NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 62 of 97

da lamarin plazar da ya faɗa min, tabbas aka rusheta ba ƙaramin asara zai yi ba, don duk ita ce jagaban kasuwancinsa. nayi nisa a wankin sai ga Fati da kaya a hannu, tana zuwa tsabar rashin mutunci ta watso min su cikin ruwan wankin, raina ya ƙuntata na waiga a fusace sai zuciyata ta taushe ni kawai na ƙyaleta, don yanzu ina magana tashin hankali zai biyo baya. "ki wanke min fuskar da hannayen da kyau". ta ce da ni cikin gadara da nuna rashin kunya, ban ce mata komai ba har ta fita. kafin na gama wankin har na gama girki dama saboda haka nayi dabarar haɗa aikin biyu, kar in kai dare ban gama girki ba Iyam ta ɗaga min hankali da cewar na bar yara da yunwa, tayi nata mai gidanma yay nasa. Nayi sa'a kayan su ka bushe da wuri. na ɗebo shanyar na linke na ajiye su akan kujerar falo, ina jiran nayi wanka na ɗan huta sai na zo na goge, kafin na bar wajen sai ga Iyam ta fito ta zo tana cewa,"gugar kuma fa bayan ga wuta nan kika wani linkafesu kika yasar da su anan koma ki kai min ɗaki. Ko ajiye min kika yi na zo na goge da kaina?". "A'a Iyam dama ina so ne zuwa ɗan ajima sai na goge". "mene wani anjima saboda dai ki bar min kaya da ƙura, dama ai ba so kike ba kika wanke, saboda Fati ta kai miki hijabi biyu shine har da yi mata tsaki ke da ba kya ƙaunar zaman lafiya, ai ba ita ta saka ki wankin ba ni ce nan, me kike yi a gidan Sa'ida in ba a saka ki aiki ba nufinki sai dai kici ki kasayar ki kwanta? kuma yarinyar nan kina gani daga makaranta ta dawo tana so ta huta ta ina zata yi wanki, anfanin duk wata hidimar gida na matar gida ne. don haka Malama zauna ki goge su kar nefar su ɗauke wutarsu, gugar solar nan ba wani kyau take ba, ko kuwa haka kike so na dinƙa saka kaya a yamutse ana zagar min ɗa, gwara ma ni akan yaran". Tunda na zauna gugar ban tashi ba sai da aka yi kiran magriba, na ɗebi waɗanda na goge na kai ɗakinta na ce mata zan yi sallah tukunna sai in ci gaba. ba dai ta ce min ƙala ba na fito na wuce ɗakina, sai alokacin nayi wanka na shirya cikin doguwar rigar atamfa. jikina banda ciwo babu abunda yake yi min, na kwanta ina ta aikin nishi, na manta rabon da na ce na huta na minti biyar tunda Iyam ta zo. Rumana ta shigo ɗakin zatonta bacci na ke yi don sai da ta zo daidai kaina kana ta shiga taɓani a hankali tana cewa,"Anty Abbaa yana kira". Na kalleta da gajiyayyun idona, zama tayi kusa da ni tare da taɓa wuyana tana cewa,"Anty ba ki da lafiya?". na murmusa kuncina na ce,"lafiyata lau Rumana, gajiya ce kawai". kanta ta kwanto bisa kafaɗata tare da riƙe hannuna. "Anty don Allah kiyi haƙuri da duk abunda muka yi miki, ni dai wallahi na daina, yanzu tausayinki na ke ji kuma ina sonki". Na shafa kanta ina cewa,"Anty ba ta fushi da yaranta, nima ina sonki Allah yay miki albarka". tashi nayi na kama hannunta muka fita, tana min surutun in ce Abbansu ya kaini asibiti idona baya da lafiya kuma duk na rame, hmm ni yanzu na masa magana ma ai ce zai yi je ki chemist. Ɗakinsa na iske shi, ni sai da ya kira ni ma na tuna da saƙon da ya bari. wani kallo ya watsa min yana cewa,"ke ba kya taɓa son a zauna lafiya, ya za'ai na bada saƙo tun ɗazu sai yanzu muyi waya da mata tace min ba a kai mata ba". "kayi haƙuri ba wai haka kawai ba ne. kaima ce kayi idan na gama aiki kuma har yanzun da kake faɗan ba gamawa nayi ba". "Sa'ida wai mene matsalarki? Me ya ke damunki ne da kika bar ɗaukar maganata da muhimmanci? na fa gaji da wannan banzan halin na ki da kika tsira". "Na ce kayi haƙuri ko, gugar Iyam zan ƙarasa babu yawa ina kammalawa sai in je, ba zai yiwu na aje nata aikin akan naka ba". bai ce min komai ba ya sadda kai ƙasa yana duba wasu takardu da ke gabansa, soyayyarsa na ji ta cika min rai, bana so yay zaton ko daina sonsa nayi, ƙaunarsa na nan yanda take a raina, duk irin baƙin ciki da ɓacin ran da ya ƙunsa min tuni na cire a raina na yafe masa, duk da shekaranjiya naji zafin zagin da yay min a gaban ƴan uwansa akan sun zo ban san da zuwansu ba ni kuma na kulle store, da kuma abunda yay min akan Fatin ɗazu. shi dai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu ba ya min ko da kwatan son da yayi min a ba ya, rabonsa da faɗa min wani kalaman soyayya tun ranar da buƙatar kansa ta kawo shi kafin ya kai ƙarata gidanmu. ni kam nayi alkawari nayi sai na rama ko da kaso ɗaya ne cikin kason ɓacin ran da ya saka ni ciki, kuma na lura ta banzatar da shi da lamarinsa kawai zan rama don hakan na masa ciwo ko bai faɗa ba. "kayi haƙuri kaji Hubbi". na faɗa ina tsugunawa a gabansa ganin yanda fuskarsa ta nuna tsantsar ɓacin rai. bai kalle ni ba ya ce,"no kar ki damu zan yi maganin abun, idan kina ganin hanyar da kika ɗauka ita ce daidai a gareki nima zan san abun yi, kije kici gaba da ɗaukar zugar duk me zuga ki, kiyi yacca kike so Sa'ida amma zan tabbatar da na matuƙar ba ki mamaki wallahi". ya faɗa yana jijjiga kai. ts
🏠