NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 97

eni sun rushe cikin ƴan watanni, halinta da ɗabi'unta sun sauya, ban san laifin me na mata ba haka kawai ta ɗora dukkan fushinta da karan tsanarta a kaina, ko bikin da aka yi watan da ya wuce cewa tayi kowa ya zauna ya huta ni a tattara min duka ayyuka, haka na zama kamar wata ƴar aiki ko baiwa, nayi ta fama da uban wanke wanken kwanukan taron biki, shara kuwa har sai da na ranƙwafa saboda mugun riƙewar da bayana yay, da an tashi rabon abincin zata kira sunana ta yarfo min zagi tace in ɗauka in bi mutane in raba musu, ban da damar zama ko na sakanni, hatta kashin ƴaƴa da wankan yaran baƙin kunya duk ni ce, haka tasa aka wareni a gefe wai banda amfani, ta mayarni kaman wata jaɓa, na sha baƙin ciki da takaici a bikin nan, har sai da na dinƙa jin kaman in gudu gidanmu, sai dai ban isa ba YaShaik tsab zai takeni idan yaji cewar nayi yaji. Su kan su ƴan bikin sai da suka ɗinka tausaya min wasu na cewa ya kamata a barni in huta, in huta tunda surukan gidan gamu nan fal, to amma ban isa ba, zaman hutawata daidai yake da zaman hutu a gidan iyayena tun da har Yaya na fushi da ni. To ni kam yanzu mugun tsoron Yaya nake yi, Wallahi a baya da zarar ta ganni take washe baki ta buɗe min hannaye in tafi jikinta ta rungume ni, amma yanzu har gwara naga hukuma su ce kamani suka zo yi akan ganinta, ganin ma ace a gidana. Harar da ta banka min ita tasa na razana na ƙarasa gaban kujera cike da furgicin ganin fuskarta babu annuri. haka na rakuɓe tsugune kamar an jijjiga ɓera a buta, ji nayi gaba ɗaya ta cika falon saboda irin matan nan ne zabga zabga masu ƙiba, duk da idona a ƙasa yake amma ina jin irin banzan kallon da take jifana da shi, tana aikin kyaɓe baki kamar taga amai, ganin na buɗe baki cikin fusata ta katse ni. "Lumɓu-lumɓu wutar ƙaiƙayi, tsiga tsiyau kazar matsiyata, wato saboda ba ki da mutunci, ba ki da tarbiya, ba ki da ɗa'a, ba ki san darajar na gaba da ke ba, ni kike jira in gaishe ki...me kika taka da har kike ganinki daidai da ni?, ko saboda an ɗauko ki daga tsiya an rufa asirinki cikin daula shiyasa kike ganin kinfi kowa?, aikin banza shafa lalle a ɗuwawu uban me ma kika aje a gidan da har za ki gadara. to ko shi me gidan yayi kaɗan in zo gidansa ya wulaƙanta ni wallahi, ke ga ƴar iska kina so ki nuna min dangin mijinki mutanen banza ne a wurinki, shiyasa har kina ji ina kwaɗa sallama ki ka barni a shanye, wato in gaji in bushe in kama gabana, to idan ba ki sani ba ki sani, ni mai sakawa ya sallameki ne kuma kin sallamu wallahi, ko idan danginki ne za ki wulaƙanta su har haka?, wato sai ni Yayar mijinki ƴar banza tazo miki gida ba za ki amsa sallamarta ba ko?". Jiki na rawa na girgiza mata kai alamar a'a ina faɗin,"duk ba haka ba ne Yaya, don Allah don Annabi kiyi haƙuri, wallahi sam banji sallamar ba ina aiki...". Daka min tsawa tayi tana katse sauran maganata, cikin faɗa sosai take cewa,"dalla rufe min baki munafuka algunguma makira mara tsoron Allah, aikin uban me kike yi a gidan nan banda kici ki kwanta, to idan ma aikin ne fina yayi da ba za ki iya katse kome ne ba, ballantana babu aikin da kike kina kwance sharaf kaman kayan tsinuwa, rashin mutunci dai irin na matan yau shi ya hanaki fitowa". Na haɗiye abin da ke tokare a maƙoshina ina karanto hasbunallahu, cikin sadda kai ƙasa nace,"don Allah kiyi haƙuri hakan ba zai ƙara faruwa ba in sha Allahu, ki yafe min Yaya don Allah". Sai na miƙe tsaye jiki babu ƙwarin kirki na shiga gyara kan kujerar da yake a gyaransa nace,"Bismilla Yaya ki zauna". Ta maimaita,"in zauna?...Sa'ida saboda raini da cin fuska ni kike kallo kina ce min in zauna saboda ga jarababba ta isheki da hayaniya, Yo Sa'ida har wacece ke a gidan nan da sai kin ban izini akan abu, ko tunaninki umarninki nake jira shiyasa nake tsaye har wa yanzu?, Ehh lallai yarinyar nan kin riƙa, wuyanki ya isa a yanka, raini da cin fuska mai muni har haka?, ina Yayar mijinki za ki wulaƙanta ni?, to uwar me kike gadara da shi a cikin gidan nan?, tun da aka auro ki wacce tsiyar kika aje?, shekara takwas babu ɓatan wata balle ɓari, kin kasa ajiye ko tsinke sai aikin ci da kasayarwa, kuma a hakan kike neman gadara da gida, to ke a wa?". Sai tayi shiru tana bin ko ina na cikin falon da kallo,"ina Nazifin yake?". "Ya fita". "Ya fita ina?, Ƙarya za ki min, shi dama yana fita ne ya wannan lokacin?" Nace,"ai in ya fita magriba sai anyi isha'i yake dawowa, kuma yauma da mota ya fita ba lallai nan kusa zai dawo ba". Zagayowa tayi ta zauna kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza su, tana ta kaɗa kai. Na wuce kitchen na ɗauko ruwa da lemu na kawo mata, a kofi na tsiyaya ina ce mata ga shi, na duƙa gefen ƙafafunta, cikin taushin murya nace da ita. "Yaya don Allah ina neman afuwar laifin da nayi". Ba ta dai ce min komai ba har wucewar wasu sakanni, kafin ta kalle ni cikin zafin rai tace,"walla
🏠