nan ma dai ba'a tsira ba wani faÉan na daban na sha kamar zai duke ni. ni dai a raina ce na ke kai da gidanku wai ba zaka zo ka sarara ba kaji Éumin mahaifanka. yanzu ba ga shi tun da na zo ganin mahaifiyata da hirar da na ke da ita ya mantar da ni wata matsala da na ke ciki da damuwa, duk da cewa dai hakan na maÆale a raina.
shima Kaka da suka dawo sai da yay nasa faÉan akan me zan zo kwana gida ana zaune lafiya, shi mijin na baida hankali da zai biye min, don haka ai maza maza a kira masa shi ya zo ya Éauke ni mu kuma, in bikin ne gobe ya kaini tasha in hau mota, mene saina zo wani gida ban da fitina da neman magana.
ni dai fara faÉan nasa Æirjina ke dukan tara tara, tsoro fal raina, dama shi wannan tsoho kwai jarabar masifa, in ya fara sai dai ayi shiru ai haÆuri kawai har ya sauke, ga ba ya fara magana ace za'a yanke shi. yaji ma da lafiyar jikinsa da bata ishe ahi ba amma inaa sai faÉan bala'i. ni dai hawaye kawai na ke saboda na san shikenan asirin da na ke Éoyewa zai falla su, da adu'ar da na ke tayi cikin raina dai Allah yasa ya haÆura yay shiru da maganar. na sauke wawiyar ajiyar zuciya ni dai na tashi na shige Éaki bayan yi musu sai da safe, kuma sai bayan na shiga Éakin ne kuka mai sauti ya Æwace min, tiryan tiryan komai ya dinÆa dawo min tun daga ranar farko na canjawar mijina da Æ´an uwansa har zuwa yau da ya ce naje gida ya bani hutu. shigowar Ummani Éakin zata kunna min maganin saura shi yasa na tsayar da kukan nayi shiru ina cusa fuskata cikin tsummokaran da nayi filo da su, a haka kuma bacci ya Éauke ni ban shirya masa ba.
washegari Æarfe bakwai muka isa tasha, mota guda muka cika, da ni da Ummani, Fati da Zainab Æ´aÆ´an Alhaji babban wan su Ummani, Anty Khairi matar Ya Imam da Maman Yasmin matar Yashaik, Mama Hajara da Umma A'i Æannen Ummani da su ke uba Éaya, sai Æananan yara duk jikoki. haka muka Éunguma muka yi Æauyenmu Geza in da nanne mahaifar su Ummani. mutanan Æauyen sun ji daÉin zuwanmu sosai, murnar ganinmu har tafi ta gudunmawar da muka kai musu na kuÉi da aka haÉa naira dubu hamsin, kun san karramawa a wajen mutumin Æauye ba kamar mutumin birni ba, aka Éinka haba haba damu, aka bamu masauki mai kyau da abinci mai kyau.
bikin yini biyu aka yi, da ike babar amaryar sun rabu da mahaifinta, saboda haka ranar farko can gidan Babanta mu ka je washegari kuma muka dawo nan gida yinin mahaifiyarta, da Babarta da Ummani Ya da Æanwa ne amma cousins. mun yi ziyara sosai a Æauyen don dama duk sanda Ummani ta je sai tayi kwana uku huÉu take dawowa, to ziyar ziyarcen da mu ke tayi yasa na manta da batun wani mijina, danginsa da matsalar da na ke ciki. harkokin gabana kawai na ke kamar ba ni ke cikin damuwa ba, na sake nayi walwalata cikin Æ´an uwana, kullum a wasa da dariya ake ba babu wani Éacin rai, sai hakan ya mantar da ni abubuwan da suka faru kwanakin da suka wuce, wataÆila sai an gama biki na dawo hayyacina sannan in koma luntsum cikin damuwar.
amma har wani fresh nayi Æirjina ya cicciko saboda garin kunun sabaya da ake damawa safe da yamma da dare muna sha da madara da zuma, ni kaina sai da na yaba da irin haÉin don gaskiya na musamman ne tun da na gani a jikina, cikin kwanan shidda kawai yay min aiki, ai ba zan tafi ba kam sai an bani lambar me siyarwar tun da naji Matar Buba ta ce a kano take.
kwananmu bakwai cif muka juyo gida, bayan an haÉo mu da sha tara ta arziÆi, ba kamar ni da aka jido min kayayyaki, tun da suka ji Ummani ta ce ai mijina babu ruwansa Éan gargajiya ne shikenan fa kowa sai ka ganta da garin masara ne, kuka, daddawa kayan dai girki iri iri, waken suya kuwa sai da aka haÉo ni da rabin buhu da shi da aya, tsintsiyar laushi da kujerun zama sai ka rantse kasuwa muka je siyayya, ga tsofaffin nan duk suka haÉo magunguna na matsalar rashin haihuwa su ka bani su ka ce in amfani da shi da izinin ubangiji zan Éauki ciki.
washe garin ranar da muka dawo gida Abbaa ya ce in haÉa komatsaina in koma gidan mijina in ya so a haÉa ni da Sauda mu tafi tare tana taya ni kwana. ai tun da yay wannan furucin na shiga tashin hankali, naji ina ma bamu dawo daga Æauyen ba, duk na hargitse daren ranar da Æyar na iya bacci saboda tunanin mafita.
da safe ina wanke wanke sai ga Babanmu ya fito zai wuce kasuwa. ya tsaya muna gaisawa nan ya tambayeni ba dai ni da wata matsala ko na ce masa ehh, yay min nasihohinsa na iyayenmu da ba sa gajiyar yi mana a ko da yaushe, duk da cewar abu Éaya ne dai ake ta faÉa maka to amma muhimmancinsa yasa ake ta nanata maka Éin.
Abbaa ya fito shima a lokacin tare da Ummani ta rako shi, da yake gaskiya iyayenmu da wuri wuri su ke fita kasuwa, zaka samu Æarfe tara sun fita. Baba Tijjani ne ma ba ya fita sai kusan sha biyu na rana, da ike shi yafi su Abbaa samu sosai, don shagunan kansa ne ma da shi har guda biyu, kuma duk ya zuba yara a ciki, to ko yaje sai dai duba yanayin yacca ciniki ke