a na fuskance shi na rissinar da kai na ba shi haÆuri tare da alÆawarin ba zan kuma cutar da yaran ba, ba zan Æara yi masa wani laifi ba. kuma memakon komai ya lafa sai ma sabon faÉa ya tashi, Abbaa dai bai ce komai Éin ba bayan maganar da yayi sai Yayyuna da Kaka ne kamar za su cinye ni Éanya.
sai da Abbaa ya buÉi baki yace da Nazifi muna iya tafiya sannan ya miÆe yay gaba, Yaya Imam da Yashaik suka bi shi, ni dai kasa tashi nayi sai lokacin na rarrafa na Æarasa gaban mahaifiyata wadda ko tarinta banji ba a wurin, na kifa fuskata saman cinyarta, kuka na ke yi sosai a hankali ina faÉa mata ban aikata ba, ba ni ke da laifi ba akan komai, to roÆa min Abba ya sauka akan hukuncin da ya yanke.
ta Éora hannunta a saman kaina, kafin ta kai ga magana Abbaa ya doka min tsawa ya ce,"zaman uban me kike da ba za ki tashi ki bi mijinki ba".
da sauri na miÆe jiki duk babu Æwari ina jin jiri na neman zubar da ni, na saita kaina tare da janyo fuskar hijabina don kar yaran su fahimci abun da ya faru, Ummani ta ruÆo hannuna muka fito daga Éakin. falonta mu ka shiga muka tsaya a tsaye, a hankali ta ce,"tsakanin ke da mijinki ban san bayan wa zan bi ba, ke da shi duka akwai yardata akanku. amma ni dai ki sani haÆuri yana daga cikin abun da ya ke taya bawa samun nasara a duniya da lahira Sa'ida, duk abun da aka ce babu haÆuri da juriya a cikinsa to zai wuya abun ya kai ga nasara. kwantar da hankalinki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina faÉa miki Allah na tare da ke, zai tsaya miki akan lamuranki muddin ba ki da nufin cutar da wani. ke dai riÆe addu'a ki tsarkake zuciyarki ki riÆe yaran da zuciya Éaya ba cuta babu cutarwa, sannan kar ki Éata zaman lafiyarki da mijinki, don Allah kar ki Éauka huÉubar sheÉan ya zuga ki aikata abun da za ki zo kina danasani, yara ne ki gyara musu idan suka yi kuskure na goyi da bayanki domin alhakin tarbiyarsu akanki ya ke, amma ban da cutarwa don Allah Sa'ida, ki Éaukar min wannan alÆawarin".
na so ace na sami wadataccen lokaci tare da mahaifiyata tana lallashina da min nasiha, na samu na amayar mata da abun da ke cikina ko naji salama, amma ina Kaka na fitowa ya kama yi mata faÉa, ita kuma jin wannan da sauri ta sakeni ta ce na tafi saboda bata so sauran mutanen gidan su san abun da ke faruwa.
a hanya muna tafiya yay wani Æasa da murya yacca yaran ba za su ji ba yana min magana a hankali irin ta neman a shirya, don munafurci wai haÆuri ya ke ba ni, yana faÉa min in kwantar da hankali kar in saka damuwa a rai, zai fahimtar da ni idan mu ka koma gida. ni dai banza na yi masa har lokacin kuma idona bai daina zubar da hawaye ba, tsabar neman gindin zama har wani tambayata ya ke wanne restaurant zamu je muci abinci idan mun koma na huta da girki. can kuma sai ce yayi,"kin sanni akan son yara shiyasa amma ba don in muzguna miki hakan ya faru ba".
"hmm to waye ba ya son yara? Ba da tarbiya ne kawai ba kowa ya iya ba".
"hmmm". ya ce yana kira sunan yaran, su ka amsa yana ce musu,"Antynku ta ce muje restaurant mu ci abinci amma wai wanne kuke so mu je?".
caraf tantiriyar cikin na su wato Atika ta ce,"Anty inda muka je last week yafi kyau Anty aje can".
jin ban kulata ba ta ratso ta tsakanin kujerunmu tana leÆo kanta wajen fuskata. "kin ji Anty please".
sai a sannan na yi murmushin da ya fidda sauti na ce,"tom shikenan yanda ku ke so".
"ina kenan?". ya tambaya idonsa a kaina.
na Éaga ido na masa wani kallo na ce,"Calido".
"tom shikenan". ya faÉa yana Éauko glass ya miÆo min,"saka wannan". na san dalilin bani glass Éin, saboda haka na karÉa ban musa ba na saka, don duk me hankali kallo Éaya zai min ya san na ci kuka na Æoshi, haka kuma ina cikin matsananciyar damuwa.
a wajen cin abincin ban iya cin komai ba, tagumi kawai nayi idona akan teburin ina tunani kala kala, shi kuma ina jinsa da yaran suna cin abincinsu hankali kwance, komai suka gani su ka ce suna so sai ya ce a kawo musu, Æarshe dai nawa abincin sai takeaway aka yi min.
sai biyar muka koma gida, ni na fara fita a motar, muna shiga ciki ni da yaran muka yi sama, shi kuma yay Éakinsa na Æasa, don shi ra'ayinsa bai fiya wani son hawa bene ba, ko da za'ai ginin gidan saboda na ce ina son bene yasa aka yi amma da niyyarsa duk girman gidan ayi flat. ina shiga Éaki na kulle tare da faÉawa saman gado na yi lamo abun duniya duk ya ishe ni, jina na ke kamar marainiya mara gata, bani da masaniyar dalilin da yasa Allah ya Æaddaro min wannan lamarin ba, amma ina roÆonsa ya bani ikon cinye jarabawarsa da dukkan iyawata.
ina kwance naji ana ÆwanÆwasa Æofa, nayi banza saboda na riga na saka maÆulli babu damar a shigo, haka kuma ba zan buÉe ba don sam bana son ganin Nazifi da yaran, kusan mintuna Éaya ana ÆwanÆwasawar sai kuma naji muryar Rumana ta na cewa,"Anty ki fito ga Iyam ta zo".
ban san lokacin da bakin