cikin tsadadden kular abincin da Hubbi yazo da su last week daga dubai, wanda naji Hamida na kuÉinsu ya kai dubu Éari biyu, bayan nan na Éauko bilenda na haÉa lemun abarba na juye shi cikin jug.
Da kammalawata na kwashi komai na kai parlon Hubbi da ke nan sama na jera akan table, na gyara Éakin ko'ina ya Éauki Æamshi sannan na fito na kulle. da na leÆa parking lot ta window banga motar da ya fita da ita ba na san bai dawo ba, hakan yasa nayi komai a nutse sai dai kuma cike na ke da mamakin rashin dawowar tasa da wuri yau, tun da shi duk inda biyar da rabi take ya dawo gida, da yaci abinci zai kwanta sai an kira magrib zai fita masallaci ba zai dawo ba sai bayan isha'i, in da nake jin daÉi kenan Allah bai bani miji mai son zaman majlisa ba, yafi ganewa zaman gidansa, duk da yanzu na kanyi fargabar dawowarsa duba da bama wanyewa lafiya da shi, ga shi na rasa gane kan dalilin hakan, na rasa silar tashin hankalin, na rasa ta ina aka samu saÉanin.
Æakina na koma nayi sabon wanka, na fito na shirya cikin riga da skirt na atamfa da Éinkin yay matuÆar amsar jikina, skirt Éin ya fito da cikakken Æuguna, musamman hips Éina wanda shi ne abu mafi Éaukar hankali a jikina bayan baiwar madaidatan Æirji. Na bar Éakin ina ta baza Æamshi, duk da halin da na san ina ciki yanzu a rayuwar aurena, hakan ba shi ke hana ni gyara jiki in ci kwalliya in isa ga mijina ba, ba kuma shi zai sa na waje ya shigo in bari ya gane ina cikin matsala ba, na iya sirrinta zaman aurena.
In da sabo na fara jure halin ko in kulawar mijina yanzu, hakan yana damuna amma na kan nuna masa bai dameni ba balle hakan ya Æara ingiza shi, ban taÉa fasa hidimta masa ba, shi kansa ya san ina da mugun haÆuri don idan wata ce tuni anji kansu, a yanzu banda burin da ya wuci mu zauna mu fahimci juna da shi, ya karanta min kuskurena in gyara, domin har ga Allah bana jin daÉin irin zaman da muke yi, auren soyayya muka yi ba auren Æiyayya ba, kuma tsawon shekara takwas da aurenmu bamu taÉa zaman da za'a ce don mun sami saÉani wai zamu shafe sama da kwanaki babu ruwan wani da wani ba har ta kai ga muna raba makwanci, ga shi yaÆi bani damar magana da shi balle ya karanta min laifina, ni kuma iyakar sanina ban masa wani laifi ba, haka dangisa ma, ban san matsalar da ta gifta a tsakaninmu ba da kowa ke nuna min Æiyayya Æuru Æuru, har shayin shiga cikinsu nake, sun dinga min kallon banza kenan ana jajja baya da ni kamar mai warin jaÉa, sai in shiga taro ma in fita babu wacce zamu yi magana da ita in ka cire gaisuwa da zata haÉa mu, abin da yake matuÆar Éaure min kai duk wannan matsaltsalun cikin Æ´an watanni ne, da can komai lafiya, har gani nake tamkar duk matan duniya babu wacca tayi dacen dangin miji irina, so da Æaunar da suke nuna min kamar za su cinye ni, miji kuwa ai sai son barka, a ko ina zan bugi Æirji in ce nafi kowacce mace sa'a, sai dai banda yanzu, yanzu kam Éaya na ke da wadda aka aurawa mijin da bai sonta.
A yanzu haka so nake na samu wani in karanta masa halin da nake ciki ko na Éan ji sanyi cikin raina, sai dai gaba Éaya na rasa wa ya kamata nayi maganar da shi, ni dai ban isa na tunkari Æawa da zancen matsalar zamantakewar aurena ba, ban ma ni da shaÆiÆiyar Æawa, mahaifiyata kuma bana so na tunkareta da magana makamanciyar wannan, ba don komai ba sai don gudun shigarta damuwa, tun da a ko yaushe burinta taji nace mata lafiya muke babu wata matsala, haka kuma a kullum nasiharta a kaina in ta haÆuri in kuma guji kai Æorafi domin hakan na Æara taÉarÉare zamantakewar ma'aurata, kuma bani da Yaya mace ko Æanwa balle in shaida musu halin tsananin da na ke ciki, sai Yayyu maza da Allah ya bani har huÉu, su kam bana jin ma zan yi kuskuren musu wannan maganar, kun san ance mai Éaki shi yasan inda ke masa yoyo, idan zan kira su in kwan dubu ina faÉa musu matsalar da ke faruwa ba zasu taÉa yarda ba, in ace matsalar daga ni ne to nan za suyi saurin cafewa har a iya samun mai zuwa har gidana ya naÉa min na jaki, amma batun wai in faÉa musu laifin Hubbi ne tabbas ruwan ashariya sai na sha na Æoshi, ba kuma wai don basa sona ba ne, su na mugun sona tun da ni Éaya ce mace a cikinsu, kuma su na matuÆar tausaya min, amma batun dai su goyi baya ga laifin mijina sai dai ya zama zance, gwarama ranar da Ya Imam ya zo duba ni yaga duk na bushe ya zauna yay min nasihohi masu ratsa jiki akan zaman duniyar gaba Éayanta Æ´ar haÆuri ce. Abbana kuwa zafi ne da shi, ina fara faÉa masa zai sa azo a Éauke ni ko kuma yace in kwaso kayana in taho, duk ranar da mijin ya san darajata yazo ya bada haÆuri in koma ko ya rabar masa da Æ´a, ni kuma ko kusa bana son abin da zai ja igiyar aurena ta sami tangarÉa, ina cikin matan da za su iya shanye kowanne kalar baÆin cikin gidan aure akan dai a sake su, wani waje daban ma ban so inji aure ya mutu bare a kaina.
Tun barowata sama