ke son sani Hubbi". Bai karɓa ba bacin ƙwayar idonsa da ya tsayar akan fuskata, kallona yake yi tamkar yau ne ya fara ganina a duniyarsa, kukan da nake ta dauriyar riƙewa ya ƙwace min ina haɗa hannayena wajen cewa,"Don Allah, don Allah don Annabi Hubbi ka ƙaryata abin da nake gani, don Allah kar ka bar kunnuwana su jiye abin da zuciyata ba zata iya ɗauka ba...". Katin ya karɓa a hannuna ya ajiye a gefensa, ya tari numfashina da faɗin,"raya sunnar ma'aikin shi ne zuciyarki ba zata iya ɗauka ba?, Jayayya za ki da lamarin da ubangiji ya rubuta?". Na zuƙi numfashi ina jujjuya kaina na ce,"ban isa ba, ban kai ba, baiwarsa ce ni ban isa nayi jayayya da lamarinsa ba, kawai ni dai ina so ka tabbatar min ne". "Rubutun da kika gani a jiki bai ishe ki shaida ba?". "Bai ishe ni ba Hubbi, sai naji daga bakinka tukunna, sai naji daga bakin da bai taɓa min ƙarya ba balle yaudara". Ɗakin ya ɗauki shiru, bakinsa ya furzar da iska, sautin muryarsa ya fito a hankali da cewa,"ƙwarai aure zan yi, zan kawo miki abokiyar zama, na kuma zaɓi ɓoye miki ne saboda tsarina ne hakan, dama na faɗa miki ai zan tabbatar da na ba ki mamaki". Furucin nasa yasa na zabura na miƙe da sauri wanda har ban san yanda aka yi na tsinci hannuna a ƙirjinsa ba. Ƙirjina ya shiga dukan tara tara ina jin zuciyata tamkar ana soyata da dalma, cikin raina ina nanata kalmar AURE da ABOKIYAR ZAMA. Muryata ta fito cikin sanyi da rauni ina cewa,"da gaske aure za ka ƙara?, Hubbi aure ba tare da na sani ba?, ace ban da masaniyar mijina zai aure sai da ya rage saura kwana biyu?, yanzun ma da ban gani ba shikenan sai dai inga ana shigo da amarya?, dama ana haka da gaske?, Hubbi komai nayi maka ban cancanci hukunci ta irin wannan sigar ba, ko ɗaya ban cancanta ba, me yasa zaka ƙara aure?, biyayyar me na gaza yi maka? duk irin haƙurin da na ke, duk irin kauda kan da na ke yi". Na ƙarasa maganar ina girgiza kaina cikin matsanancin ƙunar rai tare da binsa da kallon mamaki matuƙa. Na ƙara faɗin,"Don Allah in wani laifi nayi maka ka faɗa min wallahi na ɗauka alƙawarin zan gyara amma kar ka hukunta ni ta hanyar yi min kishiya". Maganar tawa ta katse, na duƙar da kaina ƙasa tare da damƙar gaban rigarsa da kyau. "Kayi haƙuri Hubbi, ka yafe min laifin da na aikata maka bisa rashin sani, in ka ƙara aure ka zalunce ni, haƙiƙa ka zalunce ni...". Ya katse ni a tsawa ce,"Dakata!, ƙarin aure ba yana nufin lallai sai kin min laifi tukunna zan yi ba, ra'ayina ne in zauna da adadin matan da na ke so, ba'a ce lallai da ke kaɗai zan zauna ba, don haka ka da ki nemi ki haramta abin da Allah ya halasta min...kuma da kike maganar na zalunce ki ta ina na zalunce ki ɗin?, ke idan ma ba ki gode min kin ce nayi adalci ba ai kin zama butulu, duk irin haƙurin da nayi na zama da ke a haka tsawon shekaru masu yawa?, amma ba ki ko ji kunyar kallona kina tambayar akan me yasa zan ƙara aure ba, to dama ta ya kike tunanin zanci gaba da zama da ke ke ɗaya alhalin ina so naga jinina, ke in da na san ma ba kya haihuwa zan aureki ne?, kin zo kawai kin zauna daɓas ban da ci da kasayarwa babu abin da kika sani, komai sai dai ayi miki, sai aukin a baki a baki ko kunya ba kya ji, wallahi tallahi Sa'ida ban da wata darajar ko kaɗan zama da ke ya sire min, shekaru da yawa kin kasa wayewa, kin kasa zama ƴar gari ki koyi soyayyar zamani, cikin kanki empty babu turanci, duk da dama ba wani karatun arziƙi kika yi ba...ga matan abokaina nan duk ƴan boko ko ina shiga su ke da su, amma ni har kunya na ke yi idan na tuna tawa matar satifiket ɗin sakandire ne da ita, ɗan aikin zamanin nan na zaman office babu sai shiga kitchen ɗin banza da wofi, ciki ya iya ɗaukar abinci amma ya kasa ɗaukar ɗa balle har a haife, to ni ba zan iya ci gaba da zama da wadda bata haihuwa ba, ba ɗan iska
🏠