NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 56 of 97

yara". "ya dai fi mata kwanciyar hankali". ni dai ban ce komai ba, ban sani ba yin shiruna ne ya ƙular da ita ko mene oho, na dai ga ta fusata ta ƙara ruwan bala'i sai faɗin maganganu take na cin mutuncina da zarafina. Shi da kansa ya shiga bata hakuri, bata dai yi shiru ba ta haɗe faɗan har da shi ɗin tana zagi, ya rikice yana dubana rai tamau tare da watsa min mugun kallo ya ce,"wai Sa'ida me yake damunki ne, a gaban mahaifiyata fa kike, kin yi mata laifi kuma ba za ki iya buɗe baki ki bata haƙuri ba, zan ɓata miki rai fa". ido na ɗaga na kallesa na sauke, in bada hakuri! akan laifin da banji ba ban gani ba? ai haƙuri na gama bayar da shi a gaban iyayena, sai dai komai zai faru ya faru amma ban bawa kowa haƙuri a cikinsu, da me zan ji?, Cin mutuncinsu da zarafinsu? Ko kuma sharrin yaran da makircinsu? ƙuluwa yay sosai ya shiga jijjiga kai yana nuna ni da yatsa ya ce,"mahaifiyata! kin fi ƙarfin bata haƙuri ko Sa'ida, za ki gane kuranki". Iyam ta ce,"ƙyale mahaukaciya marar hankali da tausayin yaro, juyar banza da wofi mara tarbiya da bata san darajar uwa ba, Allah dai ya rabamu da ƙyashi da baƙin ciki da girman kai, ki bari randa kika haifa ko iyayenki suka zama wasu kyayi kowanne iskanci, amma yanzu wace ke, juya ko ƴar talakawa? kina gida zaune ba ilimi babu aiki, komai sai dai a miki". zagin ya ci min rai, nayi kamar na miƙe amma na daure na zauna saboda tunawa da iyayena. faɗan Abbaa da kashedin Kaka gareni ya fara tariya cikin kaina, na hango ɓacin ran da ke shimfiɗe saman fuskar mahaifina. kawai sai na gyara zama cikin karyewar zuciya, na fuskanci Iyam cikin raunanniyar muryata na ce,"don Allah don Annabi kiyi haƙuri da dukkan abun da ya faru". shima na fuskance shi a hankali na ce,"kaima kayi haƙuri". cikinsu babu wanda yace da ni komai. kaina dai a ƙasa duk wanda ya kalleni sai ya ji tausayina. shi kuma ya numfasa ya ce da mahaifiyar tasa,"Yanzu zan kai ki gida ko sai anjima?". kamar wanda ya tsikareta tayi saurin cewa,"wanne gida kuma Nazifi, ka mance yau Malam ya bar ƙasar ne, kai dai Allah yay maka albarka ya ƙara buɗi, ko don sanin girman iyaye da kayi ba zaka taɓe ba wallahi. ai zuwa nayi na zauna tare da ku zuwa Baban naku ya dawo, tunda naga lamarin gidan na ka yanzu sai ƙalu innalillahi, to kuwa kaga ai gwara a sami babba ya zauna tare da ku ko a samu raguwar wasu iskace iskancen. ni tun wancan karan da ta hora yaran nan da yunwa hankalina ya daina kwanciya gaba ɗaya, to yau kuwa da naji batun tana neman sumar da su ai bana ci gaba da zama ba ayi kisan kai muna can nesa, gwara in zo in zauna tare da su ganin idona yasa a rage wata muguntar". furucinta ya zama daidai da saukar tsawa a tsakiyar kaina, na ambaci innalillahi wani innalaihi rajiun, zaman Iyam a gidan nan? wanne irin zama za'ai kenan? shikenan kuma na ƙara shiga gagarumar matsala, farin ciki kam nayi bankwana da shi, sai abin da naji na gani. "wanne ɗakin zan zauna? ko kuwa ma ɗaki ɗaya zamu tare da yaran, don ni gaskiya ina tsoron sharrin wannan ƴar, kar ta koma bin cikin dare ta cutar da jikokina, ba ka san wanne shiri mugun mutum ya ke yi ba, Allah dai ya karya alƙadarinta kawai". ya sauke numfashi ya ce,"su a sama su ke, ke kuma kinga ba za ki juri hawa da saukar ba, tunda akwai ɗakuna a ƙasa sai a kimtsa miki wanda kika zaɓa". ya miƙe yana ɗaukar jakar kayanta, suka yi ɗakina na ƙasa, suna zuwa naji ta ja dogon salati tana faɗin,"Nazifi ya zaka kawo ni wannan ɗakin, na san mene a cikinsa zaka ce in kwana, ai wallah sam ba zai yiwu ba. gwara ka barni in ke kwana a falon na ku ni ba baƙuwar zafi ba ce, amma wannan ɗaki kuwa sai in ƙur'ani aka sauke masa akayi turarukan karya sihiri shine sai in iya kwana, amma ba haka sakaka ba ban yo shirin komai ba duk da cewar azikarin safe da maraice bai wuce ni". ya ce,"haba Iyam ko baƙo ai ba za'a barsa ya kwana a falo ba balle ke mahaifiyata, ɗakin naki ne sai an kaɗe ƙura tukunna kin san ba wani amfani ake da su ba, kuma dole sai an sanya gado a ciki". "ai Nazifi ko a dandariyar ƙasa ni mai kwana ce akan dai kwanan ɗakin matarka". "tom bari naje na gyara miki". su ka dawo falon har lokacin ina zaune yanda suka tafi suka barni, suka wuce zuwa ɗakin da zata zauna ta dakatar da shi da cewa,"a'a to wai ita waccan shafaffiya da mai ɗin ƴar waye da tafi ƙarfin zuwa tayi gyaran". ta juyo gare ni tana cewa,"ashe haka yake tsoronki shiyasa ya kasa ɗaukar matakin komai game da rashin haihuwarki. to tashi maza gyara min wancan ɗakin na farko a shi zan zauna. in aka ce mutum na da haƙuri sai ai ta cutarsa, yanzu a ƴaƴana in ba shi da yake da uban haƙuri ba wa zai zauna kallonki kina ƙin girmama ni". haka na miƙe na wuce na shiga ɗakin, ni dai tunda muka zo gidan zan ce sau ɗaya na taɓa buɗe shi na shiga shima ranar Malam ya bada
🏠