NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 97

sa. "ai wallahi Hajiya ban taɓa taka sa'a a rayuwata ba irin yau, ni dai naji daɗin ɗaukarki wallahi. ban san waye ba amma idan rabonsa ce ke Allah ya haɗaku domin ya ce kar in ma yi kuskuren shaida miki shi". rai na haɗe na ce,"kai Malam ni fa matar aure ce, ko da ka ganni daga gidan mijina na zo gidanmu. kai kawai kaga mutum baka san da ga ina ba ya kama baka kuɗi ka karɓa, to ni da kuɗina don haka ga hakkinka nan, babu ruwana da kuɗin da wani ya baka". yay ƴar dariya da cewa,"ah ban ga kin yi kama da matar aure ba gaskiya, kuɗinki kuma ko na karɓa ma wallahi sadaƙa zan miki da su, gwara ki ɗauka ki rage zafi kafin Alhajin Allah ya bayyana a gareki ki huta da hawa abin haya". ko kusa ko alama tunanin Nazifi a lokacin bai zo cikin kaina ba, idan ma tunanin nasa ya zo ba zan kawo shi ya biya ba dan babu ta yanda za'ai ya ɗau wannan uban kuɗin ya bayar kawai kuɗin motar da bai wuce ɗari shida ba, abu sai ka ce a film ko littafi, ai ba hauka ake ba, kuɗin ba tsigarsu yake yi ba. don haka tsaki naja dogo na wuce gida ina faman masifa akan irin ƴan rainin hankalin adaidaitar nan. shi kuwa me adaidaita ya murɗa babur ɗinsa ya bar ƙofar gidan, tafe yake kawai idanunsa na haska masa hoton arniyar motar waccan mutumin, da shi kansa mutumin da kamarsa ta nuna tamkar sarki, ko ba sarki ba to ya ratsu cikin jinin sarauta, irin su ne zaka musu kallo ɗaya kasan da ba su taɓa sanin babu ba, haka ba su ƙyashin fiddawa su bayar. me ɗan sahu dai har ransa yaji mugun tausayin Sa'ida idan har mutumin yazo wajenta taƙi amince masa don yaga da gaske namijin aure ne. ina shiga gida na tarar da Ummani a tsakar gida tana gyaran alayyawu, ta riƙe haɓa tana kallona ta ce, "Amma dai kuwa Allah ya shirye ki Sa'ida, haka sai da kika taho yanzu?." yanayin fuskata kuma yasa ta ƙara cewa,"to ke da wa kuma daga zuwa sai ɓacin rai?". dafe kai nayi ina zaunawa a kusa da ita na ce,"wani banzan me adaidaita sahu ne mara tunani da lissafi kawai". ta ce da ni,"ai sai haƙuri, suyi haƙuri da mu muyi da su haka lamarin ya ke. sai ki saki ran naki haka kuma, ni ina zan wani farin ciki ina ganinki rai ɓace, ai sai kisa ni a damuwa". jikinta na faɗa ina kwantar da kaina bisa kafaɗarta ina cewa,"Ummani nayi kewarki sosai wallahi, tun fa mutuwar Inna Talatu ko?". na faɗa ina shigewa jikinta kaman zan koma cikinta. ta ce,"Kai jama'a, wai Sa'ida kam sai yaushe za ki girma ne ni kam, kita maƙalƙale ni kaman wacce bata bar shan nono ba? To ko dai cikin zan mayar da ke?" ta faɗa cikin ƴar dariya tana mai tarairayo ni jikinta, yayin da farin cikin ganina ke lulluɓe da ita. murmushi nayi ina ƙara narkewa a jikinta ina jin wani irin tasirin natsuwa, so, ƙauna, salama, jin ƙai, na fitowa daga jikinta yana ratsa ilahirin nawa jikin. na ƙara cewa,"Nayi kewar ki ne sosai Ummani, gaskiya mata muna ƙoƙari wallahi, in ba auren ba me zai nesantaka da ɗumin jikin mahaifiyarka har akai watanni da yawa". Ummani ta ce,"to ya za'ai auren kenan, kuma ai ku godewa Allah ma da zamani ya canja, mu lokacin da akayi namu auren tsakaninmu da gida ai sai shekara shekara in dai ba da wani babban dalili ba". na ɗago kai a jikinta ina zaro ido waje in ce,"shekara! tabɗijam, sai ka ce waɗanda aka kai kurkuku, duk haƙurina ba zan iya ba kam sai dai in haƙura da auren". harara ta watsa min tana dungure min kai ta ce,"ke dai anyi autar gaske, Sa'ida aure sunnah ina ke ina cewa za ki haƙura da shi. hakan ma ki gode Allah mijinki ba mai tsananin kulle ba ne". "Allah Ummani ko a haka ina jin rashin daɗi, shi ma ai kusan tsananin gare shi akan fita". "eyy fa to ba laifi kam Nazifi shima ba ya son fita amma ai ba kamar wanda za ki ga sun wuce wata uku biyar babu in da suka leƙa, kuma ke fa duk wata hidima idan ta tashi ya barki kije. kuma ni fa daɗin hakan naji bacin haka Sa'ida in aka biye miki ai rana ɗai ɗai ne ba zaki zo gidan nan ba". lafewa na ƙara yi a jikinta ina murmushi, ina jin tsantsar farin ciki da jin daɗin kasancewa da ita na ratsa zuciyata. idona a lumshe naji tana cewa,"mage sarkin son jiki sai ki tashi ai kije ki gaida mutanan gidan". na zame a jikin nata ina cewa,"wai ina su Yasmin da aka barki ke ɗaya?". na faɗa ina ƙoƙarin karɓawar wuƙar hannunta ita kuma tana cewa,"waɗannan yaran yanzu ai sai Annabin yabo, kan in ƙyalla ido sai dai kiga na neme su na rasa. yanzu fa zancen da na ke miki ban san da fitar su ba kuma da suna zaune nan Walida na kafa min sharaɗan kar in musu miya me yaji". nayi dariya ina cewa,"sai na fara make Walida in bata yi wasa ba, wato tsabar ta kai Babata ma take kafawa sharaɗi, lallai samun wurin zama, to kuwa rabon in kwasheta in mayar da ita wurin uwatta ne". Ummani tayi dariya sosai ta ce,"ke da ubanta ai kun fi kusa. ni dai ƙyale ni da tayin aikin kije ki gaida m
🏠