ayawa na yi ina kallonsa, tabbacin aiwatar da abunda zai aikata kwance saman fuskarsa, ban san me ya ke nufi ba haka ban san mai zai aikata Éin ba amma Æwarai na tsorata, bana son abunda zai Æara kaimu ga gaban iyayena, bana so sam, shiyasa ko hanyar da na Éauka ta fita a sabgarsa shi da Æ´annuwansa na ke bi a hankali ta yanda dole sai dai su buga su barni.
fita nayi naje na Æarasa gugar kayan Fati, sai da bayana ya zama kaman ya Éalle kafin na gama don kayan ba kaÉan ba ne, na kai kayan Éakinta na jera mata cikin wadrobe, sannu wannan bata ce min ba, nima ban damu ba na fito fatana ta barni haka kuma inje in samu na huta. tunda na koma Éaki na kwanta na rasa natsuwata sai faman juyi na ke yi, tunaninsa duk ya addabe ni, ban san wanne hali yake ciki ba, dole haka na tashi nayi shirin kwanciya na fita, sai da na shiga Éakin su Rumana na tofe su da adu'ar bacci kafin nan na sauka zuwa Éakinsa.
a hankali na murÉa Æofar Éakin na shiga, har ya kwanta yana fuskantar saman dakin, na tura kofar na rufe, ashema waya ya ke yi ni ban sani ba sai da na zo bakin gadon, amma a haka yayi kaman bai san da shigowata ba. "ina zuwa". shi ne abunda najinya faÉa kafin ya dire wayar yana kallon Éarin da na ke, cikin sanyin jiki na zago ta gabansa a hankali na shiga basa haÆuri, tun kafin na Æarasa ya katse ni yana sakkowa daga kan gadon.
"Ai na gama yanke hukunci akan wannan, ki ci gaba da duk abunda kika ga dama wanda ki ke ganin daidai ne a wurinki ba zan hanaki ba, ba zan takuraki ba, nima zan yi abunda na ke ganin daidai ne a wurina, sai dai kar ki ji haushina, yanda ba kya buÆatata nima bana buÆatarki a yanzu tashi ki fice min daga Éaki kafin ki hasali ni".
Tunda ya fara maganar na daskare ina kallonsa har ya kai Æarshe, ban taÉa ganin ainihin Éacin ransa ba sai yau. tsawa ya kuma doka min yana cewa,"ba za ki tashi ki fitar min a Éaki ba sai na zo ina aikata miki abunda za ki zo kina danasanin sanina, wadda bata san darajar aure ba balle sanin darajar girmama miji. to kije tsinuwar mala'ikun Allah ma kaÉai ta isheki".
Turo Æofar Éakin yasa mu kallon Æofar duka. Iyam ce ta shigo tana faÉin,"lafiya Nazifi? muryarka duk ta karaÉe gidan nan, da alama Éata maka rai aka yi".
Gefe ya juya yana cewa,"Don Allah Iyam ki ce da ita ta bar Éakin nan".
Ta dube ni tana cewa,"yau naga jaraba ni Jummai, to ana dole haka dama? ki bar masa Éaki mana tunda ya ce ki fita, kinga tashi don Allah yi waje tunda dai kina da Éakin kwanan ni bana son abunda zai Éaga hankalin Éana nima nawa hankalin ya Éaga, dare mahutar bawa amma ke sai lokacin za ki tashi neman bala'i".
kasa tashi na yi hakan yasa ta Éaga murya da cewa,"natacciya ba za ki ta shi ba ne wai". so na ke na tashi Éin amma ina jin kunyar miÆewa a gabanta da rigar da ke jikina. rigar gaba Éaya iyaka gwiwa ce haka kuma shara shara ce ana ganin komai na jikina. nayi Æasa da kaina hawaye na zuba a idanuna, saukar abu naji akaina hakan yasa na Éago, shi ne ya jefo min babbar rigarsa, daga tsugunen na Éaura kana na miÆe na fita da sauri. ina shiga Éaki na faÉa kan gado ina kuka me shiga jiki, wani irin kuka da ke fitowa daga can ÆarÆashin zuciya tare da bayyanar da labarin da ke cikinta, ban taÉa tunanin matakin share Nazifi zai janyo min matsala haka ba, da na san hakan zata faru tabbas da ban aikata ba na bari mun ci gaba da tafiya a yanda mu ke, ga yanzu har yana tunasar da ni tsinuwar mala'ikun Allah, rumtse ido nayi ina faÉin Allah ka yafe min Allah ka yafe min.
Bayan sati biyu na dawo daga unguwa, da yake azumi ya gabato na ce bari na jajje wuraren da zuwa ya kamani banje ba, in aka fara azumi fitar na zama da wahala. to sai ma kuma ya bani kayan sadaÆa da ya fitar na azumi ya ce in kakkai wurin da naga ya dace.
a matuÆar gajiye na dawo duk da ba wani jimawa nayi ba na dai fita da sassafe ne saboda gidan rasuwa muka fara zuwa ni da Ummani, tun daga compound na bawa Rumana jakata hijabin ma na cire shi da zummar ina shigowa falo zan rashe akan kujera, ni yanzu kam kullum cikin ciwon jiki na ke saboda bautuwar aikin da na ke sha, me shara da wanke wanken ma Iyam tasa tayi gaba, Fati kuwa ko tsinke bata taya ni Éaukewa, za dai a Éata da ita amma gyara ba nata ba ne, ko Éakin Iyam Éin da su ke kwana tare bata san ta gyara ba dole ni ke shiga in gyara musu.
Da shigowata nayi turus jiyo muryar su Yaya a Éakin Iyam, ga Æanan yaransu a falo suna ta dabdalarsu duk sun yi kaca kaca da wurin. Éakin Iyam Éin na shiga don shaida mata na dawo, ina shiga naga kusan duka Æ´aÆ´an mata masu auren ne ma su ka zo, ban san dalili ba naji gabana ya faÉi, tsoron da ya dirar min lokaci Éaya na kawar na Æarasa shiga Éakin, na gaida Iyam Éin na ce mata na dawo ta ce to har da min sannu da zuwa, su kuwa Æ´aÆ´an nata banda Lubabatu babu wanda ya amsa mini sai kallo da su ka Æa