ta dunÆa zugani akan in juya masa baya in koma baccina amma sai naji ba zan iya ba, haka na miÆe zaune kamar ina so kamar bana so nama kasa gane kaina.
shi dai yana tsaye kamar wani gunki kallona kawai yake yi, ya shirya cikin manyan kaya riga da wando na yadi milk colour, yayi bala'in kyau kansa babu hula. kasa daina kallonsa nayi saboda masifar kyawun da yayi min, ba tare da shiryawa ba murmushi ya suÉuce min yayin kallonsa, kalmar kayi kyau na ke shirin faÉa masa, amma sai dai saÆon da ke a saman fuskarsa yasa na sunkuyar da kaina Æasa na ce,"Ina kwana".
Maimakon amsa gaisuwar tawa sai ji nayi ya ce,"Kafin nan da awa guda ki tabbatar kin tattara kayan ki kin bar min gida, kije gidanku ki zauna har sai san da na neme ki".
a zabure na waro idanu waje har ban san lokacin da na sauko akan gadon ba saboda ruÉani, hannuna dafe da Æirji idanunsa cikin nawa na ce,"Hubbi me ka ce?".
ransa a haÉe tamkar hadari ya ce,"Kinji ai ba kya buÆatar na maimata miki, ki tabbatar kafin na dawo kin bar gidan nan in ba haka ba za ki yi karo da abin da ba ki taÉa karo da shi ba, wallahi muddin na dawo na sameki sai na miki wulaÆancin da kare ma ba zai shinshina ba".
ya faÉa yana nuna ni da yatsa, kafin ya fita ya barni tsaye cikin maÉaukakin mamaki da tsantsar al'ajabi, haka na Æame kamar gunki Æofar kawai na ke kallo idona ko Æiftawa ba yayi, tashin hankali da firgicin da su ke zuciyata kuwa tamkar zata faso Æirjina ta fito.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". na faÉa a bayyane Æirjina yana harbawa hannayena har lokacin dafe da Æirjina.
"lamarin har ya kai haka?, duk haÆurin da na ba shi?, wanne irin bala'i ne wannan?, in tafi gida fa har sai ya neme ni, me yay zafi har zai yanke tsatstsauran hukunci haka? akan dai iya abin da ya faru jiya ko kuma da wani laifin daban a gefe da ban san da shi ba? to ni kuwa in je in ce da su Abbaa me?".
a fili nayi maganar ina jan numfashi sama. daÉas na zauna kan gadon na kafe wuri Éaya da kallo, cikin kaina na rasa tunanin me zan yi, na kuma rasa inda zan Éora wannan al'amarin me girman gaske. ban san lokacin da hawaye ya shiga zarya a idanuna ba, lallai ina cikin jarabawa, kuma tabbas na yiwa kaina alÆawarin cinyeta, ba zan taÉa bari na faÉi ba in Allah ya yarda.
zuciyata ta fara bani umarnin gaggawar tashi in bar gidan karma ya dawo ya same ni yay min abin da zai zama sanadin bugawar zuciyata a yau, a karon farko naji bana son ganin ko da inuwarsa. haka na buÉe wadrobe ina Éebo kayana, ina zubawa cikin akwatu ina magana tamkar zararriya.
"Me zan ce idan na koma gida? Na ce musu mijina ya ce in je gida sai ya neme ni?, bisa laifin me? da wanne ido zan kalle su in musu bayani? Hasbunallahu wani'imal wakil, Hubbi meyasa! Me na maka a rayuwa Hubbi?".
ina kuka sosai haka na gama haÉa kayana, na Éauko hijabina zan saka wayata da ke kan madubi tayi Æara, na rufe wardrobe Éin na Æarasa da sauri na Éauki wayar don na shaida kiran Ummani daga ringtone Éin da na saka mata na Uwa Uwa Mama me share min kukana.
sai da na saita kaina da danne yanayin da na ke ciki na ce,"Salamu alaikum Ummani, ina yini".
Daga can Éangaren ta ce,"barkan ki dai Sa'ida, an yini lafiya, ya kike ke da mai gidan naki?."
na ce,"Lafiya lau Ummani, duk kuna lafiya?".
ta amsa,"lafiya lau, amma ya naji muryar taki kamar ba ki da lafiya."
na ce,"Ehh wallah Ummani na tashi da ciwon kai ne yau, yanzu na tashi a bacci ma shisa kika ji muryan nawa haka, dama ina cewa zuwa anjima zan kiraki".
na faÉi hakan ina dafe kaina yayin da sabbin hawaye masu zafin gaske ke zaryo min.
ta ce,"subhanallah to kin dai sha magani ko?".
na ce,"ehh na sha, shi ne ma naji daÉi ai".
ta ce,"to Allah ya sawwaÆe. daman maganar zuwa Æauye zan miki na bikin Æ´ar gidan Kawu Musbahu, gobe ne tafiyar da safe in Allah ya kaimu, ga shi na ji ki babu lafiya sai dai ki haÆura kya je musu daga baya ko".
tamkar anyi min bushara da kujerar makka haka naji maganar Ummani, wani farin ciki ya lulluÉe ni har hakan na bayyana akan fuskata, cikin saurin maganar da ban taÉa yi ba na ce,"lahh ai ciwon kaine fa kawai Ummani, kuma na faÉa miki naji daÉi ma".
sautin murmushin manyancenta ya bayyana har ya taÉa zuciyata, ta ce"ke dai kawai za kiyi Æarfin halin naki da kika saba, to Allah dai ya Æara lafiya. sai ki faÉawa mijin naki, idan ya barki kin fito da sassafe to mu tafi tare, in bai barki ba kuma kya taho ke Éaya tun da kuna da direba".
na ce,"ai kamar ma na sani muka yi maganar da shi Éazu, da yake shima yana shirin tafiya za su koma dubai, kin san dama nayi miki magana an gama ginin Éaya plaza Éin da ya buÉe. sai na ke ce masa to daga biki kuma sai in Éan yi kwanaki a gida ya ce babu matsala".
ta ce,"ah tou faÉuwa ma ta zo daidai da zama, shikenan to sai kin zo Éin. kya ce masa ina masa Allah kiyaye".
da haka muka yi sal