NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 57 of 97

turare ne aka yi a gidan cikin kowanne ɗaki. Awa guda da wasu ƴan mintuna na ɗauka ina gyaran, na ci wahala sosai don bayana kamar zai karye. bayan na gama na saka turaren wuta da air freshner sannan na fito na sameta ita da jikokinta, na kalli agogo ƙarfe tara da rabi, cikin girmamawa na durƙusa gefenta na ce,"Iyam na kammala ko za ki duba ki gani". tashi tayi tana cewa,"mu je in gani Allah sa ba gyaran son zuciya kika yi ba". tayi gaba ni kuma na ɗauka jakar kayanta na bita, hankalina sam yaƙi kwanciya da zamanta ɗin a gidan. tsaye na sameta tana bin ɗakin da wani irin kallo, har cikin ranta nasan yayi mata amma kawai dai saboda a kushe a nuna baka iya ba don an tsaneka sai ta kyaɓe fuska ta dube ni ta ce,"kayana fa to?". kafin na bata amsa sai ga ɗan nata ya shigo da ƙatuwar katifa wadda ta kan gadonsa ce ya ciro, wajen biyayya kam a wajen mahaifiya ba daga nan ba, shiyasa ita kanta kaf ƴaƴan nata tafi sonsa. na kama masa muka sanya katifar ya ba za mata sabon bedsheet me bala'in taushi, ya koma ya ɗauko sabon blanket da ya taho da shi daga saudiya ya ajiye, dama akwai sababbin fulalluka duk aka saka mata. da yake da taimakonsa aka ƙarasa gyaran sai ta washe baki tana yabawa sai jera masa sannu take yi. sannan ne shi kuma yake cewa da ita tayi haƙuri zuwa gobe a kawo gado da wadrobe da dai sauran abubuwa buƙata. "a'a ni hakan ma ya ishe ni Nazifi Allah yay maka albarka, abu da ba zaman dindin zan yi ba, Malam ne fa yana dawowa zan koma gida, idan na zauna can ne hankalina sam ba zai kwanta ba tun da gidan naka ya rasa macen arziƙi". kallona yay ta gefen ido ina kallonsa, ya ja numfashi ya sauke ya ce,"duk da haka dai za'a saka komai zuwa gobe in sha Allahu, Malam ko da kwana ɗaya zai yi ai ba zan barki haka ba balle watanni da yawa zai yi". "to ai shikenan, kaje ka kwanta ka huta sai da safe. yaran ka turo min su nan mu kwana tare". ya juya ya fita nima na bi bayansa bayan na ce mata sai da safe, ba kuma ta tanka min ba banda tsaki da ta bini da shi. Tun daga wannan ranar na janye jikina daga shi Nazifin, Yaran da kuma Uwarsa, tsakanina da su gaisuwa ce, shine ma kawai zan samu arziƙin ya amsa min amma ita Iyam kam dama naci daraja ta amsa ciki ciki, shi kuwa idan ba maganar da ta zama dole ba ko ganinsa ma bana tsayawa na yi. ƴan uwansa kuwa sai su zo su yini ban gansu ba, don yanzu sun mayar da gidan kamar na su, tunda mahaifiyarsu na ciki a sati bai fi sau uku ne basa zuwa ba, kuma in aka zo tun safe sai a yini ana nuna iko da isa, aita bidiri ni dai bana bi ta kansu tun gaisuwa da zata haɗamu wacca za'a amsa min a wulaƙance, dama in suka zo bana girki da kansu su ke shiga kitchen su dafa son ransu, sunce suna da iko da gidan don haka ba za'ai masu iyaka ba, ni dai ko kusa bana taɓa biye musu zaman ɗakina ya fishshe min. Ni a yanzu ba Nazifi ne kaɗai bana so ba hatta aurensa bana so, kuma har mutuwa ta naɗe ba zan manta da baƙin cikin da ya dasa min a zuciya ba, bana tuna komai da yay min, haka bana tuna duk abin da ƴan uwansa da uwarsa ke min, abu ɗaya na ke tunawa da shi kaɗai ya tsaya a raina shiga tsakanina da mahaifina da yay, har ta kai yanzu idan na kira wayar Abbaa ba ko da yaushe ya ke ɗagawa ba, idan ya ɗaga kuwa magana sama sama, wataran ma sai dai na kira Ummani in roƙeta ta haɗa ni da shi. fushi da Abbaa ke yi da ni shi ɗaya ne ciwon da ke dashe a zuciyata, ba Nazifi da abin da ya dangace shi ba, hakan ne kaɗai yanzu abin da ke saka ni zubar da hawaye a kowacce rana amma ba akan Nazifi da takaicinsa ba, haka ina ji ina gani mahaifiyata ta kwana uku babu lafiya amma Abbaa ya ce in har na zo gida babu ni babu shi, ranar ban iya runtsawa ba, ban iya shan ko da ruwa ba, amma a haka muka yi waya da mahaifiyata tana bani haƙuri da shaida min ta sami lafiya bacin na san kawai ta faɗa ne saboda in kwantar da hankalina, ƙarshe sai yaran ne su ka zo suna ce min sunje duba Ummani har ma ta basu sabuwar atamfa a ɗinka musu, suna ta murna abinsu suka bani na aje musu na ce su kaiwa Kakarsu. Yashaik kusan duk sati biyu sai ya zo gidana, ko in bai zo ba ya kirani a waya ya ce in ba su, da kansa zai saka yaran a gaba da tambayar ina yi musu wani abun ne, wannan kuma na san sawar Kaka ne, to da yake dai ƴan sharrin basa kansu sai suce masa bana musu komai, ban sani ba ko da na fita a sabgarsu ne yasa su ka fara sanyi da makircinsu oho, ni yanzu abu ma idan ina da buƙata Ummani na ke kira, ita ke tura min kuɗi in kashe sabgar gabana da yake yaga idan na tambayi fita yana bari. kuma dalilin rashin zuwana gida duba Ummani Maman Yasmin ta kira ni a waya, na zayyana mata duk abin da ya faru tace ashe shiyasa Yashaik yaƙi haɗa kayan sallah da ni wannan karan, ta tuna ranar har itama sai da yay mata masifa, nan fa ta hau min faɗa da ke jarababba ce itama shiyasa ita ɗaya ke iyawa da jarabar mijinta, kafin ta shiga roƙona akan in aje
🏠