NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 58 of 97

haƙurina da sanyina a gefe na ɗan wani lokaci in fara rama abin da ake min hakan zai saka duk su saduda, amma wannan haƙurin da na ke shi ke basu lasisin ci min fuska har shi mijin. saboda haka na aro rigar rashin mutunci da masifa da bala'i in saka in zama kamar wuta saboda zafin rai, in ci kutumar uban duk ɗan iskan da yay min ko da kallon banza ne balle ya nemi ya gaya min magana, ta ce harta uwarsa kar in raga mata, ƙarƙari in koyi kissa in yi kaman zan mata sujjada a gabansa amma a bayan idonsa in nuna mata karrr na ke bani da mutunci ko ƙwas, idan na fara hakan za su rabu da ni su kama abun da yake gabansu nima in huta. na ji shawarartata na ɗan hau kan wata, tun da lallaɓawa na ke kar na zaƙe da yawa ya kuma kai ƙarata gidanmu in shiga uku. yanzun dai yadda nake haɗe rai idan na gansa har shakkar yi min magana yake, na fita harkarsa gaba ɗaya na cire tsoro sai ya fara mamakina hakan kuma ya dame shi, ya fara neman shishshige min yana neman shiri, ni kuwa sam naƙi basa fuska na nuna masa nima mutum ce me zuciya a ƙirji. ko fita zai yi bana damuwa da in bisa in masa a dawo lafiya, sai ga shi in yaga dama wani lokacin idan zai fita ya zo yace min zai fita, ba kuwa na ɗaga ko gashin gira na kalli inda ya ke, hatta ɗakinsa yanzu tsakanina da shi in kai masa abinci da na gama gyara kuma sai washegari, karatu ma sai na so nake zama yay min, ranar nan babu yanda bai da ni ba akan in zo ɗakinsa cikin dare nayi mursisi naƙi zuwa, domin na ƙudurci ni da zuwa ɗakinsa sai ranar da ya san darajata. To haka dai na ke ta zaman babu daɗi, duk wani nawa da ya kamata ya zo gidan in gansa inji daɗi Abbaa ya hana domin da kansa yasa aka kira masa me gadi da shi Nazifin ya faɗawa me gadin duk baƙon da aka yi ya tambaye shi wurin wa ya zo, in dai wurina aka zo to kar ya bari a shiga. to Yashaik ɗin ma da yake zuwa ya daina, in ya zo dai faɗa ne ke kawo shi to amma a haka na ke farin ciki. ta ɓangarensa yanzu ba na da wata matsala tunda babu abunda ke haɗamu, daga wajen Iyam ne dai da kuma ƴan uwan nasa abun babu sauƙi matsalar ta tsananta har tafi da, sun matsa min sosai cin mutuncina su ke yanda suka so. duk abunda su ke min haka nake shanyewa in hana kaina damuwa tun da dai haihuwar ba ni zan bawa kaina ba, haka kuma shi da su ke yi akansa ɗin ba ya yi min, tunda ba shi su Atika ya rage nuna damuwa akan rashin haihuwar. Maman Yasmin kuwa ranar ta saci hanya tazo ta dinƙa faɗan maita da rashin zuciya irin nawa ne yasa na ke zaune a gidan, in bar musu gidan mana rabuwa da Nazifi ai ba shi zai hana ni ƙara yin aure ba. na ce mata sam ba rashin zuciya ba ne ina gudun bakin mutane ne da kuma ɓacin ran iyaye, domin duk ranar da Abbaa ya tashi zai ce min babbar biyayyar da zan masa ita ce na zauna gidan mijina, Ummani kuwa da ta tashi yi min nasiha zata fara ne da haƙuri sannan ta tafi ga batun babbar suturar Ƴa mace shine aure, kuma gidan miji shine mafi daraja wajen ƴa mace. Yau ya kama lahadi, na tashi da sha'awar yin jan lalle, dama zan je kitso in sha Allah daga can zan wuce ayi min ko iya hannaye ne, da yake muna da taron suna ranar laraba jiya Ummani ta kirani take faɗa min Asiya ta haihu ƴar ƙanwar su Abbaa wacce su ke uba ɗaya, haihuwar sosai ta sakani farin ciki kuma a sannan nima na cire tsammani akan ba zan taɓa haihuwa ba, domin kuwa Asiya ta riga ni aure ita shekara goma kenan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar, babu irin tsangwamar da bata sha ba don zan iya cewa har gwara ni, tunda ita sau biyu mijin na sakinta, ga kishiya da ta sanyota gaba, da yake Allah ne mai bayarwa komai kuma Lokaci ne sai ga shi yanzu Allah ya bata, ni ma Allah yasa ina da rabo, ya bani ko don masu goranta min da ganin ni na gaza. bayan na shirya na fito domin naje na yi ayyukan da zan yi, a falo na tarar da su gaba ɗaya a zaune, dama tun zuwan Iyam gidan duk ranar Lahadi yini su ke a falo gaba ɗayansu, in ba yaran ne za su wuce islamiya ba, shi kuwa tun can asali lahadi ranar hutawarsa ce da lokacin iyalinsa balle yanzu da mahaifiyarsa ke gidan, in ba masallaci ba ko ƙofar gida ba ya leƙawa. ni dai in ka ganni a falon to zirga zirgar aiki ce don ba na zama balle raina ya ɓaci, idan tana zaune na zo na zauna don tayata hira in ba ya nan sai ta kama faɗin kana zama tare da surukarka waje ɗaya saboda rashin ɗa'a, idan kuma shine zaune a falon babu ita na zo na zauna sai ta kama bambamin ai bani da kunya ba ni da tarbiya dole sai na nuna mata ƴar zamani ce ni, ina faman liƙewa miji alhalin na san tana zaune cikin gidan saboda dai ba na son zamanta so na ke ta bar gidan. ranar har ce tayi da shi ita akan lamarina na ƴan iskan mata sai ta iya tattarawa ta tafi, banda tana ganinsa kusa da ita kullum hankalinta na kwanciya ai tuni ta kama gabanta, yay ta bata haƙuri ni kuma ya sameni yace ko magana na ke son yi da shi in ke iske shi ɗakinsa kar in ƙara zuwa gareshi id
🏠