NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 97

sha biyar sai gata a ɗakin nawa tana faɗin,"ke lafiyarki? ai ce na ke ma kun wuce". kamar zan yi kuka na ce,"zan tafi ne Ummani". "wanne irin za ki tafi ne, shi mijin naki zaman jiranki zai tayi". na mayar da ƙwallar idona na ce,"ai ya jima da tafiya. maƙullin gidan ya kawo min ne". kuma ina rufe baki sai ga sallamar yaro yana cewa,"wai Sa'ida ta fito inji mijinta su tafi". Ummani ta ce da shi,"kace gata nan". sai ta dawo kaina da faɗa sosai. "ke bana son sakarcin banza, kwashi kayanki ki fita ki bi mijinki kar in saɓa miki. in kin fi ƙarfina kuma ai Yashaik na gida sai in aika a kirawo shi wallahi". tashi nayi babu shiri, na fara fitar da kaya bakin ƙofar ɗakin, Sauda ta fitar min da su ƙofar gida. "waccan ledojin ba naki ba ne, kar dai ki manta wani abun". na waiga ina kallon ledar da ta min nuni. na ƙarasa na ɗauka ina buɗewa, magungunan mata ne da ƴan uwa suka bani a ƙauye, wai in amfani da su kafin na koma gidana. a lokacin girgiza kai kawai nayi, basu san tuntuni mu'amalar aure ta daina shiga tsakanina da mijina ba, jo hannun juna bamu riƙewa, shiyasa bana wani tayar da hankalina akan gyara kaina dan bana son abin da zai jawo min matsala. sai kuma ɗayar ledar da Maman Yasmin ta bani, itama ciki kayan gyara ne masu inganci don ita dama ba daga nan ba, yawancin daga nijar ake yo mata haɗin gyaran jiki ciki da waje, shiyasa duk ta susutar da Yashaik. na fito na leƙa muka yi sallama da mutanen gidan, Ummani dai tuni ta ɗau fushi da ni don ko da na zo ina zan tafi a daƙile ta ce min ki gaida gida. na samu na lallaɓa uwata ta saki ranta, ta ƙara min faɗa da nasiha ta ban shawarwari da zan fara aiki da su tun a yau, haka na barota ina mai cike da kewarta don sam bana son tafiyar. ni dai tun da na shiga mota wurin da yake ban kalla ba. motar ta ɗauki shiru sai can naji ya kamo hannuna. "wai Habibty daina magana tayi ko kuma Hubby ta daina kulawa?". ya furta hakan cikin taushi yana kallona. Ban ce komai ba ya sake cewa,"Ashe za ki iya kwana har bakwai ba tare da kinji ko da muryarta ba balle ki so ganina Habibty, ni fa kin ganni murna na ke tayi da ganinki na kasa riƙe shauƙina, amma ke ba alamar jin daɗi tare da ke". Kallonsa nayi shima ya waigo, muka haɗa ido ya mayar da hankalinsa kan titi. "ummm Habibty kwana fa bakwai banji motsinki ba, kin san Allah gidan kamar bursun". nayi shiru ban ce komai ba amma har raina wani daɗi na ke ji, duk da ban gama yarda da shi ba. A sanyaye ya sake cewa,"ba kiyi kewa ta ba ne?". Nan ma ban amsa ba sai ya matsa hannuna yace,"Habibty fushin ya isa haka kar mu ƙarasa gida a haka, Na san nayi laifi a yafe min". ya furta cikin muryarsa mai daɗi da kwantar da kai. Nan ɗin ma shiru na masa don ni sam bana ganin zan iya tanka masa. amma haka ya ke ta zuba bakinsa ko gajiya bai yi, muryarsa a ƙasa ya ƙara cewa,"ba za ki min magana ba ko? ai shikenan zan saka kiyi magana ne bara mu koma gida, ni ban san ma Ya Hayaty haka ta iya fushi ba sai yau, to Allah ya huci zuciyarta". ɗago ido nayi na kallesa. wai Ya Hayaty, rabon da inji wannan sunan a bakinsa har na manta. kuma kawai sai na tsinci kaina da yin murmushi me sauti kuma mai kaifi, shima sai ya murmusa daga haka kuma kawai na ɗan sakko, wata maganar in amsa masa wata nayi masa shiru. zuwanmu junction ɗin gadon ƙaya muka tarar da anyi accident. police sun cika wurin don motarsu ce guda ta zo, suna ta fama da matashin saurayin yaƙi barin naushin me adaidatar da ya dakar masa mota, Hubbi ya ke cewa ai ya san lambar motar yaron, a banza ma in ƴan sanda in sun tafi da shi don ba zai rabin awa ba a station zai fito, to yana cikin maganar ma muka ga wata farar mota ta faka in da na ciki ya fito, fuskarsa cikin facemask da p-cap, ya kama hannun saurayin da ya gagari kowa ya shigar da shi motarsa yaja suka tafi, sannan ne hanya ta buɗe aka sami sauƙin go slow. komawarmu gida Hubbi da kansa ya ɗebar min kayana zuwa ciki, daman mun tsaya a hanya ya siyo abinci don yana min ƙorafin yana jin yunwa ni ko nace ka nemi abinci don banga zan iya girki ba, kuma abin tausayi a lokacin sai ya amsa min to, da har zance ya bari zan girka in mun koma ɗin sai kawai sai na ƙyale shi. bamu jima da dawowa ba ya ƙara fita sakamon kiran gaggawar da Malam yay masa, sai bayan isha'i ya dawo, lokacin ma ni har ina shirin in kwanta tun da nayi wanka ne, da abinci ya zo daga gida ba yanda bai da ni ba akan na ci na ce masa a'a, na tashi na barshi na koma ɗakina na ƙasa. ina kwance cikin tunani kiransa ya shigo wayata, na ɗaga nayi shiru, shi kuma ya ce,"ba ki gama abin da kike ba ne?". "ba abin da nake yi ai, na kwanta ne". yay muryar tausayi da cewa,"Habibty ni ɗaya za ki bari na kwana? plss ki taso ki zo ina so na nemi afuwarki". kaman a gabansa na turo baki na ce,"komai ya wuce a wurina sai da safe". cikin baccina naji ana shafa fuskata ga
🏠