an suna tare da mahaifiyarsa.
Yanzunma kallo su ke yi sai dai ita da shi suna hira jefi jefi, yaran ne hankalinsu ya tattara ga tv, nayi sallama su ka Éago su ka kalleni, a daÆile Iyam ta amsa shi kuwa sai tsareni da ido yay, sannu da hutawa nayi mata domin mun rigada mun gaisa tun Éazu, na tambayeta abinda take so a dafa da rana tace faten tsaki amma yaji gyaÉa da ganye na ce to, miÆewa nayi na wucewata kitchen ban bi ta kansa ba da bakinsa da naga yana son magantuwa da alama. tun zuwanta na daina dafa son ran kowa sai na tambayeta me take so a girka, har ga Allah jinta na ke yi kamar uwata, kullum ÆoÆarina in kyautata mata amma sam ba na tsira, komai na yi bana burgeta balle yay mata daÉi, burinta ta kushe ni kawai, ku san kullum sai ta faÉa min bata sona bata son zamana da Éanta, maganar tun tana damuna ma har na daina jinta, takurawar da baiwar Allah nan ke min yayi yawa, ta hana ni shan iska kwata kwata, ta hana na huta na sake, magana tsakaninta da ni daga gori sai cin mutunci da zarafi, kuma duk wannan abubuwan da take min daidai da rana guda ban ji ina so na mata rashin kunya ba ko na Æi bin umarninta, uwa ce ita ko bata haife ni ba ta haifi mijina.
ina tsaka da aiki sai ga shi ya shigo kitchen Éin, tun kallo Éaya da na masa na watsar, ya shiga dube duben da zai yi, ni na san babu abinda ya shigo da shi sai don dai yay min magana kawai.
kusan minti Éaya yana faman bulayin iska ganin na basar da shi sai ce yayi,"babu abunda ake buÆata?".
kamar bazan amsa shi ba sai can na ce,"babu".
"komai akwai?".
na ce,"ummm".
shiru yayi na Æ´an sakanni sannan ya sake cewa,"ki saka daddawa da yawa a ciki bata son fate babu daddawa".
na ce,"na sani ai".
ina jin kallonsa a jikina har ya fice a kitchen Éin. bayan na kammala girkin Iyam na fara zubawa na kai mata Éakinta, na zo ina zubawa yaran nasu sai Æwala kiranta naji, naje da hanzari gareta cike da ladabi da girmamawa. flask Éin abincin ta turo gabana tana cewa,"wannan abincin na ki ai kin cika tafarnuwa tayi wani bauuu, ni kuwa kin san idan tayi yawa bana iya ci. Éauki kije kawai idan anyi na dare na ci".
shiru nayi na kasa motsi, wai tafarnuwa! ni da rabon da nayi girki ma da tafarnuwa har na manta, tun farkon zuwan su Atika na daina amfani da ita saboda Rumana bata ci, kawai dai saboda ta janyo min faÉa wurin Éanta, kuma yanzu na san ba komai yasa ta yin hakan ba sai ganin zan fita ne, tunda a gabanta na tambaye shi ya ce naje amma kar nayi yamma, to fitar ce bata so idan na Éata lokaci sai yace in fasa ranta yay fari.
na sauke numfashi na ce,"to me zan Æara dafa miki?".
"a'a ke da kike sauri za ki fita ai bana Æara sa ki wahala ba".
nayi murmushi na ce,"fitar ba ta fiki muhimmanci ba, in dai fita ce kam sai na haÆura da ita akanki. don Allah ki faÉa min me zan dafa miki babu wahala ga aikin uwa".
"soya min wainar fulawa, amma kar kisa taruhu me yawa kuma albasa taji sosai".
na ce,"tou". kana na miÆe na tashi na fita. har na sa a raina na haÆura da fitar sai ga shi kuma na gama suyar da wuri. na kawo mata fuska babu yabo babu fallasa tace an gode Allah yay albarka, naji daÉin adu'ar da tayi min karon farko tun zuwanta gidan. na fita na koma kitchen Éin na kwaso nasa kayan abincin sannan na wuce zuwa Éakinsa. yana shirin fitowa muka yi kiciÉis tray Éin hannuna ya kusa faÉuwa yay saurin tareni. bai bani hanya na wuce ba ni kuma ban ce masa kanzil ba tunda dai ai yana da ido, hannuna ne dai ya Æage saboda nauyin kwanukan cikin tray Éin, yay tsaye akaina kaman wani sanda, ganin tsayuwar tasa ba me Æarewa ba ce na raÉa ta Éan tsukukun gefensa na wuce, na shimfiÉa carpet Éin da yake cin abinci akai tukunna na Éora masa kayan abincin.
Shi kuwa baki buÉe ya ke kallonta, ta raÉa shi ta wuce har tana noÆe jikinta saboda wulaÆanci, bai san nufinta ba da wannan zaman da ta tsira tsakaninsu, tana ta wani shareshi tsabar raini, ga dai shi tana sakin jiki da mahaifiyarsa wani sa'in ma da yaran, amma shi sai wani nuna halin ko in kula take masa, da sun haÉa ido sai ta haÉe rai tana faman ciccin magani, ta mayar da shi kamar wani Éan iska sai yake magana tana amsa masa a daÆile, shiyasa yake ganin kaman ba ita ba an sauyata, don mamakinya ke sosai akan canjawarta, kuma ya Éaga mata Æafa ne kawai don yaga iya gudun ruwanta, sai dai ya lura idan bai yiwa tufkar hanci ba haka za'a ci gaba da tafiya, zata mayar da shi shashashan miji ta bakin Iyam, kusan satika nawa ko ta hakkinsa ma ba ta bi, ko so take har sai ya nuna mata cewa ya gaji yana da buÆatar kasancewa da ita ne, yanayinta sam ma ba ya nuna tana da damuwa yanzu da shi, tayi wani haske Æirjinta ya cika, ko faÉa yay mata yanzu sai ta Éau fushi da shi saÉanin da da hankalinta zai ta shi ta rasa sukuni, lallai yay sake ta yawa.
ina sauke ajiyar zuciya ta gajiya na dubi inda yake na ce,"ga abincinka in zuba ya