NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 32 of 97

a, yanzun na ke cewa bara nayi sallar isha'i na kiraki, ina fatan lafiya kike da ke da mai gidan na ki ko?". wani sanyi ya ratsa ni na farin ciki da jin muryar mahaifina. nayi dakiyar danne kukana na ce,"muna lafiya lau Abbaa, fatan kuma lafiya ku ke?, ya kasuwa?". "lafiya lau fa Sa'ida, komai lafiya kinji, ba dai ki da wata matsala ko?". kamar ina gabansa na ɗaga kai alamar ehh,"babu matsalan komai Abbaa". "to ma sha Allah haka ake so ai, Allah yayi muku albarka gaba ɗayanku, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kauda duk wata fitina da saɓani a tsakaninku, Allah yay miki albarka kinji Sa'ida, Allah ya ba ki nasara da sa'a a rayuwa, mafi alkhairi yay ta bibiyarki. ki tura min lambar akawunt ɗinki zan saka miki ɗan abin da ya sawwaƙa". "tom Abbaa na gode, Allah ya ƙara arziƙi ya ƙara muku lafiya da tsawancin kwana". "amin ya hayyu ya qayyum, ya makarantar tahfeez ɗin na ki kuwa, ba dai kya wasa da zuwa ko?". "ina zuwa Abbaa". "kema da ke cikin masu saukar ta bana ne?". "a'a sai wata shekarar Abbaa". "to Allah ya bada ilimi mai albarka, ki gaida mijin naki. yanxu ina masallaci sai in na koma sai ta kira ki". har nayi haka zan kashe kiran sunana da yay ya dakatar da ni. na amsa masa sai naji yay shiru, tunanin ko kiran ya yanke ne hakan yasa na kalli screen ɗin kafin na kuma mayarwa kunne in sake cewa,"hello Abbaa". ajiyar zuciya naji ya sauke, shiru bai ce komai ba sai can yay nisa ya ce,"kina jina Sa'ida". na ce,"ehh Abbaa ina ji". ya ce,"walwala ta burin zuciyar ɗan Adam tsakanin abubuwa guda biyu take, farin ciki da baƙin ciki. idan abin farin ciki ya ratsa zuciya fuska zata nuna, za ta yi ƙyalli, zata sake sosai wajen bayyanar da farin cikinta, daga nan kuma murmushi da dariya su ziyarceta. idan kuma baƙin ciki ya ratsata sai tayi baƙi, ta turnuƙe, idanu suyi jajur su cika da ƙwalla, idan ya tsananta hawaye su jiƙa fuska, murya ta bada labarin yanayin da ake ciki...Ƴata kar ki manta da wanda kike waya, mahaifinki ne mai iya gane halin da kike ciki ko bai kalle ki ba, Sa'ida saki kukan da kike ta dannewa tun a sallamar farko, yi kukanki yacca kike so ba zan hanaki ba kuma ba zan tuhume ki dalili ba, domin shi kuka hanya ce ta rage raɗaɗin da ke cikin zuciya, sai dai ina so na tuna miki cewa kuka ba ya maganin matsala...yi kukan iyaka iyawarki ina sauraronki". zuciyata naji ta matse wani abu ya daki ƙirjina, Abbaa da kansa yau ke bani izinin yin kuka, mutumin da sauyawar yanayina kaɗai ke tada hankalinsa amma yau shi ke ce min nayi kuka iyakar yina, shin ya san matsalar da na ke ciki ne?. lokaci guda dauriyata ta ƙwace na fashe da matsanancin kuka me taɓa zuciyar duk me saurare, kamar yanda Abbaa ya faɗa sam bai yi ƙoƙarin hanani ba, bai kashe kiran ba haka bai ce komai ba, sai dai ina jiyo saukar numfashinsa, haka nayi kukana na gode Allah, murya a dusashe na ce,"Abbaa na gama, amma babu wata matsala, dama kukan soyayyarku ne kawai na ke yi". murmushin manyance naji yayi, bana ganinsa amma ina da tabbacin sai da ya gyaɗa kai kafin ya ce,"yaro yaro ne". kana ya ƙara cewa,"na sani soyayyar da kike mana zata iya sawa ki zubar da hawaye musamman idan kika tuna cewa akwai wani tabbataccen lokaci da dole mutuwa zata raba mu. sai dai ba hakan ne musababbin kukan na ki ba, muryarki kawai ta shaida min akwai matsala, haka ne?". na rumtse ido nace,"haka ne Abbaa". "to me yasa za ki ɓoye min?". "kayi haƙuri Abbaa". yay shiru na ƴan sakanni kafin yay gyaran murya. "saurare ni da kyau Sa'ida. mu iyayenki ne, babu wanda zai tsaya miki tsayin daka a duniyar nan sama da mu bayan mahallicinki. adu'armu a gareki kaɗai ta isa ta magance miki kowacce matsala da kike ciki, kuma ki sani adu'a na canja ƙaddara". yay amfani da kwantaccen lafazi wajen faɗin hakan. murya na rawa na amasa,"haka ne Abbaa, ba wai na ɓoye muku ba ne saboda tunanin ba zaku iya min komai ba, kawai shiga damuwarku akan hakan yasa Abbaa, amma kayi haƙuri Abbaa, adu'arka kawai na ke so". nayi maganar da muryar kuka ina me share hawayena. "Sa'ida ni mahaifinki ne, ba lallai sai kin ɓoye min kina cikin matsala da damuwa ba, muryarki zata bayyana min. ba zan tsaya shiga sha'anin aurenki ba, sai dai ina so na tuna miki duk lokacin da tsananin rayuwa ya dame ki, abu na farko da zai sa ki farin ciki shi ne ki tuna ke musulma ce kuma Masoyiyar Manzon ALLAH [S.A.W]. Duk tsananin da kike ciki ki tuna cewa akwai wanda ya fiki shiga tsanani, Ki tuna cewa kinfi mutane da yawa jin daɗin rayuwa. wannan rayuwar tamu ta duniya da kike gani gaba ɗayanta jarrabawa ce, Sa'ida aure kan saka mutum ya yi farin ciki a rayuwa sai dai duk tsananin farin ciki ba shi zai hana ma’aurata fuskantar matsaloli ba. ba abin mamaki ba ne idan a wasu lokuta anata fuskantar matsaloli a auratayya, domin rayuwar aure gaba ɗayanta haƙuri ce, haka kowacce mace da kalar jarabawarta
🏠