aurin barin wajen ina nufar dining, abincin na zuba mata na ce da ita ga shi nan, kamar bata jini ba haka tayi banza da ni.
ina niyyar barin wajen sai ga shi ya fito daga Éaki, Iyam na ce masa,"a'a da ce tayi ba zata bawa Fati abinci ba na ce to bara na kiraka Æila taji maganarka tunda ni ban isa ba".
kallona yayi yana cewa,"bisa wanne dalili za ki hanata abinci? wai ke ki hora mutum da yunwa daÉi ya ke miki ne? wato abunda na ÉanÉana miki kwanaki bai ishe ki ba?".
Iyam ta katse shi,"kaga duk ba wannan ba, Fati dai gata can zaune ma kallonta take, kallon dole don dawowarta kenan yunwa take ji, ka ce kawai ta bata abinci".
"ki bata abincinta karnki Æara hana wani nawa abinci tunda ba ke kike siyowa ba, don kin dafa ba yana nufin kina da iko da shi ba ne".
muryana na shaida damuwa na ce,"ban fa ce ba zan bata ba, ce nayi taje ta Éiba. kuma ga shi na zuba mata na ce ta zo ta Éauka tayi min shiru".
"ohh in magana ki Æaryata". cewar Iyam
"ni ba Æaryata ki nayi ba amma yanda kika ce ai ba haka ba ne...".
maganata ce ta katse dalilin saukar marin da naji a fuskata.
"duk ranar da mahaifiyata ta Æara magana kika nemi ki ja akai sai na mugun saÉa miki, uwata fa tana faÉa kina cewa ba haka ba, me kike nufi in ba Æaryatata ba".
idona ya ciko da hawaye ina dafe da kuncina. na jiyo shi yana cewa da Fati. "ke kuma zo ki Éauki abincin".
ta marairaice tana cewa,"Yaya Æarami Æafata ce naji ciwo bana iya takawa inama shirin ce maka zanje asibiti ne".
ya waigo ya kalle ni daidai lokacin da na ke niyyar barin wajen murya a sama ya ce,"na gama magana ne da za ki bar wajen?".
na dakata ba tare da na juyo ba.
"ki Éauki abincinta ki kai mata kina ganin ai tana da lalura".
na danne kukana na mayar da hawayena, na Éauki abincin na je na miÆa mata ta karÉa tana Æunshe dariya, cikin raina na ce Allah ya saka min.
Barinsa wajen na nufi bene nima, gaba Éaya na manta da batun wani wanki, sai munafukar yarinyar ce take cewa da Iyam wai na tafi na bar mata kaya. ita kuma ta ce ta Æyaleta da ni zamu zuba. ni kam ban tsaya ba nayi Éaki ina jin babu daÉi a raina, zama nayi saboda raina ya Éan yi sanyi amma har ga Allah na jima ban ji Éacin rai ba irin na yau.
to ni wankinma bai cin min rai ba kamar zuba abincin in kai mata kuma ta karÉa tana min dariya, in wanki ne dama tunda Iyam ta dawo ta hana badawa da guga tace masa gatan yayi min yawa komai sai a kashe kuÉi ayi min banda aiki sai kwanciya, don haka bisa umarninta kar a Æara bayar da wanki a gidan, kayan wankin guda nawa su ke da ni ba zan wanke ba sai dai ai ta Éarnar da kuÉi ni babu tausayi saboda ban san wahalar da yake sha ba kafin ya samesu, to in dinga Æwarara jiki ina motsawa, haka ma fa firij tasa an Éauke na kitchen an kai Éakinta, duk su lemo da nama in ya kawo sai yanda ta bani, duk sona da maltina yanzu sai haÆura na ke yi saboda idan naje karÉa ta dinga mita kenan.
Da rana ina cikin wankin sai ga shi ya shigo yana faÉin,"wanne irin rashin hankali ne wannan? Kin bar tukunya zata Æone kin taho wani aikin na daban, ki bari ki fara kammalawa da Éaya mana, wannan ai ba dabara ba ce. kin san yanda gas ke kara tsada kuwa, wallahi za ki ja na koma ajiye miki buhun gawayi".
Da alama bai san wankin na waye ba shiyasa, Na tsame hannuna a ruwan da sauri, ta gefensa na wuce na nufi kitchen Éin, ina zuwa na tadda ruwan zafin ko tafasa bai yi ba, ni dai dama nayi mamaki domin kuwa nayi Æasa da wutar sosai, kai bawa dai da komai kayi sai ya zama laifi, nufinsa da yay maganar in tsaya masa bayani ya hasala ya gaggaya min babu daÉi. ina kitchen Éin ya dawo ya sameni, ya ce in fito falo na iske shi, sauri sauri na wanke shinkafar na zuba na fita, yana tsaye hannayensa harÉe ta baya, hannun kujera na zauna ina ce masa,"gani".
kuÉi ya miÆo min tare da cewa,"akwai abunda ya taso min na ke so a taya ni da adu'a, ga wannan dubu talatin ne, idan kin gama aikin sai ki leÆa gidan Malama Hadiza, akwai buhun shinkafa da wake na bayar akai gidan, idan kin je sai ki tambayeta adadin kuÉin da ake buÆata, jallof ne za'ai da Æosai da kunu ayi sadaÆa".
ina kallonsa na kai hannu na karÉa na ce,"Allah ya karÉa ya biya buÆata".
Ko amsa ni bai yi ba, ya nemi kujera ya zauna ni dai na bi sa da kallo don naga kamar yana cikin damuwa. sannu a hankali na ce da shi,"ko wani abu ne ke faruwa?". ba tare da ya kalle ni ba ya ce,"plazar cikin gari gwamnati ke son rushewa wai filinta ne".
na ce,"to subhanallahi, Allah ya saita al'amura, kar ka damu insha Allahu zata dubeku ta bar muku abinku, adu'a ce kawai zata yi aiki".
ya amsa da,"ilahee ajib".
na buÉi baki da niyyar in wata maganar wayarsa tayi Æara, ido ya Éago yana kallona bayan ya gama kallon screen Éin wayar, a hankali yace,"ki bani wuri".
tashi nayi na bar masa wajen na koma bakin ayyukana, sai dai tuni na shiga damuwa