har na sakko Æasa kiran lambar Hubbi nake yi bata shiga, zuwa yanzu da akai magriba hankalina ya kai Æololuwar tashi, ga dai shi ba wai dare ne yayi ba, to amma ban saba ba, tun aurenmu sau Éaya ya taÉa kaiwa bayan isha'i a waje, shima kuma dalilin hatsarin da ya samu ne, shiyasa ko yanzu nake ta jin kaman da akwai wata matsalar, sai dai ina ta kore mugun saÆe saÆen da zuciya ke min.
Mayafi na yafa na fita, mai gadi na hangoni ya taso da sauri ganin na fito a furgice, gabana ya russina yana tambayar lafiya, da Æyar na daure na haÉiye kukana nace masa.
"Tun da Hubbi ya fita bai dawo ba ne?".
Mamakin tambayar tawa ya bayyana Æarara a irin kallon da yake min, na san mamakin bai wuci ace ni da za'a tambayi fita da dawowar mijina ba amma wai ni ce ke tambayar.
Cikin girmamawa yace da ni,"Hajiya ai bai jima da fita masallaci ba, amma dai da mota ya fita inaga ba masallacin nan kusa ya tsaya ba".
Wani Æunci naji ya ziyarci zuciyata, na kawar da Éacin raina da damuwata nace,"ok". Abin da na iya faÉa kenan na wuce na bar wajen, don idan nace zanyi doguwar magana tabbas sai ta tsarÆe da kukan da nake dannewa.
Ina komawa ciki na shiga bedroom nasa na Æasa, ya daÉe da dawowa kam daga yanayin yanda Éakin ya nuna. Abin da ya bani mamaki matuÆa shi ne sabon Æamshin turaren da ban san da shi ba, turarensa Éaya na sani a duniya wanda tun kafin muyi aure da na taÉa basa kyautarsa shikenan ya riÆe shi bai taÉa canjawa ba sai a yau, kuma yanzu da nake ganin sabuwar kwalba akan madubi bayan ga waccen kwalbar bata Æare ba.
Æakin na bi da kallo, idona ya kai kan warm coolers Éin da ke Æasa guda uku, wani abu naji ya soke ni kaman sukar mashi. Æafafuna na rawa na isa gabansu da sauri na buÉe, Æamshin lafiyayyan abincin ciki ya doki hancina, babu tantama abincin wata Æwararriyar chef Éin ne. Na bar ganina daga kai ina kallon kan gadon da kayansa ke zube waÉanda ya cire, sai naji kamar ana jana zuwa bakin wadrobe, jikina duk na rawa na buÉe Éangaren da jallabiyunsa su ke, kaf guda goma sha ukun da yake da su suna nan ciki rataye a hanger babu Éaya da ya saka ya wuce masallaci kamar yanda ya saba.
Lokaci Éaya naji yawun bakina ya bushe gaba Éaya, cikin rasa makamar abin yi na rarumi wayata na shiga kiran lambarsa, farko not available su ka ce min, na biyo kuma ringing Éin bai je ko'ina ba aka danna user busy, na kalli agogo naga lokacin sallar isha'i ya wuce, hakan yasa na Æara danna kiran, amma har sau huÉu abu guda ake faÉa min user busy ni kuma Æara kiran nake yi.
Zuciya da bata da Æashi tuni ta fara Æissima min tunanin wasu lamura, har tana haska min hoton hakan a cikin idanuwana, babu shiri na rumtse ido gam ina girgiza kaina, ban san lokaci da na sami mazauni a gefen gadon ba ina damÆe zanin gado, wani abu ya soki Æirjina, cikin raina faÉi nake ina Æara maimaitawa ba yanda za'ai Hubbi yayi min abin da zuciyata ke rayawa, ko da komai ya canja shi ba zai taÉa sauyawa daga mutumin kirki ba, nagartaccen namiji mai wuyar samu, ba Éan kuka na aura ba, duk tsanani Hubbi ba zai taÉa juya min baya ba, ba zai taÉa cin zarafina ta irin wannan hanyar ba, matsayin da nake da shi a zuciyarsa ya wuci gaban yaci mutuncina ta irin haka, yana tsanin sona na sani, kowa kuma shaida ne.
Kaman daga sama na jiyo ana kwaÉa sallama a parlo, na miÆe da sauri ina saita natsuwata na fita da sassarfa, da zumuÉin da na fita inci karo da Hubbi nah a asalin Hubbin da mu kayi aure cike da so da Æauna gami da kwanciyar hankali a zamanmu na baya.
Sai dai me! Ina isa falo gabana ya faÉi ras sakamakon tozalin da nayi, duk sai na daburce ina neman rasa ina zanyi kuma mai ya kamata inyi. Yayar Hubbi ce ta zo Maijidda wadda muke cewa Yaya, daga Æanne har Æ´aÆ´a da Æ´an uwa kowa Yaya yake ce mata, ita ce babbar su wadda ta zamar musu tamkar uwa, kowa na sonta haka kuma kowa na tsoronta, sai abin da tace ayi haka kuma idan ta faÉa ta zauna, ko mahaifiyarsu bata fiya yanke hukunci ba sai dai ta bata wuÆa da nama, haka duk abin da za'a yi sai da shawararta, ba'a taÉa yin abu ba tare da masaniyarta ba, ana girmamata sosai da mata biyayya, kuma itama tana mutunta kowa, ba zan ce bata da kirki ba idan na faÉi haka na zalunceta, macece mai Æaunar nata, duk abin da ta tattaro na ahalinta ne, burinta taga kowa cikin farin ciki, haka kuma kowa ya tashi kai kukansa ita yake kaiwa, kowa Yaya komai Yaya, sai dai tana da zafi, bata Éaukar raini, idan ta tashi faÉanta da masifarta shafar kowa yake yi, shisa kowa ke kiyaye abin da zai haÉosa da ita.
Kaf cikin matan Æannenta tafi sona babu ya ni a wurinta, ba wai don su Éin bata son su ba, a'a nima albarkacin tsananin soyayyar da take ma Hubbi ne yasa na zama ta gaban goshinta, yanda take nan nan da ni kamar Æ´arta Shatu wacce mubke sa'anni, amma duk wannan tarin soyayyar tata da kulawarta gar