NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 53 of 97

a ɗauko ya buga min a ƙashin baya. "bar ni da ƴar banza Nazifi da ina magana zata sako min baki tana ƙaryata mijinta saboda ta cika wadda bata san darajan manyanta ba. nasihar me za'a mata bayan ta san daidai da ba daidai ba, to billahillazi Sa'ida ba ki fi ƙarfin duka ba a wurina, in kina tunanin ni da kaina ba zan iya lallasaki ba zan sa Imamu yayi miki matsiyacin dukan da za ki dawo hayyacinki. don ubanki ba'a riƙe ɗan wani ita uwarki aka riƙeta, ba a haƙuri da halin yaro aka yi haƙuri da na uwarki, wa ya san kalar haƙurin da aka yi da ita, sai ke kin samu yara masu tarbiya da miji na rufin asiri shine za kike cutar da su gaba ɗaya". yay shiru na ƴan sakanni sannan ya kira sunana da cewar kina jina. na ce "ehh Kaka". "na rantse da tsarkin mulkin Allah kika janyo abun da zai rabaki da igiyar aurenki idan kin zauna a gidan nan Allah ya ɗauki raina a ranar, kuma sai nasa Salman ya sallamaki a ƴaƴansa. saboda haka ki shiga taitayinki, daga yau kuma wannan lokacin ki aje duk wani rashin mutunci da yake ranki ki kula masa da yaransa, kar na ƙara jin ƙorafi irin haka, bautar aure kika je yi ba zalunci da rashin mutunci ba". Na haɗiye yawu da ƙyar na ce,"insha Allahu Kaka, insha Allahu kawo ƙarata ba zai kuma zuwa gabanka ba, kuma don girman Allah kuyi haƙuri zan gyara nayi alƙawari". tun ɗazu Abbaana bai ce komai ba, kuma naji daɗin hakan domin ban san me nasa ɓacin ran zai sa ya gaggaya min ba, duka ne kawai Allah ya riƙi hannunsa darajar aurena, sai kuma takaici abun da Nazifi ya karanta musu akaina ya hanasa magana. gyaran murya yayi ya kira sunansa sannan ya ce da shi,"Nazifi wanne mataki zuciyarka ke faɗa maka ka ɗauka akanta? Kar ka ji nauyinmu". kansa ƙasa ya ce,"Abbaa nasiharku gareta kawai na ke roƙo". Abbaa ya sauke numfashi ya ce,"Bisa umarnina Nazifi, duk ranar da ta ƙara yunƙurin cutar maka da ƴaƴa ko ta nemi ta wulaƙanta ƴan uwanka don Allah kaima ka wulaƙantata, ka ƙuntata mata, ka ɗauki duk kalar hukuncin da zuciyarka ta yanke akanta kar ma ka kawota gabanmu...sannan bisa umarnina in har zanci alfarmar zama mahaifi gareka, ina so daga ranar yau ka datse alaƙarta da duk wasu mutane da take mu'amala da su idan ba ƴan uwanka ba ko nata, na tan ma sai wanda ka yarda tayi mu'amala da su in ba su maka ba ina goyon bayanka ka ci mutuncin duk wadda ka gani cikin gidanka". sai kuma ya juyo gareni ya ce,"ke kuma ki buɗe kunnuwa da kyau ki jini, idan ƴaƴan Sa'id ko na Imam aka ɗauka aka baki haka za ki cutar da su?". "a'a Abbaa". "to don me akan ƴaƴan ƴan uwan mijinki, baku fa akai saboda tausaya muku an san cewa rashin haihuwa da raɗaɗi, amma saboda rashin tausayi da imani sai ki ɓige da mugunta da zalunci Sa'ida, kuma akan ƙanan yara, haka ake yi dama? silar haka yanzu ba sai ki raba shi da yayunsa ba. yanzu can sun ba ki kin kasa riƙesu, kina tsammani cikin ƴan uwanki yanzu akwai wanda zai sha'awar ɗaukar ɗansa ya ba ki? in Allah ya ba ki ki mutu kika barsu wa zai ji tausayinsu ya ɗauka tun da an san uwarsu ba mutuniyar kirki ba ce". ya nunfasa,"to daga yau bisa kashedi me girma kar ki kuskura mijinki ya ƙara kawo ƙorafi akanki idan ba haka ba za ki shiga uku a hannuna, zan mugun saɓa miki ne, ki cirewa kanki duk wani mugun ƙuduri, zuciyarki ki ta so yaran kamar ke kika haifa, yanda ba'aji ƙyashin ɗauka a baku ba bai kamata ke kiji ƙyashin kula da su ba". "nayi alƙawarin gyarawa Abba, laifina ba zai ƙara zuwa gareka ba da yardar Allah, ka yi haƙuri ka yafe min". na faɗa cikin kuka me taɓa zuciyar me saurare ina haɗa hannayena wuri ɗaya alamar roƙo. ya ɗauke ido akaina ya mayar kansa ya ce,"kayi haƙuri Nazifi da duk rashin mutuncinta, na kuma gode da ka kawota muka san halin da kuke ciki. sannan abu na gaba da zan faɗa maka shine; yau ta zama rana ta ƙarshe da zan kuma ganin Sa'ida a cikin gidan nan har sai nan da tsawon shekara guda". ya faɗa yana juyawa ya kalli Yashaik yace,"Sa'id ka rubuta min kwanan watan yau". kana nima ya kalle ni ya ce,"kin ji me nace ai, kar na ƙara ganin ƙafarki cikin gidan nan har tsawon shekara guda cif, saɓa hakan kuma zai ja miki samun saɓani da ni ki kuma jawa mahaifiyarki shiga matsala". ya kalli Nazifi yace,"Allah yay maka albarka". ya ce,"amin Abbaa, na gode Allah ya ƙara muku lafiya...amma ayi haƙuri da batun zu...". "dakata wannan hukunci ne da na riga na yanke, ka riga ka san kaifi ɗaya ne ni bana sauka daga maganata. zuwa gidana na haramtawa matarka zuwansa ko da bisa izininka ne, idan tana so ta haɗu da mahaifiyarta su haɗu a wani wajen". ɗakin yay shiru don hatta sautin kukana babu domin nasa hannu na toshe bakina kamar yanda Yashaik ya umarce ni, babu abu mafi ciwo da naji irin hukuncin da Abbaa ya yanke min. haƙuri su ke ta bashi bayan nima sun sak
🏠