NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 97

a gidan auranta. ko babu komai ki gode Allah da ya baki miji me tsananin sonki da ƙaunarki gami da tausayinki. ni dai abin da na ke so da ke kar da ki dinƙa barin damuwa a ranki, hakan zai cutar da ke. kamata yayi duk san da kika kasance cikin halin tsanani, to ki ɗaura alwala ki fuskanci alƙibla ki gana da ubangijinki, a gaban mahallicinki ya kamata ki zubda tarin hawayenki, ki ƙaskantar da kanki a gabansa kina me roƙonsa cikin kirari da tsarkakewa, shi ya san halin da kike ciki kuma shi zai magance miki. kuma hakan zai sa ki samu rangwamen komai, tun haihuwarki mu ke miki addu'a kuma ba zamu daina ba har mu kai ga kushewa, kuma ina miki alƙawarin ƙara dagewa akan yi miki adu'a Ƴata. Allah bai hanaki don baya sonki ba, bai bawa wasu don yafi sonsu akanki ba, kema yana sonki kuma zai ba ki mafificin alkhairi cikin yardarsa da amincinsa. Allah yay miki albarka, Allah ya shiga dukkan lamuranki, ya yaye miki dukkan ƙunci, ya kawo miki salama da natsuwa. ayi haƙuri a ƙara haƙuri a kuma ci gaba da haƙuri kinji ƴar albarka, ina faɗa miki hakan ba kuma zan fasa faɗa miki ba ko da yaushe; haƙuri, uzuri, kawar da kai da kuma yafiya, ki kamasu tabbas kin kama makaman nasara da farin ciki, Sa'ida wanda ba ya haƙuri ba ya uzuri ba kuma ya yafiya to shi ne ke samun naƙasun farin ciki, amma me haƙuri da tawakkali da fawwalawa Allah komai wallahi ba ya tawaya, bayan tsanani sai daɗi da izinin Allah". yay shiru, ni kuma kukana ya ƙwace, cikin muryar da ta disashe da majina na ce,"na gode Abbaa nah, na gode sosai, ubangiji Allah ƙara muku lafiya, yaja min da ranku, yasa kuyi kyakykyawan ƙarshe". "amin ya Allah ƴar albarka. amma ki daina kukan, ki kuma yi min alƙawarin ba za ki ƙara ba". "in sha Allahu Abbaa". "zan tura miki kuɗi sai dai kiyi hakuri babu yawa". "na gode Abbaa Allah ƙara arziƙi da wadata" "amin ya Rahman, sai gobe kwayi waya da Ummanin, kar taji ki a wannan yanayin ta hana kanta sukuni, Allah ya sadamu da alkhairinsa, ki gaida ɗan nawa". ya ƙarasa faɗa yana kashe wayarsa, wani sabon kuka na ƙaunar mahaifina ya zo min sai dai nayi saurin toshe bakina tunawa da alƙawarin ce masa ba zan ci gaba da kukan ba. kai na kifa a gefen gado ina lallashin zuciyata da tuna kalaman mahaifina waɗanda su ka fara kwantar min da hankali, tabbas ina mai godiya ga Allah bisa ni'imar barmin su da yay a raye. wallahi ina son Abbaana, ban san ya zan kasance ba a duk san da aka ce ba ya raye, ni na sani ta kowacce fuska nayi dacen mahaifa, adu'ata Allah yasa suci moriyata kafin mutuwarsu, ya kuma sada su da aljanna maɗaukakiya. banɗaki na shiga nayi wanka, bayan shiryawata na shiga laluba jakar makarantata, cikon hukuncin ubangiji sai ga shi na samo wata matacciyar ɗari biyu, hamdala nayi ga Allah ina miƙewa na fita cikin ɗan guntun farin cikina na samun kuɗin, wurin me gadi na isa na ba shi na ce ya taimaka ya siyo min maganin ciwon jiki, idan akwai sauran canji ya siyo min awara ko gurasa. cikin mintunan da ba su haura ashirin da biyar ba sai ga shi ya dawo, nayi masa godiya sosai sannan na koma ɗakina, awarar ɗari da hamsin ce ba wata mai yawa ba guda uku, na ci na shiga banɗaki na sha ruwa na kuma sha maganin. har aka yi sallar isha'i ina ta jira ko zan ji motsin dawowar Hubbi amma shiru, ni hankalina ma gaba ɗaya na kan halin da aka ce yaran suna ciki, idan na ɗau waya zan kira shi sai zuciyata ta kwaɓeni akan hakan, daga ƙarshe kawai na aje wayar na kwanta bayan nayi sallar isha'i. wajen ƙarfe biyu na dare na farka firgigit, na sauko da sauri na faɗa banɗaki na yo alwala, sallah na tayar ina ta jero nafilfili kuma cikin kowacce sujjada da tahiya kuka na ke ga Ubangijina, ina mai yi masa kirari da tsarkakan sunayensa, ina roƙonsa da ya kawo min sauƙi a halin da na riski kaina, ya wanzar da alkhairansa a gare ni, ya canja min tsanani zuwa sauƙi, baƙin ciki zuwa farin ciki, damuwa zuwa walwala, tashin hankali zuwa kwanciyar hankali da zaman lafiya. ni dai cikin ikon Allah tun raka'ar farko na fara jin sukuni na ziyartar zuciyata, haka bayan na idar na ɗau ƙur'ani na fara karatu, karatun da ban daina ba sai da na ji an fara kiran sallar farko, wallahi zuwa wannan lokacin sai naji zuciya tayi wasaisai, naji tamkar ba'a taɓa dasa damuwa da ƙunci ba a tare da ni, haka kawai sai na ke jin wani farin ciki da ban san dalilinsa ba yana ziyartata, naji ina mantawa da faruwar komai yana barin jikina yabi iskar ɗakin. har sai da aka yi sallar asuba bayan na gama lazimi na ji bacci ya ziyarci idona, a sannan na miƙe da ƙwarin jikina da bana jin ciwo ko ɗis na hau gado na kwanta, bakina ɗauke da tasbihi bacci me daɗin gaske yay awon gaba da ni. ba ni na farka ba sai ƙarfe goma na safe, yau dai hankali kwance na sakko saɓanin da dana ke sakkowa a gigice idan na farka irin haka a makare, ba don komai ba sai don tunawa
🏠