NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 34 of 97

da abincin mai gidan, ni ai ko babu komai ma kulle kitchen ɗin nasa yay min rana, tun da ga shi nayi natsatstsen bacci, kuma na huta haka babu ƙorafin ba ki kammala da wuri ba, babu ɗauko ɗauko, maida maida. wanka na shiga nayi, na tsaya gaban madubi ina mamakin irin ramar da nayi, ka rantse da Allah zaftarata ake yi, hannu na kai na taɓa kumburarren ciwon bakina, nayi wata dariyar takaici kawai ina girgiza kaina, hoton dukan da na sha jiya ya haska min tarr a ido, haka zagin da na sha yay amsakuwwa a kunnena, a jiya ina cewa na bar su da Allah ya saka min, amma a yanzu kam na yafe musu babu kuma ƙullacinsu a raina sam, na san zan daɗe kafin na manta abin da suka min amma zan yi dukkan iyawata don ganin na manta ɗin ko saboda kar na dinƙa ganinsu da abin har yasa ni jin ɓacin rai. humra na ɗauko zan shafa, sai dai ina ɗaukowar fuskata ta washe da dariyar da haƙorana suka bayyana, ba don komai ba sai don tunawa da Ummani, duk san da na kirata na ce Ummani Humra ta kusa ƙarewa zata ce Sa'ida amma shanta kike ko, ko kuma girki kike da ita ne in sa a koma haɗo miki duro guda. haƙiƙa ina son mahaifiyata, Allah dai ya bani ikon kyautata musu a rayuwa. rigar bubu na saka na sanya hular shatali, na ɗan yi tsaki saboda yanayin kitsona da ya tsufa. agogo na kalla ƙarfe sha biyu na rana da ƴan mintuna, na jijjiga kaina da mamaki, har na nufi ƙofa zan fita sai zuciyata ta dakatar da ni da ce min in fita in yi me?, ai kawai in koma in kwanta lokacin hutawa ne Allah ya kawo min, idan har ya dawo gidan ai dole zai zo ya tada ni ko dan ya ci zarafina, musamman da ya zamana laifin nawa tsagin jikinsa na taɓa. kan gado na koma na jingina bayana da filo, ba zan iya kwanciya ba don na gaji da ita, waya na ɗauka na kunna data na shiga wattpad na lalubo sunan Oum Mumtaz da Nana Haleema, nayi saving sababbin littafansu a library, na kashe data nan da nan kuwa na hau karatu, karatun littafin hausa sam bai dameni ba, amma ko da na leƙa wani group ranar nan naji ana ta koɗa littafan nasu na ce ni kam in sha Allahu sai anyi tafiyar da ni, baza'a barni a baya ba, Kwantan Ɓauna da Lokaci ne sai in ban same su ba amma ba abin da zai hana in karanta su kam. da littafin Lokaci ne na fara, kawai sai naji maganar Baba tana dawo min cikin kaina da yake cewa kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan aure, tabbas haka ne tunda ga Umaima ma wadda matsalarta da tawa kusan ɗaya ce, sai dai ita nata da lafiya tun da babu tsangwamar dangin miji haka kuma ta samu ciki har ta haife, saɓanin ni da dangin miji suka taso ni gaba, miji babu sauƙi, sharrin ƴaƴan ruƙo, ga kuma nakasun rashin haihuwa da duniya ke ganin shi a matsayin babbar tawaya a gare ni. murmushi kawai na ke me ciwo domin ni ɗaya na san me naji a cikin zuciyata, haƙiƙa jarabawar da na ke ciki tana da matuƙar wahala, amma babu komai na faɗawa Allah daren jiya, ya amsa sai jiran sakamako wanda na ke da yaƙinin me kyau ne. can ina cikin karatun Kwantan Ɓauna ina jinjinawa sha'anin hassada da makirci irin na gidan sarauta, naji cikina ya murɗa har nannaɗewa hanjina yake saboda mahaukaciyar yunwar da nake ji, tun ina daurewa naji ina ba zan iya ba, to amma ya zan yi? na san ko na sauka babu abin da zan samu na ci, amma zanje na duba kan dining wataƙila Allah ya taimake ni in samu ko guntun biredin shekaranjiya ne. abu kamar wasa lokaci ɗaya naji jikina ya kama karkarwa, na yi cilli da wayar gefe na fita a ɗakin a gigice, tabbas yunwa bata da hankali, ji na ke fa kamar zan mutu wallahi. kamar yanda na zata har yanzu kitchen ɗin a rufe yake babu alamar ma an buɗe shi, a daddafe na wuce dining ina zuwa Allah ya taimake ni na samu ragowar yogurt a jarka, ban wata wata ba na ɗauka na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tass. na san ba zai wuce mai gidan ne ya sha ya ajiye ba don ni dai ban san da shi a wurin ba, jiya ban bar komai akai ba da nayi gyara, to ban damu da duk hargagin da zai min ba, ba hauka na ke ba a yanda na ke jin raina na neman fita sanadin yunwa ba zanga abinci in ƙi ci ba, duk abin da zai min yay min na riga na saba yanzu. ɗaki na koma na ɗora karatuna daga in da na tsaya, a hankali naji cikina na motsa min da ciwo, can kuma na fara ji kamar ana ɗaure min hanjin cikina, nayi saurin miƙewa zaune ina riƙe cikina idanuna a runtse, tambayar kaina na fara anya youghurt ɗin da na sha me kyau ne?, ko dai ba Hubbi ne ya sha ya rage ba?, to wa ya shigo da shi?. da ƙyar na samu ciwon ya lafa na kwanta ba shiri, haka nayi ta sauke numfashi ina jin bacci yana ƙoƙarin ɗaukata, dama na ware a.c sanyin sai ratsa ƙashina yake. ban san bacci ya ɗauke ni ba sai ji nayi ana taɓa ƙafata, na buɗe ido a hankali, ido muka haɗa da Hubbi yana tsaye hannayensa zube cikin aljihun wando, ji nayi zuciyata ta motsa, nayi dakiyar ɓoye tsoronsa na ɓata rai ina yin miƙa, zuciyata kuwa
🏠