haka ba bakinki zan fasa ba gidan su Siyama zan kai ki a saki a Éakin karnuka su cinye ki".
ai ko ta tsorata sosai da furucin nawa, don haka ta shiga roÆona in yi haÆuri ba zata sake ba. na juyar da ita ta fuskanci Maman Yasmin, yanda nayi maganan a tsawace yasa bakinta na rawa ta furta.
"kiyi haÆuri ba zan Æara ba"..
na Æara firgitata ina cewa,"haka ake bada haÆuri, tsuguna ki ce don Allah".
jikinta na rawa ta tsuguna gaban Maman Yasmin tana cewa,"Anty kiyi haÆuri don Allah, ba zan sake ba wallahi, ki roÆi Anty ta sakar min kunnena".
kashedi na yi mata me kyau kafin na ce ta kwashe biredin da ta zubar ta cusa haka nan taci, haka ta zauna Æasan tayels tana ci tana kuka, kuma tana gamawa na ce ta tashi a kusa da mu ta tafi Éaki ta zauna, kuma da kaina zan kaita islamiya in faÉawa Ya Ustaz abin da tayi. ai fa nan hankalinta ya daÉa tashi tai ta Æara bani haÆuri. ko da su ka shirya tafiya islamiya sai da ta zo har gabana ta duÆa ta Æara bani haÆuri kar naje islamiya na faÉawa Ya Uztaz in ba haka ba a mari zai sakata. sai da tayi min alÆawarin ta daina tukunna na ce shikenan su tafi makaranta kuma ayi karatu da yawa.
sai bayan tafiyarsu Hindatu ta ce,"cabÉijam! Sa'ida haka kike zaune da yaran nan dama? anata miki murnar samun Æ´aÆ´a ashe ke kina nan kina fama da halin su. to ke kuwa me zai hana ki mayarwa da iyayensu ki ce kin yafe".
guntun murmushi nayi na ce,"Hindatu kenan to ai bani aka bawa ba ko".
"cabÉi to sannu danga uwar haÆuri. ai wallahi da ni ce tuni labari ya daÉe da sauyawa. don wallahi tallahi ba zan Éauki Æ´aÆ´a marasa mutunci irin wannan ba sai dai in kuwa ya auro wata ta Éauka, rashin haihuwar hauka ne da za'a Éauko masifa a dire miki, wannan yarinyar dai a felle take don da gani zata yi makirci".
Maman Yasmin ta numfasa tana cewa,"sun raina wanda ya alaÆantu da ke ina ga ke kanki? Sa'ida haÆurinki yayi yawa gaskiya, na san ba akan Æ´aÆ´an kaÉai kike fuskantar Æalubale ba harda iyayensu ma, don ina da tabbacin iyayensu su ka basu lasisin cin mutuncinki, in ba haka ba ina wannan Æ´ar zata san wani juya, kar ki mu sa min domin kin san ina da ilimin karantar yanayin mutum zaman haÆuri kawai haÆurin cutar da kai. don haka ina mai ba ki shawara tun yaran nan ba su girma sun fi Æarfinki a cikin gidan nan ba ki amso abinda yake na ki, in ba haka kuwa kina ji kina gani Allah sai sun iya rabaki da mijinki. yo da irin Æ´aÆ´an nan ai gwara kishiya, su kansu Æ´an uwan na sa ki buÉe musu ido".
haka Maman Yasmin da Hindatu su ka sanya ni gaba da faÉan sanyina yay yawa, ni dai jinsu kawai na ke yi ina binsu da uhmm in sun ce ga shawara kaza da kaza, abu da na san na Éauka a cikin maganganunsu shi ne takawa yaran burki akan rashin mutuncinsu, don idan ba haka ba zasu raba ni da mutane, tun da ba kowa za su yiwa rashin kunya ba yay sha'awar Æara zuwa gidana, kuma su Éore a haka duniya ta Éora laifin akaina ace saboda ba nawa Æ´aÆ´an ba ne yasa ban basu tarbiya ba.
na samu ma da Æyar na kashe maganar, sai bayan la'asar kafin su tafi. sai dai fa Hindatu kamar za tayi bindiga saboda haushi da takaicina, wai haÆurina ya wuce Æa'ida.
washe gari da safe bayan Hubbi ya kai yaran makaranta ya dawo, mu ka yi breakfast sai dai tun dawowarsa naga kaman akwai matsala, don ba haka ya fita ba, na tambaye shi bai ce min komai ba, na ce Allah ya kyauta don bana so na takura masa da tabaya ya fusata, yana daga cikin mutanen da in ransu ya Éaci to basa so kowa yay musu magana sai sun sakko, ban kawo matsalar tsakanina da shi ba don na san babu abin da ya haÉamu, lafiya lau ya fita kai su makaranta har yana tsokana ma wai na fara tumbi.
da rana bayan ya Éauko yaran a makaranta, na zuba musu abinci suka ci, na ce musu zanje in kwanta in huta idan lokacin islamiya yayi su shirya su wuce. shigata Éaki ba daÉewa sai ga Atika ta shigo Éakin tana faÉin,"wai ki zo inji Abba".
bayanta na bi, ina shiga Éakin kamin nayi yunÆurin magana ya ce,"sako hijabinki zamu fita".
yanayin yanda yay maganar kaÉai ya shaida min bafa lafiya, na fita a Éakin kafin na sauko har sun kai mota shi da yaran, can na tarar da su ina zuwa na buÉe na shiga. magana na ke ta masa tun barowarmu gida bai ce min Æala ba, raina ya Éaci zuciyata ta Æuntata, don bana so ya ke min irin haka a gaban yaran, shiru nayi ban Æara magana ba har sanda na Éago ido naga yay parking motar a Æofar gidanmu.
nan kuma naji yana waya yana cewa,"Yashaik mun Æaraso".
ya sauke wayar a kunne yana juyawa ya kalli yaran ya ce,"ku buÉe ku fita". sai bayan sun fita nima ya ce da ni,"fita mu je".
na ce,"wai lafiya?".
"za ki gani in mun shiga daga ciki".
da tarin tambayoyi fal a raina dangane da zuwanmu gidan na fito daga motar, fitowata tayi daidai da isowar Yashaik, su ka yi musabaha nima ina cewa,"Yashaik ina wuni".
wani wawan k