ya gagara sakko min, sai zuciyata da naji tana wani irin zafi. Allah Éaya ya san irin baÆin cikin da ke narke a Æasan zuciyata. na sani a yau kam ba ni da wani gata sai na Allah, ban da ta cewa domin a wannan dogon jawabin nasa babu mai tsayawa ya saurari nawa, za'a yanke hukunci ne kawai da iya abin da ya faÉa.
Kaka na kallonsa ya ce,"Yanzu kai haka ka zauna kana haÆurin Æunsar baÆin cikin yarinya Æarama, to ai ba shiru za ka yi ba Nazifi, ci gaba da zayyano shika shikan rashin mutuncin da take shuka maka, sam sam cire tausayinta a ranka ka zayyane mana komai, wannan muguwar ai tafi Æarfin aikata ta'addacin iya haka, maza zayyano min su kaji na san akwai wasu bila adad, kai kenan tsawon shekaru takwas Éin nan zaman haÆuri ka ke da ita baka taÉa hankaÉo mana ita nan ba an gyara mata zama".
ya ce,"Kaka ni dama cuzgunawa yaran shine dai damuwar, zan Éauki komai banda cutar min da yara da wulaÆanta Æ´an uwana, idan har aka saita haka Éin to komai me sauÆi ne".
na Éaga kai ina kallonsa da maÉaukakin mamaki, Namiji Æayar Ruwa, nama rasa wanne irin tunani zan yi akansa, amma komai LOKACI NE na (oum Mumtaz).
"Keee". Kaka ya kira sunan nawa a kausashe.
gabana ya faÉi, na Éago kai a sanyaye ina amsawa cikin dashewar murya.
"bar sadda kai Æasa munafuka, idona za ki kalla muguwa wadda taci amanar tarbiyar da iyayenta su ka bata, kuma ki sani ba kiyi mana adalci ba don sam babu koyarwar zalunci a Éabi'un ahalinmu, karo na farko da naji ina danasanin wani jika nawa".
sai kuma ya juya kan Nazifin yana faÉin,"kaima lusarin namiji da ka bari mace ta rainaka har tafi Æarfin ka hukuntata sai ka kawota gaban iyayenta, ta ya ma za'ai manyan abubuwa na faruwa irin haka ka zuba mata ido".
da faÉin haka sai jin saukar kwanon sha nayi kaf akan fuskata, da ya ke na silver ne hakan yasa naji zafi sosai, na rufe ido a razane jikina na rawa, zafin na cikin ratsa jikina sai ga Æundumemiyar ashariya daga bakin Yaya Imam wanda ya taso a fusace zai sa Æafa ya hamÉare ni sai shi Nazifin yay saurin dakatar da shi.
"kar ka dakar min mata Imam, ban kawota nan dan a Éora hannu a jikinta ba, na kawota ne domin a nusar da ita daidai".
"rabu da ni Nazifi in saukewa azzaluma mara mutunci iskancin da ya ke kanta...".
Yaya Imam Éin ya faÉa a zafafe cikin hasala.
yana shiru Yashaik ya ce,"da ya ke butulu ce ke wadda bata san alkhairi ba, har a Éauki Æ´aÆ´a a baku abun da ba kowa zai iya ba, ko mu nan Æ´an uwanki bamu yi tunanin hakan ba amma ki kasa godiya garesu da ubangijin da ya ba ki ta wata hanyar, sai rama khairi da sharri? to zatonki za ki ga daidai a rayuwa?".
Yaya Imam dai so kawai yake ya dake ni, don kaÉa Æafa yake ta aikin yi yana dunÆule hannu ya yarfar.
"banza kawai, duk irin halaccin da mutumin nan yay miki shashasha idonki ya ÆeÆashe saboda kina da baÆar zuciya za ki saka yara a gaba kina cutarwa".
Yashaik ya amshe,"yo ina ta san zafin rainon ciki da haife shi da zata san darajar Éa, tunda Allah bai bata ba ai bari ta kassara na wasu saboda tana baÆin ciki, to kuwa ina za'a ba ki haihuwa Sa'ida a wannan matacciyar zuciyar ta ki, ai ubangiji ma kyawun zuciyar mutum ya ke kallo yay masa ni'ima. ni wallah ban taÉa tunanin ba ki da hankali da tunani ba sai yau, ashe daÆiÆiya ce ke me amfani da ÆwaÆwalwar jahilan farko".
ya numfasa saboda yacca amon muryasa ya tsananta nuna Éacin ransa, ni kuma sai lokacin hawaye yay nasarar sauka daga idona, na Éora hannu bisa goshina kaina kife Æasa ina jin wani azaba daga zuciyata tamkar an cirota ana babbakata, ai dama ni na san kam yau sai abinda naji na gani, haka ahalina su ke idan ransu ya Éaci komai faÉa maka su ke yi, don ma dai shi Éin ya hana a dukeni da ba za su tsaya doguwar magana haka ba, kawo yanzu ina nan da fasashshen jiki.
zan buÉi baki nayi magana Kaka ya dakatar da ni a tsawace,"kika yi magana a wurin nan sai na faffasa miki baki don uwarki da ubanki mara mutunci. idan auren kika gaji da shi yasa kika tsiri wannan iskancin yanzu zansa ya sake ki ya huta da masifa, daga nan sai inga a inda za ki zauna kiyi zaman zawarcin don ba'a gidan nan ba".
ya kalli Nazifin ya ce,"maza rattaba mata kalaman da za su rabaka da ita har abada, in ya so kaje ka auro mai mutunci da tarbiya da ilimi me imani a zuciya ka zauna da ita wadda zata riÆe maka yaranka tsakani da Allah. ni bana goyon bayan kaci gaba da zama da wannan Æ´ar banzar yarinyar, ba sonka take ba, gwara ka sakota ko bara ne ta koma yi don babu wanda zai kuma Éaura mata aure, ba mutanen banza ba ne mu da zata je ta wulaÆanta mana ahali, uban da yake zugata taje taci gaba da zama da shi".
kuka na fashe da shi sosai ina girgiza kai na ce,"Kaka wallahi duk ba haka ba ne, ba haka ba ne Ka...".
Nazifin yay caraf ya ce,"Kaka ayi haÆuri ai mata nasiha kawai...".
sandar da Kaka ke doragawa wani lokacin ita y