nkuÉe hannun Hindatu a jikinta tana cewa,"Ni ki Æyale ni". tana fuzgar numfashi ta ce,"kuma in Abba ya dawo sai na faÉa masa an hana ni abinci".
ai ko na dalla mata harara na ce,"kar ki fasa faÉa masa kinji mara kunya fitsararriya, yanzu ma ki bisa can ki faÉa masa".
yarinyar nan da ke ta ÆwanÆware a rashin kunya cikin ÆunÆuni sai ce tayi,"ni ba fitsararriya ba ce, abincin naga ai Abbanmu ya siyo, dama an ce juya bata san darajar Æ´aÆ´a ba, kuma tun da kike azabtar da mu da yunwa ba za ki taÉa haihuwa ba".
Ai karaf magar a kunnen Maman Yasmin. ta buÉe baki tana kallonta da matuÆar mamakin furucin nata, kafin tayi mata wata muguwar cafka ta fizgota gabanta. "kika ce me? ba ki da kunya dama? don ubanki ita ba Babarki ba ce".
"ni ba Babata ba ce, Mai gidan ne Abbana".
Abin ya matuÆar Éaure kan Maman Yasmin naga ta ware ido tana kallonta ta ce,"kaiiii haka kike?". ta faÉa da al'ajabi da mamaki.
ban san me tace ba kuma bana da buÆatar na sani, iya wannan Éacin ran ma ya isa. saboda haka na shiga roÆon Maman Yasmin akan ta Æyaleta kawai, abincin ne dai ba zan Æara dafa mata wani ba ko me zata yi kuwa.
"in Æyaleta fa kika ce Sa'ida, kin kuwa ji furucin da tayi? ta ya za'ai yarinya kamar wannan ta faÉi haka kuma a Æyaleta babu hukunci, maganarta ai ta girmi shekarunta, ai na ma ta san wani kalmar juya don ubanta, ke haka kike barinsu babu kwaÉa babu tsawatarwa kenan?, to in har kuwa haka ne ba ruÆon tsakani da Alllah kike musu ba domin ba ta isa tayi gaban uwar da ta haifeta ba ta Æyaleta, ai gaba ake ji".
nayi gajeran murmushi jin furucin nata, cikin sanyi murya na ce,"Æyaleta Maman Yasmin, Allah ya shirya mana kawai, ai ina musu adu'a".
kawai sai ta tsaya kallona, ban san me take tunani ba tun da ban san zuciyarta ba. kawai na san zata iya tunanin mene dalilina na cewa a barta alhalin tayi ba daidai ba. Maman Yasmin kuwa tausayin Sa'ida ne ya kamata, tana Éaya daga cikin mutanen da zasu bada shaidar haÆurin Sa'ida, kuma tayo gado ne wurin iyayenta. tun farkon zuwanta sabon gidan nan nasu ta fahimci rayuwar haÆurin da take yi, haka ko da aka ce mata an bata yara ta san kuma sai ta Allah, don riÆe Æ´aÆ´an da aka ce ba naka ba sai haÆuri, to naka din ma ya aka cika, ballanta ita an bata yara masu uwa a bakin murhu.
ai tana lure da Sa'idan tun da ta ruÆo hannun yarinyar taga tsoro ya bayyana akan Fuskarta, hakan kaÉai ya isa ya bata shaidar ba a tsawatar musu domin yi musu Éin ita zai jawowa shiga matsala.
ta girgiza kanta kawai cikin ranta tana faÉin Allah ya kyauta, sannan ta saki hannun Atikar, cikin muryar kashedi ta ce mata.
"ke! kar na Æara jin kinyi irin wannan furucin a bakinki idan ba haka ba sai nasa Antyn na ki ta zane miki jiki, idan kuma son da take miki ba zai sa ta dake ki ba ni da kaina zan miki duka. kuma daga yau duk abin da Antynki ta ce ki dinÆa yi ban da musu kinji ko, ko ba kiga yanda Æ´ar uwarki take yi ba? duk wanda fa yake wa babarsa rashin kunya Allah fushi ya ke da shi".
yarinyar ta yamutsa fuska tana tsuketa, ta turo baki tana harar gefe guda ta ce da Maman Yasmin.
"ke kika haife ni da za ki dinÆa min faÉa, ai ko Anty Abbanmu ya hana ta yi mana faÉa sai ke baÆuwa, ina ruwanki, kuma sai na Æara faÉa Éin ki kashe ni kiga in Mamana zata Æyale ki".
farrr na ware idanuwana akan fuskarta, ban tsammaci rashin kunyar Atika ya kai har haka ba, na san har iyayensu ba su bari ba shiyasa idan suka min ban cika damuwa ba, amma ban tsammaci har za su iya yiwa baÆona ba. karo na farko da naji raina yay matuÆar Éaci akansu, aiko na buÉe murya na daka mata tsawa har sai da tsorata, na tashi na isa gabanta na bata kyakykyawan mari, sannan nasa hannu na bibbige bakin nata yanda zata ji a jikinta. ji nayi hakan bai min ba saboda na kai Æololuwa a Éacin rai, na manta me zai iya faruwa sanadin hukuncin da zan mata, na shiryawa fuskantar ko menene, don haka na riÆe hannunta na isa gaban tv na cire caja na tsula mata a jiki sau biyar, sai kokawar Æwace hannunta ta ke daga ruÆon da na mata saboda ta falla ta gudu.
tana shashsheÆar kukan ta murguÉa min baki wato abin da na mata bai shigeta ba, kuma bata risina ba. na kuwa kama kunnenta na murÉe da kyau har sai da ta Æwalla Æara, na kuma daka mata tsawa na ce ta rufe min baki, idanuwana waje na zare mata su na shiga mata gargaÉi.
"Duk sanda kika kuma yiwa babba rashin kunya sai na zane miki jiki wallahi, ko a waje balle a cikin gida, haka na koya muku ko haka Abbanki ya ce kuke yi?".
ta tsorata da yanayina sosai da ban taÉa nuna musu ba, jikinta rawa kawai yake tana sosa dukan da na mata.
"kalleta ki bata haÆuri dan gidanku, ni za ku iya min komai in Æyale ku na biku da adu'a amma ba zan lamunci in ga kuna yiwa babba rashin kunya ba Atika, zan aje duk son da na ke muku a gefe in hukuntaku. kuma wallah kika Æara irin