NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 38 of 97

utan gidan tukunna". sai kuma ta ƙara cewa,"a'a sai yanzu ma abin yazo kaina, ina ƴaƴan na ki ba ku taho tare ba?". allon ƙirjina naji ya girgiza, na tuna da yaran da nake jinsu yanzu har raina, na ce,"kin san da makaranta, musamman tasu da ba'a fashi, shiyasa na kai su wajen Iyam, amma suna ta rigimar za su biyoni su zo wurinki na ce su bari sai anyi hutu sa zo suyi kwanaki ma". tana murmushi da ya nuna jin daɗin furucin nawa ta ce,"Allah sarki yaran albarka, wallahi Sa'ida sosai na ji daɗin kyautar nan da aka maki. zan samu lokaci in je har gida in yiwa Iyam ɗin godiya". na yunƙura zan miƙe ta ce,"ke dakata me na ke gani a fuskarki haka? Na ganta a kumbure". Gabana ya faɗi amma haka na ƙaƙalo guntuwar dariya na ce,"sharrin mura ne...shekaranjiya ta saka min azababben ciwon kai, muka je asibiti suka bani wani magani, shi ne ni kuma saboda tayi saurin tafiya na sha overdose ya juyar min da kai na koma kamar wata ƴar maye, garin sakkowa a bene layi ya ɗebe ni na ƙuma fuska a hannun bene". ta kalle ni da kyau tana girgiza kai ta ce,"ke kam naga ranar da za kiyi hankali, ina ke ina shan maganin mura har over, ko da ya ke da aka samu ɗin ma kika sha". fuskata ta ƙara washewa da gajeriyar dariya na ce,"Ai fa shima haka yayta faɗa". "ai dole yayi miki faɗa, da kin gangaro daga saman fa?". na datse maganar da cewa,"Allah ya taƙaita ai, Ummani ni fa yunwa na ke ji mura bata barni na ci komai ba yau, zumuɗin zuwa nan ne ma yasa na kasa tsayawa girki". "naga alama ɗaukin zuwa ƙauye yay miki yawa. je ku gaisa ɗin kafin ki dawo miyar ta kammala, nima sauri na ke tayi kar uwar tawa ta dawo ta cinye ni ɗanya da mitar Kakanta yayi cefane da wuri ni kuma naƙi gama musu abinci". ta faɗa tana tashi ta shiga madafa. dariya ta ban sosai da ta ce uwarta, Walida ce ƴar gidan Yaya Imam, ƴar nan ba dai tsufanta ba kamar aljana, tun da aka kawota Yaye shikenan ta zama ƴar gidan, tsakaninta da gidansu ziyara, har faɗa ma take ita fa Ummani ce Babarta ba Momi ba, ita da Daddynta Babansu ɗaya, duka Abba ne ya haife su. Gidanmu ba wani babba ba ne sosai, tsaka tsakiya ya ke, sai dai bai saka yawan mutanen da suke rayuwa cikinsa ba sun takura, dan zaka samu kowanne ɓangare akwai ɗakunan yara har biyu bayan na iyayensu, asalinsa ginin ƙasa ne daga baya aka sabunta shi da na bulo a hankali a hankali. gidan gado ne da iyayenmu su ka gada a wajen mahaifiyarsu, don haka ahalin mutum uku ne a gidan da su ka fito ciki ɗaya, tun bayan rasuwarta da aka raba musu gado sai suka yanke shawarar zama wuri ɗaya don babban burin mahaifiyar tasu kenan, mahaifinsu na raye shi kuma tun da ya samu karayar arziƙi har ta kai ga ya sayar da duk kadarorinsa hatta kuwa da gidansa da suke zaune saboda biyan basukan da ke kansa, shi ne ita Hajiya Umman tasa yaranta su ka gyara nan gidan nata da itama gadarsa tayi suka koma da rayuwa cikin rufin asirin ubangiji, dama ita ɗaya ce matarsa har ta mutu, don itama bata rasu ba sai da ta tsufa sosai. ɓangarenmu ne a farkon shigowa gidan, idan ka shiga daga ciki ta tsakiya kuma ɓangaren Baba Tijjani da nasa iyalan, shi ne mai mata biyu da tarin ƴaƴa goma sha biyar. sai daga gefen hagu na ɓangaren nasa nan Baba Sabi'u ya ke, shima matansa uku amma sun rabu da ɗaya, ƴaƴansa takwas duk mata ne Allah ya ba shi. zaman gidan namu dai kadaran kadahan ne, waɗanda ba su son zaman lafiya Mamu da ƴaƴanta, ita ce fitinanniya a cikin matan iyayen namu, duk wani rikici da zai ɓarke a cikin gidan to zaka samu daga gareta ko ƴaƴanta ya soma, kuma da Allah ya tashi sai ya bata kishiya daidai da ita. Mamu da ƴaƴanta akwai baƙin cikin bala'i, ita babban tashin hankalinta taga cikin ƴaƴan gidan wani yafi nata, haka ta tsani taga facalolinta sun fita da wani abun, ko fita za su yi tare taga shigarsubtafi tata to tabbas ta haƙura, ƙiri ƙiri ta ke nuna hassadarta bata iya ɓoyewa, kuma ko da yaushe ita ɗin dai ita ce koma baya, shiyasa bama wani girmamata a dalilin abin da takewa iyayenmu da kuma raba tsakaninmu da ƴaƴanta da tayi. mahaifiyata tana da haƙuri da kawaici, kuma tana cikin irin mutanen da ba su fiya son shiga hulɗar kowa ba, barsu da halinsu su kaɗai sai na jikinsu, bata ƙi ka mata abu ba taƙi ɗaga kai ta kalleka, Ummani ta ƙware a bawa iska  a jiyar mutum. amma fa idan aka taɓa mata ƴaƴa to anan ake ƙure haƙurinta, anan ake gane bata da kyau ko kaɗan, sam sam bata kawaici ta wannan ɓangaren, bata iya bari ƴaƴanta su halaka saboda haƙurinta, haƙurinta ba yasa ta bari a shiga hakkin ƴaƴanta. dalilin da yasa Mamu ta shafa min lafiya kenan a yaran gidan, ko sharrinta ne ya tashi bata cika haɗawa da ni ba kam, don ta san bakin Ummani ba zai mutu ba akan haka, a cikin ruwan sanyi zata yaɓa mata maganar da zata hanata bacci. Ummansu Hindatu
🏠