a ya suÉuce da faÉin innalillahi wainna ilaihi rajiun, hasbunallahu waniimal wakil, ina fadar hakan kuma naji gabana ya sassauta faÉuwar da yake tare da samun wani guntun kuzari na sauko a gadon kamar mara jini na Æarasa na buÉe Æofan.
"Iyam ce ta zo, Abban kuma ya fita".
na ce mata gani nan zuwa kana na koma ciki na wanko fuskata da sabulu tare da tsayar da kukana. na Éau mayafin abaya na yafa na fita.
jin takun saukata ta kallo bene tana cewa,"kina takaicin zuwana ne da kike wani sakkowa a hankali".
maganartata sai naji kaman ta harÉe ni don saura Æiris in faÉo daga benen. na Æarasa wajenta cikin sauri ina durÆusawa in ce,"sannu da zuwa, an zo lafiya".
banzan kallo ta min tana cewa,"kina Éaki abinki a kwance har da su rufe Æofa, kika bar yara komai zai faru da su ya faru da su ba asararki ba ce".
cike da ladabi na ce,"da yake ban jima da shiga Éakin ba ne, tara muka hau saman da su ma suka shiga Éaki ban san sun sakko ba".
taÉe baki tayi tace,"in kana da Æ´aÆ´a ai baka shiga Éaki ka kulle ka barsu su Éaya ba, zama kake ka kula da su".
a hankali na ce,"ayi haÆuri. ina wuni".
bata amsa min ba ta mayar da hankalinta ga jikokinta.
na miÆe a sanyaye na shiga kitchen, abincina da mu kai takeway na juye mata na haÉo da drink da ruwa na kawo mata. kallonsu kawai tayi kamar bata gani ba kuma bata ji me nace ba. na zauna a rakuÉe Æasan carpet tace,"shi Nazifin yayi ina ne haka?".
"bara na kirawo shi a waya".
ta dakatar da ni,"da tawa wayar ai, ungo kira min shi".
hmm dama ko da na hau saman ma wallahi ba kiransa zan yi ba, zan sha zamana ne in sakko in ce mata wayar bata shiga. sai bayan katsewar kiran farko sai ga shi ya kira, na Éaga na mika mata, suka gaisa take faÉa masa,"na zo ne ai ake cewa baka nan".
ban san me yace mata ba naji ta ce,"to shikenan sai ka dawo Éin, amma ka hanzarta".
ita da yaran suke ta hirarsu, ni ba abin in tashi ba na jawa kaina magana, don haka na gyara zamana na jingina da kujera ina salatin Annabi cikin raina.
sai da aka yi sallar magriba ya dawo yake bata haÆuri da cewar yaje ne gidan Alhaji Fari. na basu wuri na koma Éaki bayan wasu mintuna ya kirani a waya ya ce na sakko.
da na fito ina jin surutun yaran a Éakinsu suna musun da suka saba akan assignment.
ni da shi duk muka zauna a Æasa, kamar wata basarakiya sai da ta ja lokaci kafin ta ce,"Sa'ida me yaran nan su ka yi miki ne kike azabtar da su umm?".
da Æwarin gwiwata na ce,"ni ba su yi min komai ba Iyam, kuma abun da zuciyar kowa ke faÉa akan ina zaluntarsu sam ba haka ba ne, sai dai ba me yarda da ni amma Allah na shaidata".
wai wannan Æ´ar maganar da nayi sai ta tunzurata ta kama cewa,"a'a tou ai ba ce nayi ki faÉa min magana ba Malama Æ´ar gidan Malamai da su kaÉai su ke da Allah. to ni dai batun jikokina ne zan shata miki layi tsakaninki da su, ba sai na rantse miki ba domin ni maganata ko babu rantsuwa tabbatarwa nake na aikata abun da na faÉa, Sa'ida in har kina son zamanki da Éana to kar Æara bar min jikoki da yunwa, hakana kar hannunki ya kuma kaiwa jikinsu, ke Éaga murya ma ban yarda ba. idan wani baÆin ciki ne a ranki kike so ki huce akan wani to ga shashashan mijinki nan ki huce akansa, ki cutar da shi shi Éaya amma banda jikokina...na san ba komai ke damun ki ba face baÆin ciki da hasssada, yo banda ma dai halin Éan adam na butulci ba ki haifa masa ba kuma ki ce ba za'a ba shi ba, ke kawai da ke Éaya zai zauna ba batun wani ya raÉe shi, in da ya so ai aure zai Æara wata matar ta haifa masa ba ya tsaya karÉar Æ´aÆ´an wasu ba, amma ke saboda ba ki san halacci ba shine za ki Éige da cutar da yara saboda ki raba tsakaninsa da Æ´an uwansa, to ta Allah ba taki ba, ba yanda za'ai yayi ta cika miki ciki da abinci kina kasayarwa a masai, wanne kalar taimako ne baiwa Æ´an uwanki ba? ina ce har kasuwa ya kai Yayanki. butulu marar halacci, to yara ne dai jinin Nazifi ne, shi da uwayensu ciki Éaya suka fito kuma nono Éaya suka sha, kinga kuwa ba ki isa ki raba shi da yaran nan ba sai dai baÆin ciki yasa ki haÉiyi zuciya ki mutu ruwanki. ni to bara ma na faÉa miki abin da baki sani ba, yanzu sam zamanki tare da shi bana Æauna wallah, Allah ya gani Æaunar jin zanceki ma bana yi, kin sire min kin fita a raina, badan kar ace na zama sheÉaniya ba da tuni na yiwa tufkar hanci, yo me amfaninki auren macen da bata haihuwa, zama da juya ai Æaddararran zama ne, haka kawai ina so naga tsatson Nazifi kin babbake gida kin hana".
Haihuwa! Juya! kalmomin nan nasa zuciyata matsewa, dalilin furucinta hawayen da ban san da su ba suka fara sauka.
shi kuma ta shiga cewa da shi,"Kai kuma ka Éauki mataki, ka gargaÉi juyar matarka akan taÉa min jikoki, idan ba zaka iya ba duk kalar matakin da na Éauka akanta ita ta jiyo".
ya ce,"kiyi haÆuri Iyam, ai na mata faÉa kuma tayi alÆawarin zata g