NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 51 of 97

allo ya watsa min ba tare da ya amsa ba, yaran suka gaishe shi yana musu fara'a ya amsa tare da kama hannunsu suka shiga gidan, bayan yace da Hubbi Bismillah ka shigo. ya dube ni ya ce,"muje". na yi gaba yana biye ni da ni a baya, jikina duk a sanyaye don ban san me ke faruwa ba, kuma ƙwaƙwalwata ta kasa haska min abin da ka iya faruwa ɗin. Ummani na tsakar gida muka shiga, yanayin fuskarta sak na Yashaik babu annuri, karo na farko da banga farin cikin ganina ba duk sanda na zo gida a tare da ita. ta sakarwa Hubbi fuska su ka gaisa tana shi masa albarka sannan ta ce mu shiga falon Kaka. shi ya fara shiga daga ciki, ni kuwa tsayawa ni na kasa shiga saboda tsabar tsoro, ƙirjina sai fat fat ya ke, Ummani ta zo ta wuce ni ta shiga. Kaka ya danno min zagi ba shiri na ɗaga labule na faɗa ciki. ciki ciki duk suka amsa gaisuwata, Kaka ne da Abbaa da Yashaik da Yaya Imam sai Ummani, banga yaran ba ina ga suna ɗakin Ummani. gefen kujerar da Ummani ke kai na zauna, a tsawace Kaka ya ce in dawo daga tsakiya, na miƙe ƙafafu na rawa na isa in da ya nuna min. Kaka ne yay gyaran murya yana fuskantar Hubbi ya ce da shi,"Nazifi me yake faruwa? ka faɗi duk irin ɗibar albarkar da ƴar banzan yarinyar nan ke yi maka a gidanka ni kuma zan sa ka ɗauki matakin da ya da ce da ita don ubanta Salman da yake zaune kusa da ni, ahalinmu kaf ai babu ɗan iska to me kuma dalilin da zai sa a samu ƴar banza a gidan aure". furucin na Kaka yasa na ɗago a ruɗe ina kallonsa, kafin in kalli Hubbi da ya fara rattabo zance tamkar ɗan jarida. "amm Kaka dama matsalar dai akan yaran da Yayyuna su ka bani ne saboda sunga Allah bai azurtani da haihuwa ba, wannan tausayin yasa suka ɗebi yara har biyu suka bani halak malak, sun bani domin suna da yaƙinin zan riƙe su bisa gaskiya da amana haka kuma da yaƙinin ita iyalina zata kula da su. da lafiya lafiya mu ke zaune da Sa'ida Kaka ba wata matsala sai ɗan saɓani na wani lokaci da ba'a rasawa ga ma'aurata. amma tun zuwan yaran sai ta sauya gaba ɗaya, ta canja ɗabi'u, ta ɗauko wasu halaye na banza ta ɗorama kanta, ban san wa yake zugata ba ta ɗora karan tsanarta akan yaran nan, bata sonsu sam, kuma abin sai ya shafa har da ni, yanzu haka zancen da na ke tsakaninta da Yayyuna kallo ne bata ko gaishe su. kuma da aka ce an mallaka min yaran saboda na fita hakkinta don ban san ba ko ita zata iya cutuwa tun da ba kowa ne ke iya karɓan ɗan wani ba, lokacin ta nuna farin cikinta har da hawayen murna. amma yanzu ban san mene matsalarta da yaran ba, tsakani da Allah suna mata biyayya, amma ita kenan kullu yaumin cikin muzguna musu take yi, bata da burin da ya wuce taga sun ƙuntata, tamkar marayu haka suke komawa a gidan idan ba nan. kwanakin baya haka ta hora su da yunwa, ta hana su abincin safe kuma ta ƙi ba su na makaranta, wallahi ɗayar cikinsu Atika daga makaranta aka kaita asibiti kamar zata mutu saboda ciwon ciki, sai kirana akayi a waya aka shaida min, ina zuwa asibiti likitan yace yunwa ce a dinƙa bata abinci. to wannan ya wuce ma. jiya nayi tafiya kaduna tasa yaran a gaba ta zane akan ta dafa abinda ba sa ci sun ce a dafa musu wani, kawai sai ta hau zaginsu har tana cewa zata saka su wani gida a saka su a ɗakin karnuka, wai har da baƙinta suma suka rufarwa yaran, haka su ka yini babu abinci sai da safen nan da zan kai su makaranta su ke faɗa min abin da ya faru, saboda a gidan kasa faɗa min suka yi saboda tsoronta ta ce zata faffasa musu baki. wallahi yanzu haka shatin waya ne a bayan ita Atikar alamar ta zanu iya zanuwa, sai da ta nuna min ma na ke jin zazzaɓi a jikinta alamun ba lafiya tabbacin dukan ne ya haifar mata da zazzaɓi, har raina ban ji daɗi ba, ina son yaran, ko ɗan wani ba zan so inga ana zaluntarsa ba wallahi balle wanda ya ke nawa, duk da bani na haifesu ba amma ko yau Allah ya bani nawa ba zan banbanta su ba. tsakani da Allah idan iyayensu suka san abinda yake faruwa sai ta raba zumuncina da su, abin da ya faru wancan karan har yau mahaifiyata na fushi da ni, ba wanda zai ji daɗi yaga ana cutar masa da ɗa. to Kaka ni tunda gaskiya na kasa gane kanta shi ne na ce bari na kawota gareku, aji ta bakinta mene yaran su ka mata, kuma mene matsalarta da su ƴan uwana da yanzu ma gaba ɗaya bata shiga sabgarsu don ko abu ne ya kama na gidanmu kaitsaye zata ce min ita bata son zuwa. to ayi haƙuri a mata nasiha ta gyara don ni idan nayi mata ta dinƙa botsare botsare a gidan, in kuma wani laifi na mata da yasa ta ƙullace ni ta faɗa a samu masalaha. amma gaskiya tsakani da Allah Kaka zan faɗa muku akan ƴan uwana ko ɗan da na haifa a cikina zan iya rabuwa da shi, haka akan yarana zan iya rabuwa da uwarsu ma muddin ta takura musu. ta faɗa idan ba zata iya karɓar yaran ba ne to". tun fara jawabinsa na zama tamkar matacciya, da ƙyar na ke iya fidda numfashi, hawaye kuwa tsabar ruɗani da mamaki gami da baƙin ciki
🏠