NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 64 of 97

re min kafin daga bisani kowacce ta ɗauke ido tana faman yatsine fuska kamar sunga kashi. maganar da na riskesu suna yi naji sun koma yi ƙasaƙasa, dama can banji me suke cewa ba balle na buƙaci jin sauran zantukan. to kan me ma suke tsammanin zan damu ba yan ba dani ake maganar ba? Ni ɗin kuma ba munafuka ba?. Sai da zan fita a ɗakin kuma naga Ummaa ta fito daga banɗaki, da murmushina na tsuguna ina gaida ita amma itama sai naga tayi min yanda su Yaya suka min, wato dai amsawa a daƙile ba don ta so ba. kawai sai naji kaina ya ɗaure, na farko zuwansu gidan kaf ɗinsu kamar za'ai wani taro? na biyu Ummaa ba haka ta saba min ba dan ko satin da ya wuce naje gidan kuma fuskarta sake ba alamun kwai matsala tsakanina da ita. fita nayi daga ɗakin cikin sanyin gwiwa, karo muka yi da su Fati ita da matar ƙanin Hubbi Sulaiman, yanda su ka kalleni su ka watsar haka nima na kallesu na watsar, dama ita Zalihan cikin facalolina da ita ne bama wani ɗasawa tun can da. Da sauri nayi gaba dan jikina bani ya ke wannan taron na su kaman da wata a ƙasa, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, kaman sun yo zuga ne don cin mutuncina yacca aka saba. ina shiga ɗaki kawai nayi wankana na shirya na fita, kasa sauka nayi don sam bana so na sauka mu kuma haɗuwa da wani cikinsu, ga dole ma sai na sauka naje na sameshi tunda na ga motarsa tabbacin ya dawo kenan, Allah yasa sun yi girki sun ba shi su hutar da ni. ni dai addu'ata Allah yasa zuwan na su ba shi da alaƙa da ni dan gaskiya tuni na gama gajiya da wannan tashe tashen hankulan da komai yaƙi ci yaƙi cinyewa, kwanciyar hankali na ke buƙata a yanzu kam. kawai dai na sa a raina yau duk wacca tayi min a cikinsu tabbas zan rama ba zan ƙyale ba ko a gaban uwarta ko a gaban ƙanin na su. ko da na shiga ɗakinsa yana banɗaki, na zauna jiransa sai ga yara sun shigo suna faɗin za su tafi islamiya. jiran fitowarsa su ka yi saboda kuɗin littafan da za su karɓa. bayan ya fito ya ce na ɗauka rigarsa na ɗau kuɗin na ba su, sai dai ko da na duba babu hakan yasa shi cewa na ɗauka maƙullin motarsa,"cikin wajen da na ke zuba takardu akwai kuɗi ki ba su". na ce,"nawa?" su ka ce,"kowa dubu biyu aka ce Abba". Na miƙe muka fita tare da su, bayan na basu kuɗin na raka su bakin gate su ka wuce kana na dawo motar don ɗauko hulunansa da ya ce za'a kai wanki. dama a kujerar baya ya ke ajiye su, na tattaro su gaba ɗaya don kusan ya saka su dukka. sai dai ina shirin fitowa daga motar wani abu ya ɗauki hankalina da yasa ni ware idona akai gaba ɗaya. lokaci guda idanuwana su ka disashe, ganina ya fara ƙoƙarin ɗaukewa, haka na daina jin sautin komai a kunnuwana, lokaci guda ƙwaƙwalwata ta tsaya cak da aiki, ganin ina neman gaza shaƙar iska da fitar numfashi nayi saurin fito da kaina daga cikin motar. Sai dai ba ni da wani iko da motsa jikina domin kuwa jini ya tsaya da gudanar da aikinsa balle na sami damar ɗaga ƙafa na bar wurin saboda tsantsar tashin hankalin da na shiga. Yanda jikina ke karkarwa daidai yake da kaɗawar guguwa a tsakiyar rana, haka yanda na ke jin dummm a cikin ƙoƙon kaina tamkar saukar tsawa a tsakiyar duhun dare ne, allon ƙirjina kuwa girgiza ya ke yana neman barin ƙirjina ya tarwatse a ƙasa wanwar, ban san ta ya ba, ban san ya za'ai ba, amma tabbas bana tunanin zan iya gasgata abin da ƙwaƙwalwata ta karanta a jikin katin ɗaurin auren hannuna, balle kuma har zuciya da gangar jiki su iya ɗaukan lamarin. Idanuwana na rumtse gam na ƴan sakanni kafin na shiga buɗe su a hankali, har yanzun dai a disashe su ke bana gani sosai, don haka kawai sai na ke kallon invitation card ɗin ina ƙara kallonsa, na kasa sakinsa ya kuma ƙi faɗuwa daga hannuna duk da irin karkarwar da hannayen nawa ke yi. ta cikin ruwan hawayen da su ka ɗan taru a idona na ke ƙara bin rubutun jiki da kallo, so na ke na aro hankali a wani wajen tukunna in ƙara karanta abin da ke jiki, bana tsammani a yanzu akwai hankali a tattare da ni kam, don in akwai ba zan karantowa kaina wannan baƙar musibar ba, Aure fa, Aure guda ba abin wasa ba, auren da ban san da batunsa ba, inaa da sake, ko da mijina zai ƙara aure to ba ta wannan hanyar wulaƙantawar ba, rashin darajtawa har ina haka?. _hasbunallahu wani'imal wakil._, zuciyata ta ambata, tabbas babu ƙarya a rubutun da na gani, Aure Hubbi zai ƙara, saura kwana biyu ɗaurin aurensa, amma ban sani ba, wadda na ke da hakki akan sanin hakan. wani wahaltaccen yawu ya wuce ta maƙoshina da ƙyar, ya sauka a cikina da babu komai face baƙar yunwar da ke ƙwaƙulata tun ranar jiya, kayan cikin nawa suka amsa, na rumtse ido saboda raɗaɗin wahala. wucewar sakan ɗaya, biyu, ubangiji ya bani aron ƙwari na samu damar ɗaga ƙafata na bar bakin motar ba tare da ko na maida murfin na rufe ba, haka na bar compound na tafi bana iya
🏠