a yau tun daren farko na, shi kansa ba Æaramin gigicewa yay ba da yanda yaji ni tamkar sabuwa a leda.
yana ta aikin sauke nauyayyan numfashi ya ke min godiya da sa albarka, wannan kam lazim ne duk lokacin da ya samu natsuwa tare da ni.
can kuma ya fara surutan,"Habibty ba ki canja ba, kina nan da daÉinki sai ma Æara daÉin da kika yi, kinsa naji daÉin da na jima banji ba, ina sonki Habibty, ina sonki, Allah yasa da rabon samun zuri'a mukawa".
hawaye ya fara zubo min, ba komai yasa ba sai tuna baya, lokacin da muke zaman lafiya cikin tsantsar so da Æaunar juna, lokacin da ko Éaga murya ba ya yi min, in laifin nayi kuwa cikin kwantar da murya zai min faÉan ya kuma gyara min kuskurena.
sai da cikakkiyar natsuwa ta tabbatarwa kowannenmu kafin muka yi wanka kana muka dawo muka kwanta. lafe na ke kawai a saman Æirjinsa idanuwana a lumshe, baccin na ke so nayi amma yaÆi zuwa, ba zan taÉa iya musalta daÉi da farin cikin da na ke ji ba a cikin a raina sai dai sam na gaza bayyana hakan a saman fuskata da yanayina. shima shiru yay yana shafa gashin kaina, da Éaya hannun kuma yana shafa fuskata da tattausan leÉe na, a hankali ya hura min iska a kunne yana Æara rungumeni jikinsa, muryarsa kwance cikin taushi ya kira sunana.
"Habibty". na amsa da,"ummm Hubbi".
"ba ki haÆura ba har yanzu? ba ki bar fushin da ni ba?".
"na daina mana Hubbi".
"to amma ai ni kin Æi nuna min, yanayinki sam babu hakan, ki saki jikinki plss ba Nazifin da ya canja miki ba ne cikin wasu Æ´an watanni, wannan Hubbinki ne tun na aure. na sani na saki Éacin rai har adadin hakan ba zai Æirgu ba, amma kiyi haÆuri da duka kuskurena, ki yarda da ni kinji, mu komawa rayuwarmu ta baya, rayuwar ma'aurata mai cike da tsantsar so da Æaunar juna, kwanciyar hankali da shimfiÉadden zaman lafiya".
ni dai nayi masa shiru kawai, domin mamaki ne da rashin yarda a raina, gani na ke kawai saboda wata manufa ya ke son sasanta komai, don har yanzu babu ainihin muryar Hubbi a dukka kalamansa da yayi, kuma har yanzu babu wannan haÆiÆanin son da yake nuna min idan muna tare.
"Habibty ni dai na san dukka abubuwan da na ke yi miki wanda basu dacewa, kuma nayi alÆawarin gyara su, to amma kema ina so ki faÉa min me kike so na gyara?".
hawaye ya cika idona na ce,"Hubbi ni so na ke ka dawo mai kulawa da ni da tausaya ni, kuma ka ke min adalci wurin tsayawa ka fahimce ni a duk san da saÉani ya gifta, sannan ka bani damar zama uwa mahaifiya wacce ta tsuguna ta nayi naÆuda bayan Éaukar cikin wata tara akan Rumana da Atika, ba zan cutar da su ba kamar yanda ba zan so in ga sun halaka ba, in suka yi ba daidai ba akwai buÆatar a gyara musu, don haka kar ka tsammaci gyara tarbiyarsu wurin tsawatar musu da zan yi yana nufin bana Æaunarsu. wallahi ina Æaunar su Hubbi tun da aka ce an baka su, kaima ka sani ina tsananin sonka, da kai na ke so na Æarasa rayuwata, don Allah kar ka kuma goranta min akan Æ´aÆ´an nan, sannan don Allah da Annabinsa Hubbi ka faÉa min sakamakon da asibiti su ka bayar...".
kuka yaci Æarfina nayi shiru, da sauri ya Éora haÉarsa saman kaina yana Æara rungume ni, shiru na Æ´an sakanni ya ce.
"insha Allah ba zan kuma yanke hukunci ba tare da na tsaya na saurareki ba, kuma insha Allah ba zan Æara nuna miki cewa su Rumana ba Æ´aÆ´anki ba ne, na ba ki izini daga yau kiyi musu duk yanda kike ganin za kiwa yaron da kika haifa da cikinki, na damÆa dukkanin tarbiyarsu a hannunki domin ina da tabbacin za ki fini iyawa, abu Éaya kawai zan fiki akansu shi ne so, kuma ke za ki zama shaida akan yanda na ke so yara. batun kuma gwajinki sakamako ya nuna lafiya lau kike ba ki da wata matsala lokacin haihuwar ne kawai bai yi ba, ni da ke duk lafiya muke Allahne bai bai kawo mana ba".
a Æalla naji sanyi cikin raina, amma ban san me yasa na kasa gamsuwa da shi da zancensa ba, haka hankalina yaÆi kwanciya gaba Éaya, sai dai naji daÉi sosai da batun cewa mahaifata lafiya Æalau take. a hakan dai sai da ya san yanda yay yasa na saki jikina Éari bisa Éari da shi kafin muyi bacci.
sai da na kwana biyar da dawowa sannan ya ce in shirya muje gidansu, a kwanakin har wani murmurewa nayi saboda samun natsuwar zuciya da ta ruhi, tsakanina da shi ba wani rikici ko saÉani hankalin kowa kwance, duk da akwai canjin dai da ya kasa gyaruwa, ban sani ba ne ko shikenan har abada ba zamu taÉa komawa yanda mu ke da shi ada ba, wani lokacin zai ta nurÆufanci yana shareni amma ba zai Éauki lokaci mai tsayi ba ya sakko, sai dai fa yanzun kam na gama karantar shi shima duk yana min abin da yake min ne saboda ina da tawaya ta wajen haihuwa, dukkan fatansa da burinsa bai wuci ace ya samu Éa ba ta jininsa, na yi yunÆurin zama da shi da dama akan mu shawarta ko aure zai yi amma na kasa, idan nayi yunÆurin haka sai zuciyata ta karye.
sai da ya fita wurin aiki ya dawo sannan muka tafi gidansu, sai dai kamar wa