NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 41 of 97

tafiya, ba wai zama yake siyar da kaya ba kaman su Abbaa. gaisawa su ka shiga yi da juna, Babanmu ya ke cewa da Abba,"ai ce na ke ka fita ma naga yau na fito a makare". Abbaa ya ce da shi,"nima haka ai, don yanzu ma maganar da Sa'adatu ke yi kenan ta ce yau mun raba tafiya". Babanmu na murmushi ya ce,"yanayin garin ne ai na hazo ba zaka ankare ba lokaci ya tafi. muje ko". Ummani ta shiga yi musu adu'ar a dawo lafiya da fatan nasara, yayin da su kuma ke amsawa da amin, nima nayi musu tawa, suka nufi zaure za su fita, sannan Abbaa ya dakata ya juyo yana me kiran sunana. na ɗauraye hannu na miƙe ina yarfe ruwan. cikin ladabi da girmamawa na rissina ina cewa,"Abbaa ga ni". idonsa a kaina ya ce,"sai yaushe ɗin za ki tafi?". murya na sarƙewa na ce,"zuwa yamma dai, zan jira Adamu ya dawo daga kasuwa maƙullin ɓangaren namu yana hannunsa shi ya bawa da zai tafi". na shirgo ƙaryar da ban san taya akayi tazo cikin kaina ba lokaci guda. ya gyaɗa kai ya ce,"ba na son dai tafiyar dare kin sa ni ko". "in sha Allah ba zan kai dare ba". hannu yasa a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙo min, dubu ɗaya ce yana cewa,"babu kuɗin a jikina da yawa, ga wannan zai ishe ku kuɗin mota?". kaina sunkuye na ce,"Abbaa ka barshi ma ai Ummani zata ba ni". Babanmu ya ce da Abbaa,"maida kuɗinka". sai kuma ya kallen ya ce,"ku karɓi kuɗi hannun Al'ameen in ya tashi, ki ce na ce ya baku dubu biyar". na fara godiya maganar Abbaa ta kutso da ce masa,"dubu biyar ta musu yawa Sabi'u...". Babanmu ya katse shi da cewa,"bata yi yawa ba in da fin haka ma ƙara musu za'ai". nan su ka fita ni kuma na bi su da adu'a na dawo na ci gaba da aikin da na ke. sai dai gaba ɗaya ban da natsuwa sam, zuciyata fal da fargaba da taraddin abin da zai iya faruwa a yau, ɗayan ɓari na zuciyata faɗa min ya ke kawai in faɗa musu gaskiya a wuce wurin, faɗa ne dai zan sha, sai a zo gaba batun sulhu wanda na san dole ni za'a bawa rashin gaskiya, in ya amince in koma gidansa in bai yarda ba in ci gaba da zama gidan ubana, shikenan fa kawai, to duk takura kaina da ɓoye ɓoyen na mene?, dama damuwar iyayena da bakin ƴan gidan da basa son aurena na ke gudu, to na iya shanye duk baƙin cikin miji da ƴan uwansa ma balle faɗa na lokaci, ai kafin faruwar lamarin dare na raya ina roƙon Allah mafita kuma sai ga shi ya kawo min, don haka alkhairin kenan. haka na dawo tamkar mara lafiya, har Ummani na tambayata ko ban da lafiya ne ganin yanayina duk ya sauya. ina murmushin yaƙe na ce babu komai, kawai na shirya na fita gidan Maman Yasmin, da ke tsakaninmu babu nisa, can nayi zamana muna ta hirarmu wacca itama har sai da ta fuskanci akwai matsala, tun da ta takurani da tambaya kuma na baro gidanta na dawo gida. dawowata na tarar Ummani har ta gama girkin da na ke cewa zan dawo in ɗora, a plate ɗaya ta zuba mana ni da ita, amma sam duk bala'in sona da dambu wallahi ɗanɗane ma sai na kasa, zoɓon da na sha kuwa sai naji yana min ɗaci. idan ina tare da uwata hira mu ke sha tamkar wasu ƙawaye, amma ina yau babu hirar don ita ɗaya na bari tana ta maganarta ni hankalina yana can neman mafitar da zata hana ni tafiya a yau ba tare da fallasuwar lamarin da na rufe ba. har sai da ta gaji itama da ta fuskanci akwai matsala, ta dinƙa min tambayoyi ina basarwa, ƙarshe a dabarance cikin hikima kuma ta fara bugun cikina har ban ankare ba na bayyana mata mun sami saɓani tsakanina da mijina. kuma cikin ƙunci da ɓacin ran da na ke ciki ina turo baki gaba ba tare da sani ba na furta,"ni aurenma duk ya fita a raina, a barni kawai nayi zamana a gidan ubana inda ba me cin mutuncinka ya ɓata maka rai, da za'a sakeka ma da ka huta". baki sake ido a waje Ummani ke kallona da tsantsar mamaki, don ko kusa aka ce mata zan yi furuci irin haka ba zata taɓa yarda ba, sai ga shi na furta hakan a gabanta. ta tsura min ido tana faɗin,"kike cewa auren ya fita a ranki gwara zaman gidan ubanki, Sa'ida wa kike nufin yana cin mutuncinki har kike wannan furucin mara daɗi? hankalinki ɗaya kuwa?". sai lokacin na ankare da baragadar da nayi, ai sai na koma tamkar wadda ta yiwa sarki ƙarya, na shiga raba idanuwa ina so na musanta abin da na faɗa duba da yanda ta rikiɗe min tamkar ba uwar da ta haife ni ba. ta ɗaga murya wajen sake faɗin,"magana nayi kika mayar da ni allon kallonki". "Ummani ba yanda kika ɗauka na ke nufi ba fa, kawai...". a fusace ta ce,"mayar ni shashashar Uwa kinji ko, saboda ba ki da hankali za kike irin furucin marasa tunani. tun da kike da ni kin taɓa jin na yi magana makamanciyar haka akan aurena?". na shiga girgiza kai da sauri alamun a'a. nan kuma na shiga bata haƙuri da roƙonta cewa tayi shiru ta bar maganar haka kuskure ne na riga na yi, na san Ummani da mita kuma ga Yaya Imam na gidan yana jiyo abin da ke faruwa zai fito yay min lilis, shi ba irin Yashaik ba ne me tsayawa nazari da du
🏠