NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 46 of 97

numfashin mutum a jikina, nayi saurin buɗe ido zan miƙe ya janyoni jikinsa ya rungume. "kiyi haƙuri da abin da ya faru, ɓacin rai ne. kuma kin san ina da son yara sosai ba zan jure ganin wani abun ya samesu ba, hakan shine ya tashi hankalina har ya kai ga abin da na aikata miki. Amma kiyi haƙuri ba za'a sake ba in sha Allah". hawaye na fara tunawa da irin horon yunwar da yayi min da kalamai marasa daɗin da ya faɗa min, to ni in laifukansa gare ni ma ai sunyi yawan da ba za su ƙirgu ba, ga laifin su Yaya amma a haka ya sallame ni zuwa gida ba tare da yi min uzuri ba. jin hawayena na jiƙa jikinsa sai ya ƙara rungume ni sosai yana faɗin,"na san nayi laifi babba kiyi haƙuri ki yafe min Habibty don Allah." Allah sarki zuciya da abin da take so, hakana tsakanin mata da miji sai Allah, roƙona da yake tayi domin Allah sai naji na nemi laifinsa gare ni na rasa. na kewaye shi nima ina cewa,"Ya wuce Hubbi. Amma dan Allah ko dan gaba ka dinƙa tsayawa ka fahimce ni kafin ɗaukar mataki....". ya dakatar da ni,"shiii hakan ma ba zai sake faruwa ba fa, duk wani saɓani a tsakaninmu ya zo ƙarshe". haka muka jima rungume muna jin ɗumin jikin juna da bugun zuciyoyinmu, kafin ya ɗago kaina ya kalli idona ya ce,"Habibty kina jina?." na ɗaga kai alamun eh yace,"nayi kewarki sosai ba kaɗan ba". a sanyaye na ce,"Nima nayi kewarka Hubbi." na faɗa muryata na neman karyewa. Yayi murmushi yana ta kallona yace,"Habibty na tambaye ki?." Na ɗaga kai alamun eh yace,"Akwai wani abu wanda aka ba ki kina sha ne na gyara jikinki..? Ina nufin na gyaranku na mata." Kallonsa nake yi ban ce komai ba hakan ya saka yace,"in akwai ki daina sha ya canja min ke gabaɗaya, bana jin ki kamar da. ba gyara yake miki ba ɓatawa yake." ido na sunkuyar ƙasa, lallai namiji, wato sai yanzu lokacin faɗa min gyarana yayi, a yanzu da zanyi amfani kenan. "Habibty kin jini ba ke ci komai ba". Na ce,"to Allah ya gyara amma ni dai babu wani abu da na ke sha, asalin ɗanɗano na daka sani shi ne dai ban sha abin da zai ƙara min ba balle har ta kai ga ya rage min, amma karka damu zan koma mai daɗin da kake so". nayi furucin domin na daina ƙullewar kai, na cire kaina a sahun matan da ke jin kunyar mazajensu ta fannin soyayya. Yayi murmushi yaja kumatuna yace,"yauwa Habibty nah". zameni yay a jikinsa yana cewa,"bara na rufo ƙofan falo". ya faɗa yana ficewa na bishi da kallo. Yana fita nayi saurin ɗauko maganin da Maman Yasmin ta bani na fara sha nan take sai da na shanye haɗin zumar tasss, harda goro ma da akace naci rabi amma haka na cinye guda. na leƙa falon naga baya nan nayi sauri na shiga kitchen na buɗe fridge na ɗauki ruwan rake da ke cikin jarka na zuba garin maganin, na kafa kai shima na shanye sannan na tsaya sauke numfashi ina zare ido don duk ƙarfin hali nayi wajen shan su. ni tun aurena ban san shan wani abu maganin mata ba, ko lokacin aurena in aka bani bana sha, saboda gab da aurenmu da kansa ya ce don Allah kar in sha komai na gyara da za'a bani, in ke ba shi yana ajiyewa akwai dalilinsa na faɗin hakan. to kuma bayan auren sai ya ce dama yana so ya ɗanɗani asalin zaƙin halittata yaji, to kuma iya wannan daɗin ma ya ishe shi ba sai na ƙara da komai ba, kar in zo ina sha in canja daɗi kuma, saboda haka duk ya tattaro wanda ya ajiye da wanda nima na ajiye muka zubar. to yanzu tun da anzo lokacin da asalin halittar tawa ya bar masa daɗi ai sai in kama kaina inyi abin da ya dace ba in zauna da sakakkun laɓɓa ba. har zan fita a kitchen ɗin idona ya kai kan fruit na ɗauka nasha nasha na bar na bari, don bana taɓa mance wata likita da ta faɗa min cewa babu mafi muhimmanci a gyaran jikin mace irin shan kayan marmari, kuma sosai da na lazumci shansu na ga sakamako mai kyau. ni ko a yanzu ma ban wani yarda da dalilinsa ba, kawai dai ya faɗa ne don kare kai ya kuma wanke laifinsa. ina shiga na tarar bai dawo ɗakin ba, don haka na shiga tuɓe kayana na ɗauki towel na ɗaura. lokacin ne kuma ya shigo sanye da kayan bacci masu taushi yana ta ƙamshinsa me daɗi. muka haɗa ido da shi na wuce ina zuba kayan da na cire cikin basket. zan wuce shi ya ruƙoni yana faɗin,"ina baccin?". da muryar shagwaɓa nace masa,"na kasa, wanka na ke so nayi tukunna". na ƙwace hannuna nayi toilet ɗin sai dai ina zuwa bakin ƙofar sai na dakata na waigo na kalle shi na ce,"Hubbi kai ba zaka yi ba?". "daga wanka na fito ai". na narke idanu ina langwaɓar da kai na ce,"to ka zo kayi min, ni duk na gaji". murmushi yay wanda na rabon da naga irinsa a fuskarsa zan rantse an shekara. ya cire rigar jikinsa ya naɗe wandon ya kama hannuna muka shiga banɗakin. Tare mu kayi wankan da shi, kuma tun a banɗakin labari ya fara canjawa, ko da muka fito tuni na kasa daurewa salonsa, ni dai sai in ce rabon da mu mu'amalantu irin t
🏠