NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 97

ewa amma akwai cutuwa a hakan daga ke har shi. ban ce kisa shakku akan mijinki ba ban kuma ce ki fara zarginsa ba, amma dai kin yi shashashanci da sakarci, na san kin sani tunda kina da ilimin da ni kaina za ki bani, amma ko a addini wannan ƙauracewa junan bai halatta ba. naji kin yi iyakar yinki wajen ba shi haƙuri amma bai haƙura ba, to kin manta ke macece cikin ruwan sanyi da dabararki ba tare da tashin hankali ba za ki dawo da hankalin mijinki gareki, amma ta irin hanyar ko in kula da kika bi ai hauka ne, sai ya fara sha'awar wata macen can daban, ga ƴan uwansa kusa da ke da su ke jiran kowacce dama dan shiga tsakaninki da shi amma ba ki fahimta ba. duk wannan abin da suke aure su ke son saka shi yayi ko ya sallameki, amma in sha Allahu ba zasu yi nasara ba. gwara ki zauna ku fahimci juna, da kalar na ki salon ki faɗa masa idan har akan rashin haihuwa ya sauya miki to kin amince masa ya auro wata ke ba ki da matsala da kishiya". Haka mahaifiyata ta saka ni gaba da tarin nasihohi akan biyayya da haƙuri a zamantakewar aure, ta bani shawarwari wajen kulawa da mijina, da hanyoyin da zan bi wajen karkato da hankalinsa kacokam gare ni. numfashi na sauke bayan gama jin duk kalamanta, cikin raina ina alƙawarin cigaba da haƙuri da kau da kai fiye ma da wanda ni a baya. nan ta umarce ni da in tashi in fara shiryawa la'asar na yi magriba zata kawo kai, bacin haka ma in yamma tayi masu mota sun fi cika kuɗi. A sanyaye na miƙe ina wucewa ɗakina, ina shiga kuma na fashe da kuka don har ga Allah ni dai bana so na koma gidan Nazifi a yanzu, ina so zuciyata ta huta na lokaci mai yawa in dawo hayyacina. to na rasa ta yanda zan buɗi baki in bayyana musu cewa shi da kansa ya sallamo ni, ina hasko yanda zasu ƙuntata ne shiyasa na zaɓi in ɓoye ɗin, gwara kawai in haɗa kayan in koma can ƙauye nayi zamana in ya so in nemi ɓangaren da kwata kwata bamu kai musu ziyara ba, ko in koma gidan nasa in yaso duk wulaƙancin da zai min yayi na shirya ɗauka, da wannan shawarar da zuciyata ta bani na shiga kimtsa kayana cikin ƙwarin gwiwa. motarsa ta faka a ma'adanar motoci, ya fito daga cikin motar hannunsa riƙe da leda fara me ɗauke da tambarin gidan abinci. me gadi yay masa sannu zuwa shi kuma ya shige bayan gaisawarsu. da shigarsa falo ya aje ledar akan kujera, ƙarasawa yay ya kunna tv ya dawo ya zauna, can kuma ya miƙe tare da ɗaukar ledar ya shiga kitchen, abincin da ke cikin takeaway ɗin ya juye a plate, duk abin da yake yana yi yana bin kitchen ɗin da kallo, gani yake kamar zai ga Sa'ida ta bayyana da wannan annurin a fuskarta, fuskar da kana gani zaka tsinci zallar so da ƙaunar kyautatawa mijinta, fuskar da bata nuna fushi ko da tana cikin damuwa, ko da ta gaji zaka ga akwai murmushi a fuskarta. cikin sanyin jiki ya fito daga kitchen ɗin ɗauke da plate a hannunsa, duk cikin kwanaki shida da suka wuce yaune ranar da ya fi jin gidan ya masa mugun girma, haka kuma yau yafi jin yana matuƙar kewar matar gidan. zama yay yana cin abinci sai dai cinsa yake yana jin kamar magani, bai sani ba rashin daɗin daga bakinsa ne ko kuma daga abincin ne, duk da dai yana ɗora hakan ma akan damuwar da yake ciki, don faruwar lamarin su Atika yasa Iyam ta ɗauki fushi da shi, tana faɗa masa lallai sai dai ya zaɓa ko yaran ko kuma muguwar matarsa juya wadda bata san darajar ɗa ba. shi bai taɓa sanin Sa'ida ce gidan nan ba sai bayan tafiyarta, don ranar da ya dawo jin gidan yay ya zama tamkar kango, ga dai shi ba wai suna good time da ita ba ne, haka ba wuri guda su ke kwanciya ba, amma sai yaji ashe motsinta ma a gidan rahama ne, a washegari kuwa da safiya tayi babu abincin safe babu na rana sai yaji duk kewarta ta cika shi, duk da ko kusa bai nadamar turata gida, haka ya gangara ya tafi gidansu zai ci abinci saboda shi ba mai son na siyarwa ba ne, sai dai yana zuwa Iyam tayi masa gate tace ai yanda ba'a bawa yara abinci a gidansa haka itama abincin gidanta ya daina ci duk da gidan ubansa ne, dole yana ji yana ganin abincin da yake so ya tafi ya barshi, sai ƙanwarsa Basira ya kira ta kai masa office da yake bassu nisa da gidanta. kasa cin abincin yayi ya ajiye ya kwantar da kansa a jikin kujera, idanuwansa a rufe tamkar mai bacci, ya jima a haka kafin ya buɗe ido yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa. lambarta ya danna sai dai bai latsa kira ya tafi ba, sunan da ke kan screen ɗin kawai yake kallo, shi kam har ga Allah ko da yace ta tafi bai taɓa tsammanin zata yi zuciyar tafiya ba, kamar yanda bai taɓa tsammanin za'a yi kwanaki har bakwai babu kiranta babu saƙonta, saboda shi ya san wace ita akan haƙuri, kuma shi ya san wace Sa'ida akan son Nazifi. Numfashi ya sauke ya ajiye wayar a gefe yana so ya daure kar ya kirata ɗin amma ya kasa daurewa saboda mugun kewarta da ke addabar zuciyarsa, sai dai yana kira aka shaida masa wayar a kashe. wannan hakan kuma ya taɓa zuciyarsa, kallon agogon falo
🏠