ba akan batu. aifa kamar na turata faÉa take yi har sai da na fara hawaye, don idan akwai abin da na tsana bai wuci Éacin ran mahaifiyata ba musamman ace ni ce sila. ni dai ina ga tun da ta haife ni ban taÉa shan faÉa a wurinta ba irin yau, haÆurina ba shi yasa ta haÆura ba sai don karan kanta.
"ni dama tun ranar da kika zo na kalle ki na kasa yarda da yanayinki, shiru kawai nayi miki. don haka buÉe ba ki ki faÉa min haÆiÆanin matsalar da ke faruwa har kike ikirarin a sakeki ki huta".
ina kuka na ce,"Ummani babu komai, kawai ji nayi na gaji da zaman auren, gaba Éaya na daina farin ciki sai tarin damuwa, maimakon dariya kullum cikin kuka na ke, ni har son Nazifin ma na daina, kuma ban san dalili ba".
"ehh lalataccen lamarin babba ne tun da har da kanki yau kike buÉar baki ki faÉi sunan mijinki gatsal abinda ba ki taÉa ba, auren ma kin gaji da shi la gaira wala dalil, to ko dai aljanu sun shigeki bamu sani ba Sa'ida".
"aljanu kuma Ummani!".
"to in ba aljanu ba haka kawai ki ce kin gaji da gidan aure kin daina son miji duk babu dalili".
nayi shiru ban ce komai ba. ita Éin ma shiru tayi tare da tsura min ido, kallona take cike da zurfin nazarin son gano gaskiyar lamarin. a gefe guda kuma itama damuwa ta bayyana Æiri Æiri a fuskarta, tabbas uwa dabance.
"zan iya cewa ba ki taÉa min Æarya ba Sa'ida, fito ki faÉa min gaskiyar abin da yake faruwa kar ki Éoye min. ba akan kowacce matsala ta gidan aure ake shiru a Éoye ba, in ta girmama faÉarta ake don a san hanyar da za'a bi a magance, balle ke da kika yi irin wannan furucin kowa yaji ya san lamarin ba Æarami ba ne".
ajiyar zuciya na sauke ina tunanin abin da zance mata, bana so na faÉa mata abunda zai Éaga hankalinta ya sakata a tsananin damuwa, to amma kuma idan ban faÉa mata ba bayan ita Éin wa na ke da shi?, idan na ce zanci gaba da Éoye komai a raina ina barinsa ni kaÉai cutuwa zan ta yi, don haka gwara na faÉa mata Éin, ita uwa ce, wacca ta shekara kusan arba'in a gidan aure, don haka fahimtar matsalar gidan aure ita Éin ce kawai, har ta kwantar min da hankali cikin salama.
takaicin da ke Æasan zuciyata shi ya riÆe zubar hawaye na, tiryan tiryan na shiga zayyano mata halin da na ke ciki kusan shekara guda, sai dai haka dole na Éoye mata zancen dukan da da su Yaya suka min da kuma shi da yace in dawo gida sai ranar da ya neme ni.
ta dinÆa kallona da matuÆar mamaki. muryarta a sanyaye ta ce,"yanzu tsawon wannan lokacin kika kasa samuna ki sanar da ni matsalar nan. ai shikenan komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma komai yayi farko zai yi Æarshe, Allah ya magance. hakan kaÉan kenan daga jarabawar gidan aure, sai dai ba kowacce mace ke iya cinyewa ba, a zamanin nan wadda zata yi irin haÆurinki da wuya. kema tun da kika faÉa ba kya jin daÉin zaman tabbas kin gaji da abubuwa ne, to amma ki sani ba ke kaÉai ke cikin irin wannan yanayin ba, mata da yawa basa jin daÉin zaman haÆuri kawai ake ana shanyewa, da za kiji matsalar wasu sai ki ce naki ba komi ba ne, akwai case Éin auren da naji a radiyo ce nayi idan ni ce sai dai auren ya mutu, to amma ba yanda ka iya, mutuncin mace da darajarta na ga gidan miji, idan ka fito ma zaman zawarcin kansa Æalubale ne babba. saboda haka ki Æara haÆuri akan wanda kike yi Allah ba zai barki dawwama a haka ba. daidai da rana Éaya karki ce za ki Éauki huÉubar shaiÉan domin zai kai ki ya baroki, a Æarshe ya barki da faÉawa kogon danasani. kuma ki godewa Allah Sa'ida domin masu matsalar rashin haihuwa da yawa suna gidan iyayensu auren ya mutu saboda ba za'a iya zama da su a haka ba, kuma sun fito an rasa me aurensu. Tabbas mijinki yay ÆoÆari kuma yay haÆuri, in wani ne tuni ya Æaro aure, kuma matar ta zo da zarar ta haihu ya samu Æofar wulaÆantaki, don Æarara zai nuna miki banbancinku. to amma kinga bai auren ba bai kuma da niyya, ba don ba ya so ba sai dan ganin in yay hakan bai kyauta miki ba. babbar matsalarki Æ´an uwansa masu shiga hurumin da bana su ba, don haka ki Éauke ji da ganinki akansu da ita kanta mahaifiyar tasa, in kika nuna musu damuwarki kin Æara basu gudunmawar cin mutuncin goranta miki ne. ke dai in har kina riÆe da addu'a, nafilfili da karatun Æur'ani kin gama wallahi, nasara sai dai ta fuskanceki ba dai ta juya miki baya ba, kuma komai sai ya juye miki shi zuwa alkhairi, haihuwa Allahn da ya basu har su ke goranta miki akan ke ba ki samu ba, in sha Allahu kema kafin gushewarsu a duniya Allah zai dube ki ya azurtaki da haihuwar nan su ga Æ´aÆ´anki, amma sam ki daina damuwa da kalmar juya duk da kalmar akwai ciwo, Allah ya saita lamuranki".
"Ameen Ummani na gode sosai Allah Æara lafiya da tsawoncin kwana".
ta numfasa kafin ta Æara cewa,"kuma ina so na ankarar da ke Sa'ida, duk fushin namiji duk wulaÆancinsa akan matarsa ba ya fasa nemanta ya karÉi hakkinsa duk da suna iya jur