nzu ko sai anjima zaka ci?".
bai ce da ni komai ba, na kuwa miÆe na shiga gyara abunda zan gyara a Éakin ban Æara kula shi ba har ya gaji da tsayuwar da yake ya zo ya zauna gefen gado.
sai da na kammala kana na ce masa,"zan wuce gidan kitson".
agogo ya kalla kana ya ce,"ok to nawa zai ishe ki?".
wani kallo nayi masa sannan na ce,"abun da ya samu".
yasa hannu a aljihu ya Éauko kuÉi, dubu biyu ya zaro ya bani yana ce min wai babu cash a wajensa, kuma na san akwai kawai yanzu ba ya son bani kuÉinsa, tunda Iyam ta Æyalla ido akan yana ban na cefane bayan yana ajiye komai sai ta fara Æorafi akan hakan, tun daga haka kam na ce in anyi duniya don manzon Allah ban Æara tambayarsa kuÉi, in ya bani falillahil hamd in bai bani ba Ummani na tura min kuÉi yanzu.
na fita na bar Éakin bayan na ce masa na tafi. Allah ya gani ba Æaramin juriya da Æarfin hali na ke yi ba akan sharesa, yanda ya ke nuna kaman ya damu haka ni to nayi muguwar damuwa, faÉin na daina sonsa sai na tuna shiga tsakanina da Abbaa ne duk da yanzu Abbaan ya Éan sakko yana kirana ma wani lokacin da kansa, amma Allah ya sani ina mutuwar son mijina, kawai na fita a sabgarsa ne saboda zaman lafiya da kwanciyar hankalina. sau da dama ina jin na karaya idan ina kusa da shi amma na kan danne na tursasawa zuciyata, in kuwa na kasance ni Éaya babu tunanin abunda na ke sai rayuwarmu ta baya tun daga haÉuwarmu zuwa auranmu da muka rayuwa cikin farin ciki da Æaunar juna kafin shaÉan ya shigo tsakani.
shirina na yi cikin sabon hijab Éin da Alhaji Yayan su Ummani ya aiko min wancan sati, da maÆulli na kulle Éakina don yanzu ba na iya idan zan fita na barsa a buÉe, duk da ba raya wani mugun abun zai iya faruwa ba amma idan ka kiyaye sai Allah ya kiyayeka, masu zuwa gidan ba Æaunata su ke yi ba, to ban san iyaka inda manufarsu ta tsaya ba don satin baya da Anty Aisha ta zo ce tayi sai taga bayana a gidan nan.
na sakko ina ÆoÆarin Éaura niÆab Faty ta shigo da sallama da yanayin gajiya sosai a tare da ita. ita ce autar Iyam a mata, kuma duk Æ´aÆ´an gidan ita da Salaha ne kaÉai Allah ya ci da su rabon karatun boko me zurfi, yanzu tana polytechnic ta nan Éorayi, satin Iyam uku da zuwa ta dawo itama wai makarantarta tafi mata sauri daga nan, ni dai adu'ana Allah yasa kar zaman nata yay tazarce dan ba mutunci ta cika ba dama ita tun asalinta haka take, ita da Anty Aisha halinsu Éaya.
fuskata ta washe da fara na ce mata,"sannu da dawowa Æ´an makaranta".
"Yauwa". ta amsa min a ciki tana shigewa Éakin mahaifiyarta.
shigarta kenan sai ga Iyam ta fito. ganinta yasa na tsaya tambayar,"wani abun za'ai maki Iyam?".
ta ce,"ehhh fa". ta faÉa tana yi min duban sama da Æasa. "Ce zan yi dama ki haÆura da fitar kawai, kayan wanki ne na Éebo su, nawa ne da na Faty, kuma yaran naji suna faÉar kayan makarantarsu na gobe ba'a wanke ba, kinga fita kuwa bata kama ki ba, ki bari zuwa goben sai ki je duk inda za ki tunda ba tashin duniyar za'ai ba".
shiru nayi hakan yasa ta Éaga murya da cewa,"ko kuwa ba za ki ba Sa'ida na ga kin Éata rai, ina uwar mijinki ban isa na sa ki aiki ba kenan?".
ido na rufe na sauke ajiyar zuciya, murya Æasa na ce,"ya za'ai na ce ba zan yi abunda kika saka ni ba, don Allah ki bar faÉin haka".
"na ji bana son kissa, yauwa ki wanke yanzu kar ki ce sai anjima yamma tayi su Æi bushewa har dare su zo suna warin rima".
sai ta shiga Æwala kiran "Faty! Faty! fito min da kayan nan da na Éaure, ki tabbatar kin sako duk kayanki na dattinkar daga baya ki zo kina min mitar kin rasa kayan sawa in za ki wuce makaranta".
Fatin ta fito da damin Æunshin kaya na cullo su gabana tana faman hararata, kallon kayan na yi kawai na san da gayya aka Éebo su, kuma rabi na san na Fati ne tunda ko cikakken sati banyi ba da yiwa Iyam wanki. abun yana ci min rai yana Æonan zuciya duk sanda Iyam ta bani wankin kayan Fati, Æanwar miji fa? ba ma dole yarinyar ta dinga gani na a wulaÆance ba.
maganar Fatin ta katse tunanina tana cewa,"ba ki ba ni abinci ba kuma".
ban ko kalleta ba na duÆa zan Éau kayan Iyam ta ce,"jin abunda ta faÉa ne ba ki yi ba ko kuwa abincin ne ba ki da niyyar bata isashshiya. ko kin mata gidan Yayanta ne uwa Éaya uba Éaya?".
kayan suna da nauyi sosai ban Éauka ba na Éago ina kallon Fatin na ce,"amma ai kin san hanyar kitchen Éin Fati ki shiga ki zuba mana ko na taÉa hana ki. idan ma shiga kitchen Éin ba za kiyi ba ai ga flask Éin su Atika nan kan dining ki zuba mana".
"banga zan iya yin duka biyun ba, kece matar gida kece da dafawa da zubawa. saboda haka ki zuban abincina kawai ko na haÉaki da Yaya Æaramin shi ai ya isa da ke idan ita Iyam Éin kin rainata".
kallonta kawai na ke raina na sosuwa har ta wuce ta zauna kan kujera tana Éaukan remote ta canja tasha. Iyam ta shiga Æwala kiran Nazifi, gabana na faÉuwa nayi s