ce lakwaf lakwaf, shiyasa Mamun ke mata yanda ta so ita da Æ´aÆ´anta duk da ba miji guda su ka haÉa ba, sau tari sai kishiyarta ce ke shigar mata idan tayi mata abu, ita Ummani babu ruwanta haka take cewa kowa tashi ta fishshe shi.
tun bayan da Yashaik yay aure aka bige Éakinsa aka Æara girman kitchen Éinmu da tsakargida, sai duk tsakar gidanmu yafi na sauran girma, ga shi Yaya Imam da Yashaik suka haÉa kuÉi aka zuba mana fasashshen tayels, shikenan tun daga wannan gyaran fa Mamu ta Éaura gaba da Ummani da Æ´aÆ´anta, tsakaninta da mu harara da gyatsine, amma a hakan duk san da na zo Ummani sai ta tura ni ta ce inje in gaisheta duk da ta san ba zan samu tarbar arziÆi ba.
Æangaren Baba Tijjani na fara shiga, shi ne wanda Abbaana ke binsa. ina ta sallama daga tsakar gida babu wanda ya amsa min ga shi ina jiyo hirarsu a falon na su, sai da na Éaga labule na leÆa falon tukunna. cikin yaran ba wanda yay min kallon arziÆi kamar yanda mahaifiyar tasu tayi min, don haka a tsaitsaye na gaisheta na fito na wuce Éangaren Babanmu, shi kuma shi ne yake bin Abbaana Baba Sabi'u kenan, Æ´aÆ´ansa ke ce masa Babanmu duk sai muka Éauka, na same shi yana nan muka gaggaisa har yana tambayar zuwan nawa na lafiya da rana tsaka haka, na ke shaida masa zancen zuwa Æauye amma duk da haka sai ya kama min faÉa me yasa ban bari sai gobe da safe na taho ba, hakan ai rashin hankali da tunani ne, saura kuma idan an tafi bikin inga wajen zama in mance matar aure na ke.
mu ka fito tare da Hindatu tana min dariya, wacca na haÉe fuska tun ganinta ina aika mata harara saboda fushin da na ke yi da ita akan rashin zuwa gidana, zan iya cewa sau Éaya taje sabon gidan nan namu, tsohon kuwa tsab zan Æirga zuwanta shima. ko da yake mu haka iyayenmu suke, sai ka ce zaka je gidan Éan uwanka a tsareka da tambayar me zaka je yi.
dawowata na iske Ummani har ta kammala girki, ta zuban abincin ta aje. sannu da aiki na mata sannan mu ka zauna ni da Hindatu, wacca ke faman tsokanar bai kamata a bani abinci ba ta san sai da na gama cin me maiÆo na taho. ban tanka mata na shiga cin abincina, loma biyar nayi naji abincin ya fita a kaina gaba Éaya, ajiyar zuciya nayi yayin da zuciyata ke min Æuna tunawa da abinda Nazifi yay min, nayi saurin mayar da Æwallar da ta cika idona ina saurin miÆewa na je ga fanfo zan face majina.
Ummani ta bini da ido kafin ta ce,"kin Æoshi ko me?".
"Ummani wannan murar ban san ya zan mata ba wllahi, ina son cin abinci amma sai in kasa ci".
"to Allah ya ba ki lafiya, ai da sauÆi ma tun da kina iya ci ko babu yawa".
sai sannan na ke tambayarta Kaka saboda na leÆa Éakinsa ban gansa ba. ta shaida min Yaya Kamal da Yaya Al'ameen sun je kaishi wurin magani in da ake masa gashin Æafa.
jakunkunan kayana na kwashe na shiga da su cikin Éan Æaramin Éakina, na bar guda Éaya wadda na ajeta nan kan tabarmar da muke zaune ina cewa,"ga kaya nan Ummani za'a kai Æauye".
Ummani ta jawo jakar tana duba kayan tace,"kai kai ai ko kin gwangwaje su, wannan kaya masu kyau haka, ai fa bari na Éebewa amarya ma su kyan".
ta faÉa tana Éaga wata abaya, ai ko Hindatu tayi saurin cafewa da magiya. "Ummani don Allah ki bar min wannan don Allah Ummani".
Ummani ta saki baki tana kallonta. "ke Hindatu me za ki da wannan rigar? duk uban kayan da kike da su saboda dai rashin godiyar me sama".
ta langaÉar da kai tana ci gaba da roÆon Ummani har sai da ta haÆura ta bar mata, kuma Ummani na tashi zuwa ta kai kayan abinci Éakin Abbaa tayi sauri ta wawuri wasu kayan ta arce tana ce min ai batta Æara fitowa sai gobe kuma. zaman da nayi ni Éaya sabon zafin baÆin cikin gidan aurena ya shiga huda Æirjina, sai dai haka nayi ta kokawa da kaina don ganin na dakatar da fallasa yanayin halin da na ke ciki akan fuskata, yanda na zo gida sam bana son abin da zai sa in ke tunawa da gidan Nazifi, a yau sunansa ma ciwo ya ke min mai raÉaÉi.
Ummani na can Éaki tana kimtsawa, na miÆe na shiga Éakina na hau gyaransa, bayan na gama na shiga Éakin Ya Al'ameen na kunna tv, har akai magriba ina Éakin ina kallo ni da su Yasmin da suka dawo daga yawonsu, kallon ma duk sun hanani da surutunsu, kowacce sai aikin tambaya da ita zan koma gidana? yaushe Yaya Æarami zai zo ya basu alawa?
sai bayan sallar isha'i Abbaa ya dawo, a tsakar gida ya samemu muna ta hirarmu, yaran ma har sun yi bacci sai ni da Ummani da Sauda Æanwar Hindatu da ta shigo wajenmu. cikin tsoro da fargaba na gaishe shi, kuma bai amsa min ba sai ya dubi Ummani ya ce,"lafiya dai?".
ta ce da shi,"tayi maka bayani da kanta mana".
ai lokaci guda Abbaa ya juyo kaina ya hauni da faÉa sosai akan ya hana ni zuwa gida in kai dare irin haka, kuma tun yaushe ya haramta min zuwa kwanan gida idan ba da babban uzuri ba. sai da ya gama faÉan tukunna Ummani ta ce masa ai tafiya Nazifi zai yi shiyasa ya ce in taho Éin kawai,