n yayi wanda yake Éauke da hotonsa da nata, hoton tun na Éaurin aurensu ne, kuma agogon Yaya ce ta basu gudunmawarsa. Æarfe huÉu da rabi na yamma, ya sauke numfashi ya rumtse ido gam tare da riÆe kansa, anya yau zai iya kwana shi Éaya a gidan nan? anya zai iya kwana a koma ina ne babu motsin Sa'ida?
miÆewa yay tamkar wanda aka tsikara yana isa gaban TV ya kashe, sannan ya dawo ya Éauki maÆullan mota ya fita ba tare da tunanin ina za shi ba, shi dai kawai zai fita Éin ne don neman mafitar da zuciyarsa ta bashi.
********
na fito daga wanka na saka kaya, ina tsaye na kasa fita sai saÆa da warwara na ke yi, Sauda ta shigo Éakin tana cewa,"wai ba ki shirya ba? kin san fa yacca abin hawa yake ga shi har biyar da rabi saura, kar muna bakin titi su Abbaa su dawo mu sha faÉa, naga kamar ma ba ki son tafiyar".
ba tare da ta lura ba na share hawayena, a sanyaye ina murmushin dole nace mata,"ke kin raina gida ne, ni in da za'a barni ma ai shekara zanyi".
tana dariya ta ce,"cabÉi abinda ba zai yiwu ba kenan. bara na Éauko mayafina". ta faÉa tana juyawa ta fita.
daga tsakar gida na jiyo hayaniyar su Walida, ko me su ke wa murna oho ina dai jiyo su sama sama da Ummani. gyalena na Éauko na yafa daidai kuma da Éaga labulen Éakin da Ummani tayi tana shigowa ciki.
"kin gama shirin?".
"ehh na gama, a samo almajirai su fitar min da su kin san waÉancan marasa kunyar ba taya ni za su yi ba". ina nufin su Asad da Khaleel Æ´aÆ´an wurin Baba Tijjani.
tana ta kallona ta ce,"sai kuma ga mijinki ya zo Éaukar ki".
Da mamaki na kalleta nace,"Mijin wa?."
ta ce,"mijinki mana, ga shi can a waje yana jiranki. ya jido kayan zaÆi ya bawa yara har da kuÉi, Walida dai ta ce cewa yay ta zo ta kamo hannunki ta kai ki zai bar mata motarsa".
da wani mamakin Æarara a fuskata na sake cewa,"Wai da gaske Ummani?".
"A'a da wasa. Malama je ki dawo ki kwashi kayanki ki wuce ki tafi gidanki lada ya isa".
"Ummani yaran nan Æarya su ke yi fa, a halin nan dai Nazifi bai zuwa gidan nan balle har ya ce Éaukana ya zo yi".
"to ai sai kije ki duba idan ba shi Éin ba ne shikenan, idan shi ne kuma sai kiyi murna".
ta faÉa tana fita. ta barni da bin ta da kallo zuciyata na harbawa cike da mamaki gami da tsoron zuwansa.
mayafin na mayar na Éauki Hijabi na saka na fita jiki a mace. Yana zaune cikin mota ya hango fitowarta, ya sauke numfashi ji yake kamar an cike masa wani gurbin da ya jima da yin rami a cikin zuciyarsa, a hankali yake ganin takunta zuciyarsa na motsawa, sam ya kasa Éauke ido daga kanta domin kuwa gani yayi kamar an canja ta, kwana nawa dudu bai ganta ba amma har ta isa Æara yin kyau da cika haka?, wato ita hankalinta kwance yake ma, shi yana can rashinta a gidan da matsalar da yake ciki sun hana shi sakat.
ko da isa gaban motar sai na tsaya, ina iya jin kallonsa a jikina, fuskar nan tawa naci kunu ina kalle kallen gefe abuna sai Æifta idanu na ke, yay horn wanda ya ke shaida min na in shigo motar amma sai nayi biris. sai ga shi ya fito da kansa ya taho har inda na ke, yay tsaye gabana hannayensa naÉe a Æirji.
na Éan ja da baya ina ce wa,"salamu alaikum".
sautin murmushinsa na ji kana ya ce,"yi haÆuri Ya Sayyada, amsawar sallama ne dole ba yinta ba".
na ce,"haka ne. Abbaan ba ya nan bai dawo daga kasuwa ba. amma Yashaik yana gidansa, in kuma kana iya jiran dawowar mahaifin nawa to tabarma ce da mu".
ina faÉin haka na juya zan koma gida ya ruÆo hannuna.
"wurinki na zo ba wurin Abbaa ko Yashaik ba".
nayi shiru ban ce komai ba. ya faki idon mutane yasa hannu ya Éago fuskata, na kulle ido ina kauda kai gefe.
cikin dakiyata na ce,"wacece ni da na isa ka zo wurina?".
"matata".
nayi guntun murmushi na takaici ina cewa,"ina wuni". na furta a sanyaye ba tare da na kalle shi ba.
ya amsa,"lafiya lau, na sameki lafiya".
nayi shiru. ya sake cewa,"zuwa nayi mu tafi". nan ma nayi shiru. Éumin iskar bakinsa da ya fesar ya sauka a fuskata. ya Æara faÉin,"ki shiga ki Éauko kayanki mu tafi". kamar da dutse dai yake magana. ya daÉa ce wa"Habibty Hubbi fa ke magana". nan ma na masa shiru. sai ya sauke dogon numfashi alamun ya Æosa kana ya Æara cewa,"ki shiga ki Éauko kayanki mu tafi, duk abin da za'ai ma yi shi a can gida".
nayi masa wani kallo na ce,"ba ni da wani gida da ya wuce wannan". na faÉa ina masa nuni da gidanmu. "kana iya jiran mahaifina ya dawo ka sanar masa ka zo mayar da ni ne. kuma bari kaji zan koma cikin gidanmu amma ba don in Éauko kaya in bika mu koma wancan prison Éin ba, ba zan koma in da ban da wata daraja ba".
"Habibty mu mance faruwar komai anan. ni ba zan iya tsayawa inga Abbaa ba domin ina jin kunyarsa akan abin da ya faru, kiyi haÆuri ki zo mu tafi kinji".
hmm wato tunaninsa ansan turoni gida yay, tsaki kawai bar masa na shige gida. Ummani bata san da dawowata ba saboda tana Éaki, sai bayan kusan minti goma