NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 48 of 97

ncan zuwan da nayi na ƙarshe babu wata tarba mai kyau daga uwar mijina, jin haushina tsantsa bayyane a saman fuskarta, don ko da na gaida ita da ƙyar ta amsa mini, sona kam dai yanzu ba shi a tare da ita. zama da nayi a ɗakinta ma sai ce tayi da in fita daga parlo ko wajen Amarya tana so zata huta. haka na kwaso jiki na fito parlo in da anan na sami ƴan mata gidan suna kallo ana hira, Rumana da Atika na ganina amma yaran nan babu wacce ta gaida ni kamar ma ba su sanni ba, Atika ma da nayi mata magana sai tsaki ta min tayi wucewarta ɗakin Iyam, abin ya taɓa zuciyata sai naji ina ma kar su koma gidan namu don gani nake komawarsu zai ƙara taɓarɓara zamana da Hubbi. yini muka yi a gidan, da Amarya muka ta hira duk ta ɗebe min kewa, dama ita Ummaa ba wani sakin fuska take ba, Lubabatu kuwa dama ta gidana ce, in muna tare sai ka ce Hassana da Hussaina, na samu na saki jiki daga takurewar da nayi, don duk na damu da rashin nuna halin ko in kula na uwar mijina, ban san me na mata ba na kuma rasa ta hanyar da zan bi na gyara alaƙarmu. sai dare ya zo ɗaukarmu da yaran, kuma tun a mota yay musu faɗa sosai, faɗa irin na uba da ƴaƴansa, yace in har suna so su shirya da shi to su girmama ni kamar yanda za su girmama Yaya da Anty Aisha, don yanzu ni ce matsayin uwa a gare su kamar yanda shima ya koma uba a garesu. to tun daga wannan ranar kam sai dai in ce Alhamdulillah. sati biyu tsakani ina zaune a parlo muna waya da Hubbi, sai ga su Maman Yasmin sun zo, nayi tsallen murna na tafi na rungume su, naji daɗin ganin su sosai, yau dai Hindatu ta wanke laifinta na rashin zuwar min da take yi, a hakan ma ashe da ƙyar Babanmu ya barsu su ka zo, wai yana tambayar me za su je suyi min a gida bayan ba jimawa na zo gidan suka ganni. tare da Hindatu da Sauda mu ka shiga kitchen, dama ban ɗora abinci ba da yake Hubbi ya tafi Kaduna yau, kuma sai dare zai dawo, shiyasa ban wani ɗora girki ba na ce idan yaran sun dawo a makaranta na dafa mana indomie. gidanmu mayun taliyar hausa ne da manja da yaji, ko a gida idan za'a dafata haka mu ke haɗuwa da ƴan ɓangarenmu da Ƴaƴan Babanmu, dama Ƴaƴan Baba Tijjani tsakaninmu da su kallo, gwara ma Surayya ta kan shigo cikinmu bata da mugun hali irin na ƴan uwanta. taliyar na bayar aka siyo mana muka dafa tun da naji suna murna a dafa ɗin, Sauda ta haɗa mana lemun tsamiya don Maman Yasmin mayyarsa ce. muna cikin cin abinci sai ga Rumana sun dawo daga makaranta, ba don mun haɗa ido da su ba ba za su gaida ƴan uwana ba, gaisuwa na ɗaya daga abin da basa so, don ko ni da muke kwana tare mu tashi tare ba kullum su ke gaishe ni ba sai dai Abban na su, nayi iyakar yina akan su ɗoru akan hanyar hakan amma lamarin na su sai adu'a. na ce suje su cire kayansu suyi wanka su zo su ci abinci kafin lokacin islamiya yayi, Yasmin sarkin son yara ƴan uwanta nan fa daɗi ya cikata da ganinsu, duk da sun girmeta don ita shekara bakwai take yanzu. muna ta hirar saurayin Hindatu da zai kawo kuɗi Maman Yasmin na mata tsiya akansa, sai ga su sun sakko, idan na gansu fes fes raina yana sanyi da hakan, sai in ƙara jin sonsu sosai, don wallahi ko fushi na ke yi na gansu ɓacin raina kan gushe duk da dai ga yanda mu ke da su, ba su ɗauke ni uwa ba kamar yanda ni na ɗauke su tamkar ƴaƴan cikina. Rumana ta zo ta zauna kusa da ni tana faɗin,"Anty abinci fa". kafin nayi magana Atika ta ce,"Anty wai wannan taliyar hausar aka dafa?". ta faɗa tana nuna taliyar da ke cikin bowl Maman Yasmin na bawa Irfan. na ce mata,"ehh ita na dafa har ma da salad, in kika ci kunnenki sai ya kusa tsinkewa". na faɗi hakan ina buɗe cooler sai ce tayi. "ni ba zan ci wannan taliyar ba gaskiya". ina kallonta na ce,"to me kike son ci?". "a dafa mana wani abun, soyayyan biredi da ƙwai zan ci". ajiyar zuciya na sauke, bana tunanin ko ɗan da na haifa zai juyani kamar yanda su ke juyani, ina binsu ne a yanda suke so ba don komai ba sai don in zauna lafiya a gidan aurena. Rumana da tace zata ci na zuba mata nata suka koma gefe ita da Yasmin wacca ta ce zata ƙara. ita kuma na tashi na shiga kitchen na soyo mata biredin na kawo mata, yarinyar nan tun da na bata ta karɓa sai ta tsaya kallonsa tana aikin ɓata rai alamun bai yi mata ba. raina ya ɓaci na ɗaga mata murya da cewa,"ba za ki wuce kije kici ba sai anjima ki zo kina min kukan yunwa. idan shima kuma ba za ki ci ba sai ki kai ki ajiye don ba zan kuma dafa miki wani abun ba ai na faɗa miki ku dinƙa cin abin da ya samu". daga mata wannan maganar sai ta saka kuka kamar wacca nasa hannu na buga. nayi mata banza na wuce na barta, Maman Yasmin na kiranta akan ta zo amma ko kallonta bata yi ba, Hindatu kuwa lallashin duniya ba wanda bata mata ba har tana tambayarta me take so amma bata tanka ba, dama zuciyar bala'i ce da ita. ƙarshe kawai sai ta yar da plate ɗin, da yake na tangaran ne take ya fashe, ta tu
🏠